Tsananin zafin rana ya sanya kankara zama tamkar zinare a jihar Bauchi

Tsananin zafin rana ya sanya kankara zama tamkar zinare a jihar Bauchi

- Saboda matsanancin zafin da ake a jihar Bauchi ya sanya kankara tafi komai daraja a cikin kayan abubuwan da ake amfani da su wurin buda baki a wannan watan mai alfarma

- Wani mutumi da ya ke sana'ar sayar da kankarar ya ce a kullum yana samun ribar naira 30,000

Masu sayar da kankara a jihar Bauchi kasuwa ta bude sosai, yayin da ake matsanancin zafi ga kuma azumi a bakin al'umma, inda suke amfani da wannan damar suke cin karensu babu babbaka.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya bayyana cewa matsanancin zafin ya sanya kankara tana wahala, kuma ta zama tamkar zinare, domin kuwa yadda ake nemanta ba a neman kayan marmari da sauran abubuwa.

Wani dan jarida da ya ziyarci wani mai sayar da kankara a unguwar Fadamar Mada da kuma unguwar Yelwa a cikin jihar Bauchi, ya bayyana cewa sana'ar ta na da riba matuka, musamman yanzu da ake fama da tsananin zafi a jihar.

Tsananin zafin rana ya sanya kankara zama tamkar zinare a jihar Bauchi
Tsananin zafin rana ya sanya kankara zama tamkar zinare a jihar Bauchi
Asali: Facebook

Kankarar da ake sayarwa naira hamsin yanzu ta koma naira dari, kuma mutane basu damu ba saboda bukatar ta da ake yi.

"Akwai ranar da kankara ta yi karanci, inda mutane suka dinga shiga lungu-lungu domin nemanta, duk wurin da ake sayarwa a lokacin idan kaje wurin sai kaga ana yin dambe tsakanin mutane."

KU KARANTA: Sau uku kawai na yiwa yarinyar makwabcina fyade - Wani mutumi

Usman Suleiam, wani mai sayar da kankara a unguwar Fadamar Mada, ya ce an dauki shekaru kankara ba ta yi darajar da ta yi ba yanzu. Ya ce yana samun ribar naira dubu talatin a kowacce rana.

Haka shima wani mai sayar da kankarar, Hussaini Abubakar, ya ce masu sayen kankarar ba wai daga iya cikin Bauchi kawai suke zuwa ba, wasu har daga garuruwa irinsu Darazo, Ningi, Dass da Alkaleri suke zuwa.

"Duk da irin yawan kankarar da muke kawowa, amma ba kowa ne yake samu ba, da yawa suna komawa gida ba tare da ita ba," in ji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa nan: Domin karuwa cikin wannan wata mai alfarma na Ramadana

Asali: Legit.ng

Online view pixel