Saboda Tsananin Zafi, Wani Mutum Ya Fado Daga Bene Ya Mutu Yana Tsakar Bacci

Saboda Tsananin Zafi, Wani Mutum Ya Fado Daga Bene Ya Mutu Yana Tsakar Bacci

  • Wani Dauda mai shekaru 30 da doriya ya fado daga bene mai hawa biyu inda take yanke ya rasu a Ilorin cikin Jihar Kwara yayin da yake tsaka da bacci
  • An samu bayanai akan yadda lamarin ya auku da misalin karfe 12 na ranar Juma’a a anguwar Ile Oniyo cikin Ita Merin inda ya rasu kafin a isa asibiti
  • Mazauna Ilorin suna kwana a waje saboda tsananin zafin da garin yake da shi, kuma mamacin ya kwanta ne yana shan iska inda bacci mai dadi ya kwashe shi har ajalinsa yazo

Jihar Kwara - Wani dilan kayan motoci, Dauda ya rasu bayan ya fado daga bene hawa na biyu a Ilorin cikin Jihar Kwara, The Punch ta ruwaito.

The Punch ta tattaro bayanai akan cewa shekarun mamacin 30 da doriya, kuma ya fado daga benen ne yayin da yake tsaka da barci inda ya mutu kafin a isa asibiti da shi.

Saboda Tsananin Zafi, Wani Mutum Ya Fado Daga Bene Ya Mutu Yana Tsakar Bacci
Saboda Tsananin Zafi: Wani Ya Fado Daga Bene Ya Mutu Yana Tsakar Bacci. Hoto: The Punch
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Lamarin ya auku ne da misalin karfe 12 na ranar Juma’a a Ile Oniyo a Ita Merin da ke garin Ilorin.

Yanzu mazauna Ilorin ba sa iya bacci a cikin dakunan su

Mazauna Ilorin da dama sun koma kwana a wajen dakunan su saboda tsabar zafin da ke damun su.

An samu bayanai akan yadda mamacin dilan kayan motoci ne a kasuwar Jengbe da ke Ilorin.

Abokin sana’ar mamacin mai suna Alfa Abdul yace Dauda bai dade da gama koyon aiki ba inda yake koyon sana’a tare da wani abokin aikin su da ke kasuwar kafin lamarin ya faru.

Wani shugaba na yankin kasuwar ya ce Dauda mutum ne mai hankali

A cewarsa:

“Gidan bene ne mai hawa uku amma akwai wani wuri da mutane suke shan iska saboda yanzu haka ba sa iya bacci a dakunan su saboda zafin da ake ciki.
“Ya dawo gida sai ya zarce wurin da yake bacci kamar yadda ya saba. Ta yuwu kara jujjuyawa ya yi daga nan ya fado.
“An yi kokarin garzayawa da shi asibiti inda aka tabbatar da cewa ya mutu. Kuma an dade da birne shi kamar yadda addinin musulunci ya tanadar.”

Wani shugaba na yankin kasuwar, Baba Musa ya tabbatar da aukuwar mummunan lamarin. Inda ya ce:

“Dauda bai dade da samun ‘yancin kansa ba daga shugaban sa. Mutum ne mai hankali da biyayya. Mun yi babban rashi amma Allah ya fi kowa sani.”

Obasanjo: Sai an binciko kuma an hukunta wadanda suka banka wa gona ta wuta

A wani rahoton, Tsohon shugaban kasa Obasanjo ya yi alawadai akan kona gonarsa da wasu batagari suka yi a garin Howe da ke Karamar Hukumar Gwer ta Kudu a Jihar Binuwai a kwanakin karshen makon nan, The Punch ta ruwaito.

Tsohon shugaban kasar mai shekaru 84 ya kwatanta lamarin a matsayin mummunan abu kuma ya ce sai jami’an tsaro sun gano wadanda suka tafka ta’asar.

The Punch ta ruwaito yadda batagari suka babbake gonar Orchard wacce mallakin babban mutumin ne na Hilltop da ke Abeokuta a ranar Asabar.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel