Matasa Sun Yi Baje Kolin Fasaha wajen Yakar Labaran Karya gabanin Zaben Najeriya
- Ana ta horar da matasa wajen amfani da dabarun zamani don tabbatar da gaskiyar labarai kafin babban zaben Najeriya
- Matasa daga Kano, Legas, Enugu da wasu jihohi sun halarci taron don gina hanyoyin dakile jita-jita da karya a yanar gizo
- FactCheckAfrica ta fitar da sababbin dabaru, shirye-shirye da dokokin amfani da kafafen sada zumunta cikin lumana
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Gidauniyar FIAP ta shirya taro na musamman inda aka nuna fasaha wajen yaki da labaran bogi da na karya a Najeriya.
Fundación para la Internacionalización de las Administraciones Públicas wato FIAP ta shirya taron ta hannun FactCheckAfrica.

Source: Facebook
Taron baje-kolin fasahar yakar bayanan karya
Kamar yadda bayanin bayan taro da FactCheckAfrica ta fitar a yanar gizo ya nuna, an yi wannan zama ne a birnin tarayya Abuja.
Taron kwanaki biyu da aka gudanar sun fito da dabarun da wasu matasa suka fito da su da nufin a yaki labaran karya gabanin zabe.
Baje-kolin da aka yi mai taken #CheckBeforeYouPost a wani otel mai suna Reiz Continental Hotel ya tattaro matasa daga jihohi da dama.
Matasan sun yi amfani da zane, hotuna, bidiyoyi, wasan kwaikwayo da shafukan yanar gizo domin ganin karshen labaran bogi.
Daga cikin matasan da aka tattaro akwai ‘yan jarida, masu fada a ji a shafukan sada zumunta, sha’irai da da masana fasahar zamani.
Wannan yunkuri yana cikin kokarin da EU ta ke yi na tallafawa kungiyar ECOWAS a shirin EPSG domin inganta tsaro da zaman lafiya.
Kokarin da FactCheckAfrica ta ke yi a Najeriya
Gabanin taron Abuja, an yi makamancinsa a Legas, Kano da Enugu. Wannan karo sai aka zakulo mahalartan daga garuruwan nan.
Mahalartan sun samu horo wajen bankado bayanan karya da kuma yadda za su kawo zaman lafiya a dandalin sada zumunta na zamani.
A rana ta farko an duba darasun da aka dauka daga tarukan baya tare da kokarin ganin an samu dankon zumunci tsakanin mahalatan.
Washegari a rana ta biyu kuwa sai aka yi wa duniya baje-kolin fasahan da aka kirkiro.
Baya ga gajerun fina-finai, wakoki, hotuna da sauransu, an nuna shafukan yanar gizo da aka kirkiro masu fallasa labarai na bogi.
A wajen ne kuma FactCheckAfrica ta kaddamar da abubuwan da ta kirkiro domin tsabtace shafukan sadarwa daga karyayyaki da jita-jita.
Daga cikinsu akwai kundin gudanar da aikin jarida salin-alin, ka’idoji 10 na amfani da dandalin sada zumunta da dai makamantansu.
Shugaban FactCheckAfrica ya yi magana
Abideen Olasupo, wanda ya kafa FactCheckAfrica ya ce baje-kolin ya nuna rawar da matasa za su iya takawa wajen hana yada karya.
Olusupo ya ce wadanda aka gayyato za su cigaba da amfani da dandalinsu wajen binciko labaran da ba su da tushe gabanin zaben badi.
Jakadun kungiyoyin EU da ECOWAS da wakilan kasashen Denmark, Jamun da Sifen sun samu halatar babbantaron a ranar Juma’a.
Labaran karya: Yadda aka horar da matasa a Kano
An ji FIAP da FactCheckAfrica sun gudanar da horo a Kano da nufin samun dabarun yaki da labaran karya da kalaman kiyayya a yanar gizo
A kokarin ganin an yi zaben 2027 cikin lumana, FIAP da Fact Check Africa sun horar da matasa yadda za a yaki labaran bogi a Najeriya.
Horon yana ba matasa ilimin amfani da fasahohin zamani (kamar su AI) don tantance hoto, bidiyo, ko labarin da ke yawo kafin su yada shi.
Asali: Legit.ng

