Ana Shirin 2027, an Gano Bindigogi 399 da aka Yi Shirin Kawowa Najeriya
- Hukumar Kwastam ta Najeriya ta gano bindigogi 399 da wasu muhimman sassan bindiga a cikin wani kaya da aka kama a Legas
- Hakan na zuwa ne yayin da ake cigaba da kara kaimi wajen yaki da fataucin makamai domin tabbatar da tsaro a fadin Najeriya
- Ta ce za ta miƙa makaman ga NCCSALW, yayin da take ci gaba da binciken gano waɗanda ke da hannu wajen safarar makaman
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Abuja – Hukumar Kwastam ta Najeriya (NCS) ta kammala harhada cikakken bincike kan wasu tarin makamai da aka kama a tashar Tin Can Island, inda aka gano bindigogin Jojef guda 399 da aka harhada.
Hukumar ta ce an kuma gano wasu muhimman sassan bindiga da dama a cikin kayan, lamarin da ya ƙara bayyana girman kayan makaman da aka yi ƙoƙarin shigar da su cikin ƙasar.

Source: Facebook
Legit ta gano haka ne a cikin wani sako da hukumar kwatsam ta wallafa a shafinta na Facebook a ranar Lahadi, 9 ga Agustan 2026.
Yadda aka gano makaman
Jaridar Punch ta ruwaito lamarin ya biyo bayan sanarwar da Babban Kwanturolan Kwastam, Adewale Adeniyi, ya yi a ranar Alhamis, 6 ga Agusta, 2026, cewa jami'an hukumar sun kama wata kwantena da aka ɓoye akwatunan sassan bindigogi a cikinsa.
A cewar hukumar, da farko an gano kayayyakin a matsayin sassan bindigogin Jojef da aka tarwatsa domin a shigar da su cikin ƙasar.
Bayan kammala haɗawa tare da tantance kayan, jami'an Kwastam sun gano bindigogi 399 da aka harhada gaba ɗaya.
Gargadin da kwatsam ta yi
Adewale Adeniyi ya yi gargaɗin cewa ƙungiyoyin masu aikata laifi na iya ƙoƙarin amfani da iyakokin ƙasa, tashoshin jiragen ruwa da filayen jiragen sama wajen shigar da haramtattun kayayyaki yayin da ƙasar ke tunkarar babban zaɓe.
Ya ce hukumar za ta ƙara tsaurara sa ido da bincike domin hana shigar da irin waɗannan makamai cikin Najeriya.
Za a miƙa makaman ga NCCSALW
Adeniyi ya sake jaddada cewa hukumar za ta ci gaba da amfani da bayanan sirri wajen dakile safarar makamai, tare da ƙarfafa sa ido a kan iyakoki da haɗin gwiwa da sauran hukumomin tsaro.
Ya ce hukumar za ta haɗa hannu da NCCSALW da ke ƙarƙashin Ofishin Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Tsaro (ONSA), domin ganowa tare da tarwatsa hanyoyin safarar makamai.

Source: Facebook
Bayan kammala tantance makaman, Kwastam ta ce tana shirin miƙa su ga NCCSALW domin a tabbatar da cewa an cire makaman gaba ɗaya daga hannun jama'a, yayin da bincike zai ci gaba domin gano waɗanda ke da hannu a safarar su.
An kashe danbindiga a Imo
A wani labarin, mun ruwaito cewa jami'an Special Tactics Squad (STS) na Sashen Leken Asiri na Rundunar 'Yan Sandan Najeriya sun kashe wani mutum da ake zargi da jagorantar ƙungiyar masu aikata laifi da ke da alaƙa da kisan sarkin Ochia a jihar Imo.
Rundunar 'yan sandan ta ce wanda aka kashe, Ojiogu Elumah Martin, wanda aka fi sani da “Acid”, yana cikin waɗanda ake zargi da hannu wajen kisan HRH Eze Paulinus Ekwueme.
Jami'an STS-FID sun gudanar da wasu samame tsakanin 2 zuwa 6 ga Agusta, 2026, bayan samun bayanan sirri kan ƙungiyar da ake zargi da hannu wajen kisan sarkin da wasu mutane biyar a yankin Ohaji/Egbema.
Asali: Legit.ng


