'Dalilin da Ya Kamata Ya Sanya Hukumar INEC Ta Gudanar da Zaben 2027 a Rana Guda'

'Dalilin da Ya Kamata Ya Sanya Hukumar INEC Ta Gudanar da Zaben 2027 a Rana Guda'

  • Mataimakin shugaban marasa rinjaye na Majalisar Wakilai, Abdussamad Dasuki, ya nemi INEC ta gudanar da zaɓen tarayya da na jihohi a rana ɗaya
  • Dasuki ya ce gudanar da zaɓen a rana guda zai rage asarar tattalin arziki da kuma kuɗaɗen da gwamnati ke kashewa
  • Dan majalisar ya kuma nemi a cire Sashe na 63(2) na Dokar Zaɓe saboda abin da ya kira barazana ga sahihancin zaɓen 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Abdussamad Dasuki, mataimakin shugaban marasa rinjaye na Majalisar Wakilai, ya buƙaci Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta sake duba tsarin gudanar da zaɓen 2027 a ranaku daban-daban, tare da gudanar da zaɓen tarayya da na jihohi a rana guda.

Dasuki ya kuma nuna damuwa kan Sashe na 63(2) na Dokar Zaɓe, yana gargadin cewa tanadin na iya yin illa ga sahihancin zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

Babban Sarki ya kama layi, ya ce ya kamata a hana kowa kamfe a jihar ban da Tinubu

An ba INEC shawara kan zaben 2027
Shugaban hukumar INEC, Farfesa Joash Amupitan da Abdussamad Dasuki Hoto: INEC Nigeria, House of Representatives, Federal Republic of Nigeria
Source: Facebook

Ya bayyana hakan ne a ƙarshen mako yayin da yake karɓar bakuncin matasan ADC, waɗanda suka kai masa ziyara domin taya shi murnar samun matsayin mataimakin shugaban marasa rinjaye, cewar rahoton Daily Trust.

Dasuki ya nemi a gudanar da zaɓe rana daya

Da yake jawabi ga matasan, ɗan majalisar ya ce gudanar da zaɓen 2027 a rana guda zai taimaka wajen rage babbar asarar tattalin arzikin ƙasa da ke faruwa sakamakon katse harkokin zamantakewa da tattalin arziki yayin gudanar da zaɓe a ranaku daban-daban.

Ya ce gudanar da zaɓen a rana ɗaya zai kuma rage wa gwamnati nauyin kuɗaɗe, saboda alawus-alawus da sauran kuɗaɗen ma’aikatan zaɓe na wucin gadi, jami’an tsaro da sauran kayan aikin gudanar da zaɓe za a kashe su ne na rana ɗaya maimakon ranakun zaɓe biyu.

Ya ce hakan ya zama wajibi musamman saboda ƙarancin kuɗaɗen da ake fama da shi na sauran buƙatun da suka shafi jin daɗin jama’a kai tsaye, jaridar TheCable ta kawo labarin.

Kara karanta wannan

Mabiyan Kwankwaso sun ɓullo da wasu dabaru da ka iya zama matsala ga Tinubu a zaben 2027

Menene amfanin yin hakan?

A cewarsa, haɗa zaɓen zai kuma rage yawan tafiye-tafiyen da ’yan Najeriya da sauran masu ruwa da tsaki za su yi saboda zaɓe, musamman duba da ƙalubalen tsaro da ƙasar ke fuskanta.

Ya bayyana cewa a tsarin da ake amfani da shi yanzu, mutanen da ke tafiya domin harkokin zaɓe na iya yin tafiya ɗaya a watan Janairu domin zaɓen tarayya, sannan su sake yin wata tafiya a watan Fabrairu domin zaɓen jihohi.

Ya ce idan aka gudanar da zaɓen a rana guda, irin waɗannan tafiye-tafiye za a yi su sau ɗaya ne kawai.

Dasuki ya buƙaci INEC ta haɗa zaɓen tarayya da na jihohi, tare da gudanar da su ko dai a watan Janairu ko Fabrairu na 2027.

A hada zabukan a takardu 5

Dasuki ya ce zaɓen da aka haɗa zai ƙunshi takardun zaɓe guda biyar da suka shafi zaɓen shugaban ƙasa, Sanatoci da ’yan Majalisar Wakilai a matakin tarayya, da kuma zaɓen gwamna da ’yan Majalisar Dokokin jihohi a matakin jiha.

Kara karanta wannan

Cikin gwamnoni 18 ya duri ruwa da EFCC ta fara bincike kan zargin karkatar da kudade

Mataimakin shugaban marasa rinjayen ya ce INEC na da damar tafiyar da takardun zaɓe guda biyar yadda ya kamata idan aka yi isasshen shiri tun kafin ranar zaɓe.

Dasuki ya soki dokar zaɓe

Da yake nuna damuwa kan wani tanadi na Dokar Zaɓe, Dasuki ya ce Sashe na 63(2) na iya yin illa ga sahihancin zaɓen 2027, saboda yana ba da damar ƙirga takardar zaɓe da ba ta ɗauke da alamar hukuma a wasu yanayi.

Saboda haka, ya nemi a cire Sashe na 63(2) daga Dokar Zaɓe. Ya ce tanadin na iya samar da wata kafa da za a iya amfani da ita wajen shigar da takardun zaɓe na bogi ko waɗanda ba su da izini cikin tsarin zaɓe.

Ya jawo hankali kan tanade-tanaden Sashe na 63(1) da na 63(2), musamman abin da ya bayyana a matsayin saɓani tsakanin sassan biyu.

An bukaci INEC ta hada zabe rana guda
Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), Farfesa Joash Amupitan Hoto: INEC Nigeria
Source: Facebook

INEC ta kara wa'adin mika sunayen 'yan takara

A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta kara wa'adin mika sunayen 'yan takarar gwamnoni da na majalisun dokoki a jihohi.

Hukumar zaben ta INEC ta bayyana cewa ta kara wa'adin ne bayan jam'iyyun siyasa sun nemi bukatar hakan daga wajenta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng