"Ba Za Su Iya ba," Gwamna Namadi Ya Hango Nasarar da Shugaba Tinubu Zai Samu a 2027
- Gwamna Umar Namadi ya dora yan adawa a sikeli, ya ce babu daya daga cikinsu da zai iya kalubalantar Shugaba Bola Tinubu a 2027
- Namadi ya bayyana cewa duba da dubban mutanen da suka fito zaben fitar da gwani, Tinubu da APC za su samu gagarumar nasara
- Gwamnan Jigawa ya sake jaddada alkawarin da ya yi na samar wa Tinubu sama da ƙuri’u miliyan ɗaya a zaɓen 2027, yana mai cewa hakan abu ne mai yiwuwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jigawa, Nigeria - Gwamnan Jihar Jigawa, Umar Namadi, ya bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu zai samu gagarumar nasara a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Gwamna Namadi ya bugi kirjin cewa babu wani ɗan adawa, har da tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan, da zai iya kawo barazana ga jam’iyyar APC a zabe mai zuwa.

Kara karanta wannan
2027: Kakakin majalisar Kwara ya raba gardama a zaben fitar da dan takarar gwamnan APC

Source: Facebook
Tribune Nigeria ta ce gwamnan ya bayyana hakan ne jim kaɗan bayan kaɗa ƙuri’arsa a zaɓen fitar da gwani na shugaban ƙasa da aka gudanar a mazaɓarsa da ke Ƙaramar Hukumar Kafin Hausa a Jigawa.
Dubban mutane sun fito zaben Tinubu
Namadi ya ce dandazon mutanen da suka fito domin shiga zaɓen alama ce da ke nuna cewa har yanzu al’ummar Najeriya, musamman na Jigawa, suna da cikakken kwarin gwiwa ga Shugaba Tinubu da gwamnatin APC.
A cewarsa, yadda aka gudanar da zaɓen cikin lumana da tsari ya ƙara tabbatar da jajircewar shugaban ƙasa wajen tabbatar da dimokuraɗiyya da adalci a cikin jam’iyyar APC.
Ya ce:
“Abin da ya fi muhimmanci shi ne dimokuraɗiyya ta cikin gida. Shugaban ƙasa ya bar tsarin dimokuraɗiyya ya gudana cikin ‘yanci, wanda hakan ke nuna cewa shi cikakken ɗan dimokuraɗiyya ne mai kishin ci gaban Najeriya.”
Gwamna Namadi ya yiwa Tinubu alkawari
Namadi ya sake jaddada alkawarin da ya yi na samar wa Tinubu sama da ƙuri’u miliyan ɗaya a zaɓen 2027, yana mai cewa hakan abu ne mai yiwuwa duba da yadda APC ke ƙara samun karɓuwa a jihar.
“Kamar yadda kuka gani, mutane sun fito da yawa domin Bola Ahmed Tinubu. Wannan ya nuna irin amincewar da suke da shi da kuma APC,” in ji shi.

Source: Facebook
Gwamnan ya kuma bayyana cewa sakamakon zaɓen fitar da gwanin shugaban ƙasa ya riga ya nuna abin da zai faru a babban zaɓen 2027, inda ya yi hasashen cewa APC za ta yi nasara a dukkan matakai.
“Sakamakon a bayyane yake. Da yardar Allah, zaɓen 2027 zai zama mai sauƙi ga APC saboda mutane sun yarda da jam’iyyar da gwamnati,” in ji shi.
Tsohon gwamnan Jigawa zai bar APC?
A wani rahoton, kun ji cewa tsohon Ministan Tsaron Najeriya, Mohammed Badaru Abubakar, ya yi magana game da jita-jitar barin APC mai mulkin Najeriya.
Badaru, tsohon gwamnan Jigawa ya musanta rahotannin da ke yawo cewa yana tattaunawa domin sauya sheka daga jam’iyyar APC zuwa ADC.
Ya ce babu wata gaskiya ko kadan a cikin rade-radin da ke cewa yana shirin komawa wata jam’iyya, yana mai kiran rahotannin da ƙirƙirarru.
Asali: Legit.ng
