Bakin Haure 49,000 daga Afrika Sun Shiga Spain Ta Tekun Morocco
- Mahukuntan Sifaniya sun ce kimanin bakin haure 49,000 ne suka shiga yankin Ceuta daga Morocco cikin sa'o'i 24 da suka gabata
- Gwamnatin Sifaniya ta tura sojoji domin ƙarfafa tsaro bayan dubban mutane sun tsallaka ta ruwa da kuma ta kan iyaka zuwa yankin
- Akalla mutum 15 sun mutu a ruwa yayin da suke ƙoƙarin isa Ceuta, lamarin da ya jefa cibiyoyin karɓar 'yan gudun hijira cikin matsin lamba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Madrid, Spain – Gwamnatin Spain ta sanar da tura sojoji zuwa yankin Ceuta da ke Arewacin Afirka bayan dubban 'yan gudun hijira sun ratsa daga kasar Morocco zuwa yankin cikin sa'o'i 24.
Mahukuntan ƙasar sun ce kimanin mutane 49,000 ne suka shiga Ceuta ta ruwa da kuma ta kan iyaka, lamarin da ya haifar da babbar matsalar tsaro da ta karɓar bakin haure.

Source: Getty Images
Biyo bayan lamarin, BBC ta rahoto cewa akalla mutum 15 sun rasu yayin da suke ƙoƙarin iyo domin isa yankin Ceuta daga gabar tekun Morocco.
Dalilin da ya sa tura sojoji Ceuta
Ma'aikatar harkokin cikin gida ta Sifaniya ta bayyana cewa an tura sojoji domin su taimaka wa jami'an tsaron farin kaya wajen tabbatar da tsaro da kuma dakile rikicin da ya biyo bayan yawaitar shigowar bakin haure.
A cewar gwamnatin, ƙungiyoyin safarar mutane na amfani da wani sabon hukuncin Kotun Koli ta Sifaniya domin ƙarfafa wa bakin haure gwiwar tsallakawa zuwa Ceuta ba tare da takardu ba.
Kotun ta yanke hukuncin cewa ba za a iya mayar da bakin hauren da aka kama a teku kai tsaye zuwa Morocco ba idan suna ƙoƙarin shiga Ceuta ko Melilla.
Sanchez zai kai ziyara Ceuta
Firaministan Sifaniya, Pedro Sanchez, na shirin kai ziyara yankin Ceuta domin duba halin da ake ciki tare da ɗaukar matakan dawo da zaman lafiya a wajen.
Rahotanni sun nuna cewa cibiyoyin karɓar 'yan gudun hijira sun cika maƙil, yayin da hukumomin yankin suka zargi gwamnatin tarayya da yin jinkirin mayar da martani.

Source: Getty Images
Haka kuma gwamnatin Italiya ta ce tana nazarin ɗaukar matakai na musamman, ciki har da yiwuwar rufe iyakar yarjejeniyar Schengen tsakaninta da Sifaniya idan matsalar ta ci gaba.
Ga bidiyon yadda mutane ke shiga Spain da Elon Musk ya wallafa a X:
Yarjejeniyar Hamas da Amurka
A wani labarin, mun ruwaito cewa shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da cewa kwamitinsa ya cimma wata yarjejeniya ta tarihi kan kwance damarar kungiyar Hamas da sauran kungiyoyin Falasdinawa masu dauke da makamai.
Trump ya bayyana matakin a matsayin wani babban ci gaba wajen aiwatar da shirinsa mai mataki 20 domin samar da zaman lafiya a Zirin Gaza.
Rahotanni sun ce jami'an Hamas sun amince da shirin bayan tattaunawar da masu shiga tsakani daga Masar, Qatar da Turkiyya suka gudanar a birnin Alkahira, yayin da Isra'ila ba ta fitar da wata sanarwa kan lamarin ba.
Asali: Legit.ng

