An Fadi Abin da Kashim Shettima ke Yi bayan Tafiya Hutun Mako 2

An Fadi Abin da Kashim Shettima ke Yi bayan Tafiya Hutun Mako 2

  • Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya kaddamar da hutunsa na mako biyu ta hanyar maida hankali kan karanta litattafai da nazari
  • Hotunan da aka wallafa sun nuna mataimakin shugaban ƙasar yana duba litattafai daban-daban a yayin da yake hutun da ya dauka bisa doka
  • Mataimaki na Musamman ga Shugaban Ƙasa kan Kafofin Yada Labarai da Sadarwa a Ofishin Mataimakin Shugaban Ƙasa, Stanley Nkwocha ne ya saki hotunan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja – Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya fara hutunsa na mako biyu ta hanyar dukufa wajen karanta litattafai da yin bincike, abin da fadar shugaban ƙasa ta bayyana a matsayin damar faɗada iliminsa domin bunkasa ayyukan da yake yi wa Najeriya.

Hotunan da aka fitar a ranar Litinin sun nuna mataimakin shugaban ƙasar yana duba litattafai tare da zurfafa tunani a lokacin da yake nesa da hidimomin ofis.

Kara karanta wannan

Rigima ta yi zafi, Atiku ya yi tone tone kan Obasanjo

Kashim Shettima a dakin karatu
Kashim Shettima na duba littatafai a wajen karatu. Hoto: Stanley Kingsley Nkwocha
Source: Facebook

Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaban Ƙasa kan Kafofin Yada Labarai da Sadarwa a Ofishin Mataimakin Shugaban Ƙasa, Stanley Nkwocha, ya wallafa a X cewa wannan lokaci hanya ce ta karatu, bincike, da neman sani.

Nkwocha ya ce:

"Kamar yadda mutane da dama suka yi hasashe, a yayin hutunsa na sati biyu, Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima, kamar yadda ya saba, yana amfani da lokacin wajen karatu da bincike."

Manufar hutun Shettima

Nkwocha ya bayyana cewa janye jiki daga hidimomin yau da kullum na samar da damar yin nazari kan sakamakon ayyuka cikin tsanaki tare da komawa bakin aiki da sabon karsashi da sabuwar fahimta.

Jaridar Punch ta wallafa cewa ya kara da cewa shagaltuwa da nauyin shugabanci ba ya dakatar da neman ilimi, sannan ya ce:

"Jagoranci yana dorewa ne ta hanyar kasancewa a shirye don ci gaba da koyo... Ga Mataimakin Shugaban Ƙasa, wannan lokaci dama ce ta karuwar ilimin da ake buƙata don ci gaba da yi wa Najeriya hidima."

Kara karanta wannan

Bayan haduwa da Tinubu, Sheikh Ibrahim Dahiru Bauchi ya gana da Wike

Shettima ya tafi hutun ne a ranar 7 ga Agusta, inda ake sa ran zai koma bakin aiki a ranar 20 ga Agusta. Wannan shi ne hutunsa na farko tun bayan rantsar da shi a ranar 29 ga Mayu, 2023.

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima
Kashim Shettima yana duba wasu littattafai. Hoto: Stanley Kingsley Nkwocha
Source: Facebook

An ce zurfafa ilimin zai taimaka masa wajen duba tsare-tsaren gwamnatin Tinubu na Renewed Hope Agenda da kuma fahimtar muhimman al'urorin manufofin cikin gida da na ƙasa da ƙasa.

Shettima ya yabi Tinubu

A wani labarin daban, kun ji cewa Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu ya cancanci yabo maimakon sukar da ake masa sakamakon sauye-sauyen tattalin arziƙi da gwamnatinsa ta kawo.

Shettima ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin da yake jawabi a taron bunkasa tattalin arziki da zuba jari na jihar Delta da aka gudanar a garin Asaba, babban birnin jihar.

Haka zalika, mataimakin shugaban ƙasar ya jinjina wa gwamnan jihar Anambra, Chukwuma Soludo, saboda goyon bayan da yake bai wa tsare-tsaren gyaran fuska na gwamnatin Tinubu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng