Dalilin da Ya Sa Tinubu Ya Cancanci 'Yan Najeriya Su Kara ba Shi Dama a Zaben 2027

Dalilin da Ya Sa Tinubu Ya Cancanci 'Yan Najeriya Su Kara ba Shi Dama a Zaben 2027

  • Ministan lafiya, Muhammad Ali Pate ya yi bayanin abin da ya sa yake ganin Shugaba Bola Tinubu ya cancanci tazarce a zaben 2027
  • Ali Pate ya ce Shugaba Tinubu ya samu nasarori da dama ciki har da sama wa matasa ayyukan yi a shekaru uku da ya kwashe a kan madafun iko
  • Ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da manema labarai a ƙarshen mako bayan zaɓen fitar da gwani na shugaban ƙasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Bauchi, Nigeria - Ministan kula da harkokin lafiya da walwalar jama’a na tarayya, Muhammad Ali Pate, ya yi ikirarin cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya cancanci wa'adi na biyu.

Ministan ya bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu ya cancanci yan Najeriya su sake zaɓensa karo na biyu duba da nasarorin da gwamnatinsa ta samu a cikin shekaru uku da suka gabata.

Kara karanta wannan

"Kamar nadin sarauta," Masani ya yi kaca kaca a nasarar da Tinubu ya samu a APC

Muhammad Ali Fate.
Ministan Lafiya, Muhammad Ali Pate ya wurin kaddamar da shirin lafiya na gwamnatin tarayya Hoto: Muhammad Ali Pate
Source: Twitter

Abin da zai sa a sake zaben Tinubu

Ali Pate ya ce daga cikin nasarorin gwamnatin Bola Tinubu har da samar da aikin yi ga matasa sama da 3,000 a Jihar Bauchi, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Ya kuma yaba wa gwamnatin Tinubu bisa samar da damar aikin yi ga matasan Najeriya, yana mai cewa matasa sama da 3,000 a Bauchi sun samu aiki ta hanyoyin shirye-shiryen gwamnatin tarayya cikin shekaru uku da suka gabata.

Haka kuma ya yaba da matakan da gwamnatin ta ɗauka a ɓangaren lafiya, musamman ƙaddamar da aikin tiyatar haihuwa ta 'cesarean' kyauta ga mata masu juna biyu, yana mai cewa wannan shiri abu ne da ba a taɓa gani ba.

Tinubu ya zuba ayyuka a Bauchi

A cewarsa, ayyukan more rayuwa da gwamnatin tarayya ta aiwatar ƙarƙashin shugabancin Tinubu sun bayyana a sassa daban-daban na ijihar Bauchi.

Ministan ya ce mazauna jihar Bauchi na iya ganewa cikin sauƙi ayyukan da gwamnatin APC ta kawo domin inganta rayuwarsu.

Kara karanta wannan

'Ba za mu bar 'yan adawa ba,' Tinubu ya magantu kan zaben 2027

Pate ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da manema labarai a ƙarshen mako bayan zaɓen fitar da gwani na shugaban ƙasa da APC ta gudanar ranar Asabar.

A matsayinsa na jami’in tattara sakamakon zaɓen fitar da gwanin shugaban ƙasa na APC a Bauchi, Pate ya ce Tinubu da ɗan kasuwa Sterlyn Osifo ne suka fafata wajen neman tikitin.

Shugaba Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a fadar gwamnatin Najeriya da ke Abuja Hoto: @OfficialABAT/X
Source: Facebook

Kuri'un da Shugaba Tinubu ya samu a Bauchi

Ministan ya bayyana cewa an gudanar da zaɓen cikin lumana a ƙananan hukumomi 20 na jihar tare da cikakken halartar mambobin jam’iyya daga matakin mazaɓu, ƙananan hukumomi da kuma jiha baki ɗaya.

A cewarsa, jami’an tattara sakamako daga dukkan ƙananan hukumomin jihar sun gabatar da sakamakonsu kafin a gudanar da tattara sakamakon ƙarshe a matakin jiha

Ya ce Tinubu ne ya lashe zaɓen da ƙuri’u 156,541, yayin da Sterlyn Osifo ya samu ƙuri’u 2,650, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Matsalar da Tinubu zai fuskanta a Kudu

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Ogun, Aremo Olusegun Osoba, ya yi zargin cewa ana kullawa shugaba Bola Tinubu makarkashiya a Kudancin Najeriya.

Kara karanta wannan

"Ni ma na rame": Tinubu ya amince manufofinsa sun jefa ƴan Najeriya a wahala

Osoba ya ce makircin na da nufin fito da ‘yan takarar shugaban kasa daban-daban daga Kudancin kasar domin rage tasirin Tinubu a zaben 2027.

Osoba ya bayyana haka ne a Abeokuta yayin sanar da sakamakon zaben fitar gwani na shugaban kasa da jam’iyyar APC ta yi a jihar Ogun.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262