Dakarun Sojoji Sun Yi Wa 'Yan Ta'adda Kwanton Bauna a Katsina, an Kashe Tsageru

Dakarun Sojoji Sun Yi Wa 'Yan Ta'adda Kwanton Bauna a Katsina, an Kashe Tsageru

  • Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasara kan 'yan ta'addan da ke addabar mutane a jihar Katsina da ke yankin Arewa maso Yamma
  • Sojojin sun samu nasarar hallaka 'yan ta'adda bayan sun yi masu kwanton bauna a karamar hukumar Dutsinma
  • Hakazalika, dakarun sojojin sun samu nasarar kwato makamai da kudade daga hannun tantiran 'yan ta'addan masu kai hare-hare

​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Katsina - Dakarun runduna ta 17 ta sojojin Najeriya sun yi wa wasu da ake zargi ’yan ta’adda ne kwanton ɓauna a ƙaramar hukumar Dutsin-Ma da ke jihar Katsina.

Dakarun sojojin sun kashe maharan guda uku tare da ƙwato makamai da wasu kayayyaki a hannunsu.

Sojoji sun kashe 'yan ta'adda a Katsina
Shugaban rundunar sojojin kasa na Najeriya, Laftanar Janar Waidi Shaibu Hoto: @HQNigerianArmy
Source: Twitter

Jaridar Daily Trust ta ce hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mukaddashin mataimakin daraktan yaɗa labarai na runduna ta 17, Kyaftin Abayomi Adisa ya fitar ranar Lahadi, 10 ga watan Mayun 2026.

Kara karanta wannan

Dakarun Sojoji sun dakile mummunan harin yan ta'adda, sun tura 50 lahira a Yobe

Sojoji sun ragargaji 'yan ta'adda

A cewar rundunar sojojin, dakarun da ke sansaninsu a FUDMA ne suka gudanar da aikin a matsayin ɓangare na ci gaba da kai hare-hare kan ’yan ta’adda da masu laifi a jihar.

Sanarwar ta ce dakarun sun mamaye wasu muhimman wurare a kan hanyar Turare–Kitibawa–Kuka Mai Damusa biyo bayan bayanan sirri da aka samu kan motsin wasu ’yan ta’adda da ke tserewa daga yankin Matazu.

Ya bayyana cewa da misalin ƙarfe 9:40 na dare a ranar Asabar, 9 ga Mayu, dakarun sun yi nasarar yi wa mutanen da ke ɗauke da makamai kwanton ɓauna yayin da suke ƙoƙarin tserewa daga ayyukan soja da ake gudanarwa.

Sojoji sun kashe 'yan ta'adda a Katsina

A cewar sanarwar, an kashe ’yan ta’adda uku yayin fafatawar, sannan dakarun sun ƙwato bindiga ƙirar AK-47 guda ɗaya, rumbun harsasai ɗauke da harsasai guda uku, babur guda ɗaya, adduna guda uku, layu daban-daban, da kuma tsabar kuɗi N3,500.

Kara karanta wannan

2027: Mata 6 da suka nuna sha'awar takarar gwamna a Najeriya

Sojoji sun samu nasara kan 'yan ta'adda a Katsina
Taswirar jihar Katsina, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Rundunar sojojin ta ce dakarun sun ci gaba da kai hare-hare kan masu laifi da nufin dawo da zaman lafiya da tsaro a faɗin jihar Katsina da jihohi maƙwabta, jaridar The Punch ta kawo rahoton.

Haka kuma, ta yi kira ga mazauna yankin da su ci gaba da ba wa hukumomin tsaro haɗin kai ta hanyar ba da sahihan bayanai akan lokaci waɗanda za su taimaka wa ayyukan da ake yi kan ’yan ta’adda da ’yan bindiga a jihar.

Sojoji sun dakile harin 'yan ta'adda

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojoji na rundunar Operation Hadin Kai (OPHK) sun dakile wani mummunan hari da mayaƙan ISWAP suka kai sansanin Brigade ta 27 da ke Buni Gari, jihar Yobe.

Yayin dakileharin, dakarun sojojin sun yi nasarar hallaka 'yan ta'addan kungiyar ISWAP 50. Sai dai sojoji biyu sun rasa rayukansu yayin musayar wutar da aka yi.

Mayaƙan na ISWAP sun kai harin ne daga wurare daban-daban a duhun dare, amma sojoji sun mayar musu da martani mai ƙarfi tare da nuna bajinta da ƙwarewa wajen kare sansanin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng