Tsananin Zafi Ya yi Sanadiyyar Rayuka 900 a Hajji, Musulmi na Cigiyar 'Yan Uwansu

Tsananin Zafi Ya yi Sanadiyyar Rayuka 900 a Hajji, Musulmi na Cigiyar 'Yan Uwansu

  • Musulmi sama da 900 ne ake zaton sun koma ga mahallicinsu bayan tsananin zafi da jawo rashin lafiya yayin aikin hajjin bana da aka kammala ranar Asabar
  • Rahotanni sun tabbatar da cewa yanzu haka alhazai da dama na cigiyar 'yan uwansu da aka nema aka rasa, suna wallafa bayanansu ta shafukan sada zumunta
  • Kasashe da dama ciki har da Najeriya, Misra, Indonesiya, Jordan, Indiya da sauran kasashe sun rasa alhazansu yayin da zafi ke kara tsananta a Saudiyya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Saudi Arabia- Sama da musulmi 900 ne su ka kwanta dama a aikin hajjin bana, yayin da mutane da yawa ke neman ‘yan uwansu da aka nema aka rasa a kasa mai tsarki.

Kara karanta wannan

Hajj 2024: Alhazai 600 ƴan ƙasa 1 sun mutu a Saudiyya, an gano silar ajalinsu

An gudanar da aikin hajjin bana cikin tsananin zafi da ya jawo rashin lafiya masu alaka da zafi ga alhazan. Zafin rana a Makkah ya kai 51.8 bisa ma’aunin selsiyos.

Haramain
Musulmi sama da 900 sun rasu a aikin hajjin bana Hoto: Inside Haramain
Asali: Facebook

The Guardian ta wallafa cewa akalla musulmi miliyan 1.8, ciki har da tsofaffi da masu karancin lafiya ne su ka gudanar da aikin hajjin bana cikin zafi mai kuna.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Musulmi na cigiyar yan uwansu ta Facebook

Rahotanni daga Saudiyya sun tabbatar da cewa musulmi na wallafa bayanan ‘yan uwansu a shafukan sada zumunta, musamman manhajar facebook yayin da ake fargabar rasuwarsu.

Channels Television ta wallafa cewa akalla muslimin kasar Misra 600 ne su ka rasu yayin aikin hajjin bana, kuma wasu da yawa sun bata.

Najeriya, Iran, sun rasa mutane a Hajji

Zuwa yanzu kasashen Misra, Jordan, Indonesiya, Iran, Senegal, Tunisiya da Najeriya sun rasa wasu daga alhazansu a kasa mai tsarki.

Kara karanta wannan

Mahara sun dira Jihar Binuwai a babur, an shiga fargaba bayan kashe rayuka

Cututtukan zafi wanda wasu ke jawo asarar rayuka yayin aikin hajji ya fi kamari tsakanin wadanda ke shiga kasa mai tsarki ba a hukumance ba saboda ba za su iya biyan kudin tanadin da aka yiwa mahajjata ba.

An samu karuwar rasuwar alhazai

A wani labarin kun ji cewa adadin alhazan da su ka riga mu gidan gaskiya a kasa mai tsarki na karuwa, inda yanzu haka aka tabbatar da rasuwar alhazan Jordan da Iran da Najeriya.

Kungiyar agaji ta Red Cross a Iran ta tabbatar da rasuwar alhazanta guda biyar, yayin da 14 na Jordan su ka rasu. Sannan wasu mutane 17 kuma ana fargabar sun bata a kasa mai tsarki.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.