Zaben Fitar da Gwani: Yadda Tinubu Ya Samu Kuri’u Kusan Miliyan a Borno, Kano

Zaben Fitar da Gwani: Yadda Tinubu Ya Samu Kuri’u Kusan Miliyan a Borno, Kano

  • Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi nasara a zaben fitar da gwani da aka gudanar a sassan Najeriya baki daya
  • Majiyoyi sun ce shugaban ya samu kuri’u kusan miliyan daya a zaben fitar da gwani na APC a Kano da Borno
  • A Kano, Gwamna Abba Kabir ya fadi yawan kuri'u da Tinubu ya samu da kuma abin da abokin takararsa Stanley Osifo ya samu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya yi nasara a zabukan fitar da gwani da aka a jihohin Borno da Kano.

Tinubu ya samu jimillar kuri’u 915,840 a zabukan da aka yi na shugaban kasa na jam’iyyar APC a Kano da Borno domin zaben 2027.

Tinubu ya samu nasara a zaben fitar da gwani
Shugaba Bola Tinubu na Najeriya. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Facebook

Kuri'un da Tinubu ya samu a Kano

A Kano, Tinubu ya samu kuri’u 500,852 inda ya doke abokin takararsa, Stanley Osifo, wanda ya samu kuri’u 2,675 a kananan hukumomi 44 na Kano, cewar Punch.

Kara karanta wannan

Tsohon IGP Adamu ya yi barazana bayan rasa tikitin APC na zaben gwamnan Nasarawa

An sanar da sakamakon zaben ne a gidan gwamnatin Kano yayin da jami’an jam’iyya da masu sa ido suka halarci taron tattara sakamakon.

Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau I. Jibrin, ya ce ya kada kuri’arsa a mazabarsa ta Kabo kafin ya halarci tattara sakamakon a gidan gwamnati.

Barau ya bayyana cewa gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, shi ne jami’in tattara sakamakon zaben APC na shugaban kasa a fadin Kano baki daya.

Ya ce an gudanar da zaben cikin lumana da gaskiya yayin da jami’an dawo da sakamako daga kananan hukumomi 44 suka gabatar da sakamakonsu a fili.

Barau ya ce nasarar Tinubu ta nuna irin karfin goyon bayan da shugaban kasar ke samu daga daukacin kananan hukumomin Kano gaba daya.

Zulum ya fadi yawan kuri'un Tinubu a Borno
Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno. Hoto: Prof. Babagana Umara Zulum.
Source: Original

Yawan kuri'un Tinubu a Borno

A Borno kuwa, Gwamna Babagana Zulum ya sanar da Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben fidda gwani bayan samun kuri’u 414,988 daga kananan hukumomi 27.

Zulum ya bayyana cewa an gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali a dukkan kananan hukumomin jihar ranar 23 ga watan Mayu, 2026 ba tare da matsala ba.

Kara karanta wannan

'Mutumina ne': Peter Obi ya yi magana da ake zargin yana gujewa Atiku

Ya ce an yi wa mutane 430,715 rajista domin zaben, yayin da kusan mutane 416,000 suka samu izinin kada kuri’arsu a zaben APC, cewar Daily Post.

A cewarsa, Tinubu ya samu dukkan ingantattun kuri’un da aka kada yayin da abokin takararsa Stanley Osifo bai samu ko kuri’a daya ba.

Zulum ya ayyana Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben fidda gwani na shugaban kasa a Borno tare da bayyana hakan a matsayin nasara mai girma.

Gwamna Namadi ya hango nasarar Tinubu a 2027

An ji cewa Gwamna Umar Namadi ya dora yan adawa a sikeli, ya ce babu daya daga cikinsu da zai iya kalubalantar Shugaba Bola Tinubu a 2027.

Namadi ya bayyana cewa duba da dubban mutanen da suka fito zaben fitar da gwani, Tinubu da APC za su samu gagarumar nasara.

Gwamnan Jigawa ya sake jaddada alkawarin da ya yi na samar wa Tinubu sama da ƙuri’u miliyan ɗaya a zaɓen 2027, yana mai cewa hakan abu ne mai yiwuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.