
Maiduguri







Gwamna Zulum ya miƙa sandar mulki ga sabon Shehun Bama, Dr. Umar ElKanemi, tare da yabawa tsohon Shehu kan gudunmawarsa a ilimi, lafiya da zaman lafiya.

Rahotanni sun tabbatar da cewa wani kwamandan Boko Haram a Borno mai suna Mulwuta ya yi barazana ga mazauna Banki a karamar hukumar Bama a jihar.

Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ya yi nasarar zama sabon shugaban ƙungiyar gwamnonin yankin Tafkin Chadi, ya ce zai maiɗa hankali kan bunƙasa yankin.

'Yan ta'adda sun kai wa sojoji da fararen hula hari a Borno, inda aka rasa mutane da dama yayin aikin kwaso gawarwakin manoma da aka kashe a yankin Dumba.

Gwamna Zulum ya yi Allah-wadai da kisan manoma 40 a Dumba, ya ja kunnen jama'a su zauna cikin yankunan tsaro don kare rayuwarsu daga barazanar 'yan ta'adda.

'Yan ta'addar Boko Haram sun kai mummunan hari jihar Borno sun kashe manoma 40. Boko Haram sun mamaye kauye suna harbi kan mai uwa da wabi yayin harin.

Mayakan Boko Haram sun kai hari a ofishin 'yan sanda na Borno inda suka kashe jami'ai biyu. An ce wasu gurnetin hannu biyu da mayakan suka jefa ya yi kashe jami'an.

Sanata Ali Ndume ya ziyarci dakarun sojojin Najeriya da suka kashe 'yan boko Haram da dama. Ya raba tallafi ga mutanen mazabarsa da harin ya shafa.

Shugaban majalisar Borno, Abdulkarim Lawan, ya bukaci kafa rundunar soja a Guzamala da Kukawa don ’yantar da yankin daga Boko Haram tare da dawo da zaman lafiya.
Maiduguri
Samu kari