Yan Bindiga Sun Magantu, Sun Tsuga Miliyoyi na Fansar Alkalin Babbar Kotun Kebbi
- 'Yan bindiga sun nemi Naira miliyan 200 daga iyalan alkali a Kebbi bayan sun sace shi daga gidansa a karamar hukumar Bunza
- Rundunar 'yan sandan Kebbi ta tura jami'ai domin bibiyar hanyoyin tserewar masu garkuwa tare da ƙarfafa tsaro don ceto alkalin
- Kwamishinan 'yan sanda ya gargadi jama'a su guji tafiya da tsakar dare, yana cewa hakan na ƙara haɗarin fadawa hannun 'yan bindiga da masu laifi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kebbi - Wasu da ake zargin 'yan bindiga ne sun yi magana bayan sace alkalin babbar kotun jihar Kebbi da ke Arewacin Najeriya.
Yan bindigar sun nemi Naira miliyan 200 daga iyalan alkalin Babbar Kotun Jihar Kebbi, Mai Shari'a Faruku Hassan Bunza, domin su sake shi.

Source: Original
Kwamishinan 'yan sandan Jihar Kebbi, Umar Muhammad Hadejia, ya tabbatar da hakan ga manema labarai ranar Litinin a Birnin Kebbi, cewar Leadership.
Kokarin da jami'an tsaro ke yi
Hadejia ya ce bayanan sirri sun nuna cewa masu garkuwar sun nemi kudin fansar ne bayan sun sace alkalin daga gidansa da ke kan titin Zogirma.
Lamarin ya faru ne da sanyin safiyar ranar Lahadi a karamar hukumar Bunza, inda jami'an tsaro suka kai dauki cikin gaggawa bayan samun rahoto.
Kwamishinan ya ce rundunar ta tura hadaddiyar tawagar jami'an tsaro domin binciken dukkan hanyoyin da ake zargin masu garkuwar sun bi wajen tserewa.
Ya kara da cewa an kafa shingayen bincike a wurare masu muhimmanci domin hana masu garkuwar tserewa tare da ceto alkalin ba tare da rauni ba.
Hadejia ya bayyana kwarin gwiwarsa cewa matakan tsaron da aka dauka za su taimaka wajen cafke masu garkuwar tare da kubutar da alkalin cikin aminci.
Ya kuma tabbatar da kashe Abdulaziz Dogo da kama Ibrahim Abdulwahab dangane da sace tsohon mataimakin kakakin majalisar dokokin Kebbi a shekarar 2025.

Source: Facebook
Shawarar kwamishinan yan sanda a Kebbi
Kwamishinan ya shawarci jama'a, musamman jami'an gwamnati, da su guji yin tafiye-tafiye da tsakar dare saboda barazanar hare-haren 'yan bindiga, cewar Punch.
Ya ce iyalan Mai Shari'a Bunza sun shaida wa masu bincike cewa alkalin ya saba yin tafiya da dare duk da matsalolin tsaro da ake fama da su.
Hadejia ya kuma bayyana cewa masu garkuwar sun tuntubi wani magatakardan Babbar Kotu da ke Abuja kan batun biyan Naira miliyan 200 kudin fansa.
Rundunar 'yan sanda ta tabbatar da cewa bincike da farautar masu garkuwar na ci gaba domin ceto alkalin cikin koshin lafiya tare da gurfanar da wadanda suka aikata laifin.
Yan bindiga 200 sun kai hari a Sokoto
An ji cewa 'yan bindiga da ake zargin sun sanya kayan sojoji sun kai hari Unguwan Lalle da ke karamar hukumar Sabon Birni a Sokoto.
Maharan da yawansu ya kai kusan 200 sun kwashe kusan sa'o'i shida suna wawushe kaya a gidaje da shaguna tare da sace dabbobi.
'Yan bindigar sun kai harin ne jim kadan bayan sojoji sun bar kauyen bayan sun mayar da martani kan wani hari da aka kai da rana.
Asali: Legit.ng

