Jira Ya Kare, Gwamnan Adamawa Zai Nuna Ɗan Takarar da Yake So Ya Gaje Shi a 2027
- Gwamna Ahmadu Fintiri na jihar Adamawa ya sanar da cewa nan ba da jimawa ba zai bayyana sunan mutumin da yake so ya gaje shi a zaɓen 2027
- Gwamnan ya ce har yanzu ana kan tuntuɓar masu ruwa da tsaki kuma zai yi amfani da dukkan tsarin doka domin ganin wanda ya zaɓa ya yi nasara
- Ya jaddada cewa adalci da aminci ga al'umma ne za su jagoranci matakin da zai ɗauka, yayin da ya fara ganawa da d'an takara, Dr. Salihu Mustapha
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Adamawa - Gwamnan Adamawa, Ahmadu Fintiri ya bayyana cewa nan ba da jimawa ba zai nuna mutumin da yake so ya gaje shi a zaɓen gwamnan jihar na shekara mai zuwa
Gwamna Fintiri ya bayyana hakan ne a ranar Litinin a garin Yola yayin da yake karɓar ɗaya daga cikin masu neman takarar gwamna a ofishinsa.

Source: Twitter
Fintiri zai nuna magajinsa makon gobe
Gwamnan ya nanata cewa yana da damar zaɓar wanda yake so, kuma nan da mako mai zuwa zai nuna wa duniya wanda ya tsayar a matsayin ɗan takararsa, in ji rahoton The Cable.
Fintiri ya bayyana cewa:
“Zan yi amfani da haƙƙina na naɗa da kuma zaɓar ɗan takarara. Ina duba dukkan abubuwan da suka dace, kuma nan da mako mai zuwa zan nuna ɗan takararar”.
Gwamnan ya ce har yanzu yana ci gaba da tuntubar masu ruwa da tsaki, yayin da ya kara da cewa za a kaddamar da tsarin da zai jagoranci tabbatar da nasarar dan takarar da za a fitar a zaben na 2027.
Salo da manufar zabar 'dan takara
Gwamna Ahmadu Fintiri ya jaddada cewa ya san abin da al'ummar jihar suke buƙata kuma ya san wanda suke so ya gaje shi.
Ya bayyana cewa ba ya tsoron tsangwama ko matsin lamba wajen tabbatar da cewa mutumin da ya fi dacewa ya gaje shi, har ma ya ce a shirye yake ya sadaukar da rayuwarsa domin nasarar jihar.
Duk da cewa yana da wanda yake so, Gwamna Fintiri ya bayyana cewa ƙofarsa a buɗe take ga sauran masu neman takara.
Gwamnan ya kuma ya ƙarfafa gwiwar duk wanda yake jin yana da gogewa da kuma ƙarfin gwiwar shiga fagen takara da ya fito yayin da ya jaddada cewa adalci da aminci ne za su zama babban ma'auni a cikin tsarin.

Source: Twitter
Ganawar Fintiri da Dr. Salihu Mustapha
Bayan ganawa da Dr. Salihu Mustapha a ofishinsa, Gwamna Fintiri ya wallafa a shafinsa na X (da aka sani da Twitter a baya) cewa ya karɓi baƙuncinsa kuma ya sanya wa kudurinsa albarkarsa.
Dr. Mustapha ne ɗan takara na farko daga jam'iyyar APC da ya ziyarci ofishin gwamnan domin bayyana sha'awarsa ta tsayawa takara.
Gwamna Fintiri ya nanata cewa za su yi aiki tuƙuru domin tabbatar da adalci da kuma nuna aminci ga al'ummar jihar Adamawa.
Karanta sanarwar Fintiri a kasa:
Fintiri zai yi takarar Sanatan Adamawa
A wani labari, mun ruwaito cewa, Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, zai kammala wa'adin mulkinsa na biyu a shekarar 2027.
Tuni dai gwamnan ya amsa kiran al'umma na fito wa takarar kujerar sanatan Adamawa ta Arewa a karkashin inuwar jam'iyyar APC mai mulki.
Da wannan, Gwamna Fintiri zai fafata da shahararren dan kasuwa wanda ya koma siyasa, Abdulrahaman Kwacam domin samun tikitin APC.
Asali: Legit.ng


