Hankula Sun Tashi da 'Yan Ta'adda Suka Tare Matafiya a Zamfara, an Tafka Barna

Hankula Sun Tashi da 'Yan Ta'adda Suka Tare Matafiya a Zamfara, an Tafka Barna

  • 'Yan ta'adda dauke da makamai sun yi wa matafiya kwanton bauna a jihar Zamfara, inda suka bude masu wuta
  • Tsagerun 'yan ta'addan sun kashe mutanen da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba tare da yin awon gaba da wasu da dama
  • Mazauna yankin da aka kak harin sun bayyana cewa daga cikin mutanen da aka kashe har da jami'an tsaro da ke yi wa motocin rakiya

​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Zamfara - Wasu da ake zargi ’yan ta’adda ne da ke gudanar da ayyukansu a yankin Dansadau na jihar Zamfara, sun yi wa matafiya kwanton ɓauna a kan hanyar Magami zuwa Dansadau.

'Yan ta'addan sun kashe mutanen da ba a tantance adadinsu ba tare da yin garkuwa da wasu da dama.

'Yan ta'adda sun sace matafiya a Zamfara
Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal Hoto: Dauda Lawal
Source: Facebook

'Yan ta'adda sun yi ta'asa a Zamfara

Kara karanta wannan

An shiga tashin hankali a Filato, ƴan bindiga sun kashe gomman mutane a sabon hari

Wani mazaunin Magami, wanda ya nemi a sakaya sunansa saboda dalilan tsaro, ya shaidawa tashar Channels tv cewa lamarin ya faru ne ranar Lahadi, 10 ga watan Mayun 2026.

Ya ce lamarin ya auku ne tsakanin ƙarfe 4:00 zuwa 5:00 na yamma, lokacin da maharan suka buɗe wa motocin da ke bin hanyar wuta.

A cewarsa, zuwa yanzu an gano gawarwaki 10 da 'yan ta'addan suka kashe yayin harin da suka kai a kan hanyar.

Yadda 'yan ta'adda suka kai harin

“Kamar yadda kuka sani, hanyar Magami zuwa Dansadau tana buƙatar rakiyar jami’an tsaro kafin matafiya su kai ga al’ummominsu cikin aminci."

"Matafiyan sun jira na kusan sa’o’i 7 ranar Asabar kafin jami’an tsaro su zo su raka su zuwa Dansadau. Suna cikin tafiya ne, sai wasu da ake zargi ’yan ta'adda ne suka kai hari kan jerin gwanon motocin, inda suka farmaki motar jami’an tsaron."
“Jerin gwanon ya kai ƙauyen Dogosatsin ne lokacin da ’yan ta'addan suka buɗe wa motar jami’an tsaron wuta, waɗanda ke raka matafiyan zuwa Dansadau, inda suka kashe jami’an tsaro, farar hula, da mambobin ƙungiyar sa-kai (CJTF), sannan suka bar wasu da dama da raunuka daban-daban."

Kara karanta wannan

Ana fargabar sabon harin sojoji ya kashe mutanen gari a jihar Neja

“Mun gano gawarwaki 10 kuma har yanzu muna ci gaba da neman wasu. Wadanda suka ji rauni an kwantar da su a babban asibitin Magami, amma daga baya aka tura su zuwa Gusau. Sai dai, har yanzu suna asibitin domin babu jami’an tsaron da za su raka su zuwa asibitin Gusau a yanzu."
“’Yan ta'addan sun kuma yi awon gaba da mutanen da ba a tantance adadinsu ba, waɗanda ke kan hanyarsu ta zuwa ƙauyuka daban-daban a yankin."
"An samu gagarumin ƙoƙari daga dakarun sojoji wajen korar ’yan ta'addan cikin daji da luguden wuta, wanda hakan ya rage yawan asarar da aka yi a lamarin.”

- Wani mazaunin kauyen Magami

'Yan ta'adda sun kai hari a Zamfara
Taswirar jihar Zamfara, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Abin da 'yan sanda suka ce kan harin

Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan jihar Zamfara, Yazid Abubakar, ya ce yana da masaniya game da harin.

Sai dai, ya bayyana cewa har yanzu ana ci gaba da tabbatar da adadin mutanen da suka mutu ko suka ji rauni ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.

Sojoji sun kashe 'yan ta'adda

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya sun yi wa 'yan ta'adda kwanton bauna a jihar Katsina da ke yankin Arewa maso Yamma.

​Dakarun sojojin sun samu nasarar kashe 'yan ta'addan guda uku tare da ƙwato makamai da wasu kayayyaki a hannunsu.

Sojojin sun kuma kwato wasu kayayyaki ciki har da kudade daga hannun tantiran 'yan ta'addan yayin artabun da aka gwabza.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng