Borno: Yadda aka Yi Dauki ba Dadi da Yan Boko Haram Suka Yi wa Sojoji Kwanton Bauna
- Wasu sojojin Najeriya huɗu sun jikkata bayan fashewar bam a lokacin da 'yan ta'adda suka yi masu kwanton ɓauna a hanyar Damboa zuwa Maiduguri
- Dakarun runduna ta 25 sun fafata da waɗanda ake zargin ƴan ta’adda ne bayan harin ba-zata da aka kai wa sojojin da ke aiki
- An yi arangama mai zafi kafin sojojin su samu nasarar dakile harin tare da fice wa daga yankin da aka so tsuke su a ciki yayin fafatawar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Borno – Sojoji huɗu sun samu raunuka bayan wani harin bam da kuma kwanton ɓauna da aka kai wa dakarun soji a babbar hanyar Damboa–Kumala–Maiduguri da ke jihar Borno.
Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne da 11.45 na safe a ranar 16 ga watan Mayun 2026, kimanin kilomita tara daga mahadar Kumala a ƙaramar hukumar Konduga.

Source: Facebook
Zagazola Makama ya wallafa a shafin X cewa majiyoyi sun shaida cewa dakarun runduna ta 25 da ke gudanar da sintirin tabbatar da tsaro sun ci karo da wani bam da aka dasa a bakin hanya wanda ake sarrafa shi daga nesa.
Sojoji sun gamu da sharrin yan ta'adda
Majiyoyin tsaro sun tabbatar da cewa bayan fashewar bam ɗin ne kuma 'yan ta'adda suka yi wa dakarun kwanton ɓauna wajen kai wa dakarun hari.

Source: Original
Duk da harin, rahotanni sun nuna cewa sojojin sun yi artabu da maharan tare da ƙoƙarin fatattakar su daga yankin bak daya.
Sai dai a yayin musayar wutar, sojoji huɗu sun samu raunuka daban-daban, amma ba a samu rahoton asarar rayukan dakarun ba.
Bayan aukuwar lamarin, an tura ƙarin dakarun soji daga hedikwatar da ke yankin domin tallafa wa aikin da kuma ƙara tabbatar da tsaro a hanyar.
Sojoji sun kwance bama-bamai
Haka kuma, an tura tawagar masu lalata bama-bamai ta EOD domin bincike da kawar da duk wata barazana da ka iya kasancewa a yankin.
Rahotanni sun ce jami’an EOD sun gano wani bam da ake zargi an dasa a kan hanyar, inda suka yi nasarar lalata shi cikin nasara ba tare da ya yi wata illa ba.
Majiyoyin tsaro sun ƙara da cewa an yi wa motoci farar hula guda 89 rakiya zuwa inda suka nufa domin tabbatar da kare rayukan matafiya.
Sai dai saboda dalilan tsaro, an kuma mayar da wasu motoci 165 zuwa Damboa domin kauce wa shiga yankin da ake gudanar da aikin tsaro.
Hukumomin soji sun tabbatar da cewa ana ci gaba da gudanar da aikin share hanya da sintiri domin tabbatar da cewa matafiya na amfani da babbar hanyar cikin tsaro.
Sojojin Amurka da Najeriya sun kashe yan ta'adda
A baya, mun wallafa labarin cewa dakarun sojojin Amurka da na Najeriya sun fafata da 'yan ta'addan kungiyar ISIS a wurarenTafkin Chadi bayan sun kai hare-hare zuwa yankin.

Kara karanta wannan
An shiga tashin hankali a Filato, ƴan bindiga sun kashe gomman mutane a sabon hari
Majiyoyi sun bayyana yadda aka kai hare-haren wadanda suka yi nasarar kashe babban dan ta'adda da ke jagorantar addabar bayin Allah a yankin, Abu-Bilal Al-Minuki da mayaka da dama.
An bayar da tabbacin cewa ba a samu asarar rayuka ko rauni ba daga bangaren sojojin Amurka da Najeriya wadanda suka gudanar da aikin, lamarin da ya jawo ayar tambaya kan ikirarin sojin kasar nan a baya.
Asali: Legit.ng

