Tinubu na tsaka Mai Wuya, Kungiyar Tijjaniya Ta Yi Barazana kan Tsare Sheikh Sani Khalifa Zaria

Tinubu na tsaka Mai Wuya, Kungiyar Tijjaniya Ta Yi Barazana kan Tsare Sheikh Sani Khalifa Zaria

  • TIGMEIN da wasu ‘yan jihar Kaduna sun bukaci gwamnatin tarayya ta bi umarnin kotu kan sakin malamin addinin musulunci, Sheikh Sani Khalifa Zaria
  • An kama Sheikh Sani Khalifa ne bisa zargin yana da hannu ko masaniya kan juyin mulkin da ake zargin an yi yunkurin yi a shekarar 2025
  • Kungiyar ta 'yan darikar Tijjaniyya ta yi barazanar janye goyon baya ga Bola Ahmed Tinubu da APC idan aka ci gaba da tsare malamin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kaduna, Nigeria - Kungiyar 'yan darikar Tijjaniya ta TIGMEIN tare da wasu ‘yan jihar Kaduna masu rajin kare hakkin bil'adama sun tsoma baki kan tsare Sheikh Sani Khalifa Zaria.

Yan Tijjaniyyan sun bukaci gwamnatin tarayya ta bi hukuncin babbar kotun tarayya da ta bayar da umarnin sakin malamin addinin Musulunci, Sheikh Sani Khalifa Zaria.

Kara karanta wannan

Atiku ya bukaci a gaggauta sakin El Rufai, ya aika sako ga Tinubu da Uba Sani

Sheikh Khalifa Zaria.
Fitaccen malamin addinin musulunci, Sheikh Sani Khalifa Zaria Hoto: Garkuwan Makarantar Zazzau
Source: Twitter

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa kungiyar TIGMEIN ta bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a Kaduna.

TIGMEIN ta nemi a saki Shekh Sani Khalifa

Ta bayyana cewa ci gaba da tsare malamin duk da hukuncin kotu ya sabawa doka da kundin tsarin mulkin kasar nan.

Jami'an tsaro sun kama malamin ne bisa zargin hannu a shirin da aka yi na kifar da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu a 2025.

Da yake jawabi ga manema labarai, shugaban kungiyar TIGMEIN na Kaduna, Sayyadi Nasiru Sheikh Bello (Hayin Banki), ya ce wajibi ne gwamnatin tarayya ta mutunta bangaren shari’a ta hanyar sakin malamin ba tare da wani sharadi ba.

Umarnin da kotun tarayya ta bayar

A cewarsa, babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yanke hukuncin cewa tsare Sheikh Sani Khalifa Zaria ya saba wa hakkokinsa na dan Adam, tare da bayar da umarnin a sake shi nan take.

Kara karanta wannan

"Ba dai a matsayin rauni ba," Gwamna Radda ya kafa sharadin sulhu da 'yan bindiga

Kotun ta kuma umarci gwamnati ta biya shi diyyar Naira miliyan takwas saboda toshe asusun ajiyarsa da kuma tsawaita tsare shi ba bisa ka’ida ba.

Sai dai kungiyar ta ce maimakon gwamnati ta bi umarnin kotun, sai ta sake shigar da wasu sababbin tuhume-tuhume a kansa, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

“Maimaikon gwamnatin tarayya ta bi umarnin kotu, sai ta dauko wasu matakai da ke nuna rashin biyayya ga bangaren shari’a. Wannan abu ne mai hatsari ga dimokuradiyya,” in ji kungiyar.
Shugaba Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a fadar gwamnatin tarayya da ke Abuja Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

'Yan Tijjaniyya sun yi baranzana

Kungiyar ta bukaci a saki Sheikh Sani Khalifa Zaria ba tare da wani sharadi ba tare da dakatar da duk wani yunkuri na sake kama shi ko sake gurfanar da shi a kotu.

TIGMEIN ta yi gargadin cewa idan gwamnati ta ci gaba da tsare shi, hakan na iya haifar da sakamakon siyasa, ciki har da janye goyon baya ga Shugaba Tinubu da jam’iyyar APC.

Sani Ahmad, wani dan darikar Tijjaniyya ya tabbatar wa Legit Hausa cewa ko dai a sako malam, ko kuma ba za su sake zaben Shugaba Tinubu ba.

Kara karanta wannan

An ware Naira Biliyan 1.4 domin saya wa Gwamna Ahmed Aliyu sababbin motocin aiki

A cewarsa, babu dalilin da gwamnati za ta ci gaba da rike Sheikh Sani Khalifa bayan kotu ta ba da umarnin a sake shi bisa tanadin kundin tsarin mulki.

"Ai ko wannan kungiya ba ta fito ta yi wannan maganar ba, ba za mu sake zaben APC ba matukar aka ci gaba da tsare malam, wannan ita ce matsayarmu," in ji shi.

Sheikh Sani Khalifa ya yi bayani a kotu

A wani labarin, kun ji cewa babban malamin musulunci a Zaria, Sheikh Sani Khalifa ya gabatar da bayani kan zargin da ake yi masa na hannu a shirin juyin mulki.

Bayanin malamin na kunshe ne a wani faifan bidiyo da bangaren gwamnatin tarayya duka gabatar a zaman babbar kotun tarayya da ke Abuja.

Malamin ya shaida wa kotu cewa tun farko ya gargadi wadanda suka kitsa yi wa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu juyin mulki cewa ba za su yi nasara ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262