An Kuma: Matar Aure Ta Hallaka Mijinta Yana cikin Barci
- Ana zargin wata matar aure da sanadiyyar kawo karshen rayuwar mijinta wanda ko shekara daya ba su yi da aure ba
- Lamarin ya faru ne a daren Asabar, 8 ga watan Agustan 2026 lokacin da marigayin yake tsaka da barcinsa
- ’Yan sanda sun kama matar yayin da aka ajiye gawar marigayin a dakin ajiye gawa domin ci gaba da gudanar da bincike
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Abia – Wata mata mai suna Innocent Serah ta shiga hannun ’yan sanda bayan an zarge ta yin ajalin mijinta, Innocent Nwaoji.
Ana dai zargin matar ta soka wa mijinta, Innocent Nwaọjị, wuka har ya mutu a Umuokereke Ngwa, ƙaramar hukumar Obingwa ta jihar Abia.

Source: Original
Jaridar The Punch ta kawo rahoton cewa lamarin ya faru ne a daren Asabar, 8 ga watan Agustab 2026 inda ya jefa mazauna yankin cikin firgici da mamaki.
Ba a bayyana cikakken abin da ya jawo zargin soken ba, amma an tattaro cewa an soki Nwaọjị ne yayin da yake barci.
An kama matar aure kan kisan mijinta
Wani mazaunin yankin, David Amaraizu, ya tabbatar da faruwar lamarin yayin wata tattaunawa ta wayar tarho da manema labarai ranar Lahadi, 9 ga watan Agustan 2026.
Amaraizu ya ce lamarin ya girgiza mazauna yankin, inda ya bayyana cewa ma’auratan sun yi aure ne a watan Disamba na 2025.
Ya ce a lokacin da lamarin ya faru, aurensu bai kai wata takwas ba da daurawa.
“Ba mu san da wata rashin jituwa tsakanin ma’auratan kafin faruwar lamarin ba. An kama matar kuma a halin yanzu tana hannun ’yan sanda, yayin da aka kai gawar marigayin dakin ajiye gawa.”
Me 'yan sanda suka ce kan lamarin?
Lokacin da aka tuntubi jami’ar hulɗa da jama’a ta rundunar ’yan sandan jihar, Maureen Chinaka, ta ce:
“Zan dawo gare ku.”
Sai dai har zuwa lokacin kammala wannan rahoto, ba a samu ƙarin bayani a hukumance daga rundunar ’yan sandan ba.
An taba kama wata mata
A watan Fabrairun 2026 ma, rundunar ’yan sandan jihar Abia ta tabbatar da kama wata mata a Umuahia, babban birnin jihar, bisa zargin soka wa mijinta, wani jami’in hukumar shige da fice, wuka har ya mutu.
A cewar kwamishinan ’yan sandan jihar, Danladi Isa, an kama wadda ake zargin cikin gaggawa kuma ana yi mata tambayoyi a sashen binciken manyan laifuka na jihar kan zargin kisan kai, jaridar The Sun ta kawo labarin.

Source: Facebook
Asirin matar aure ya tonu
A wani labarin kuma, kun ji cewa wata mata mai suna Oluchi, wadda iyalanta suka bayyana cewa an yi garkuwa da ita a jihar Edo, ta shiga hannun jami'an tsaro.
Jami'an rundunar 'yan sanda sun gano Oluchi tana sheke ayarta ne tare da wani da ake zargin saurayinta ne a wani otal da ke jihar Delta.
Wata majiya ta bayyana cewa jami'an tsaro sun bi diddigin wata lambar waya da ake alakantawa da ɗaya daga cikin wadanda ake zargi har zuwa otal ɗin.
Asali: Legit.ng

