An Yi wa Nafiu Bala Barazanar Raba Shi da Rayuwarsa kan ADC? Gaskiya Ta Fito

An Yi wa Nafiu Bala Barazanar Raba Shi da Rayuwarsa kan ADC? Gaskiya Ta Fito

  • Shugaban tsagin ADC a Najeriya, Nafi’u Bala ya yi magana game da barazanar da aka ce an yi masa kan jam'iyyar adawa
  • Nafiu Bala ya musanta rahoton da ke cewa ya yi nadamar rikicin jam’iyya tare da zargin rayuwarsa na cikin haɗari
  • Ya bayyana rahoton a matsayin ƙarya da farfaganda, yana mai cewa bai ba da wata hira ba kuma bai tura kowa ya yi magana madadinsa ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Gombe - Shugaban tsagin jam’iyyar ADC, Nafi’u Bala, ya yi martani game da rahoton cewa an yi masa barazana.

Matashin ya musanta wani rahoto da ya ce ya nuna nadama kan rawar da ya taka a rikicin cikin jam’iyyar.

Nafiu Bala ya ƙaryata nadama kan jawo rigima a ADC
Shugaban tsagin ADC a Najeriya, Nafiu Bala Gombe. Hoto: Hon. Nafiu Bala.
Source: Facebook

Bala, wanda ya tsaya takarar gwamna a Gombe ƙarƙashin ADC a zaɓen 2023, ya ce rahoton da ke ikirarin rayuwarsa na cikin haɗari ƙarya ne, cewar Punch.

Kara karanta wannan

Zance ya kare: Peter Obi ya fice daga jam'iyyar ADC, ya bayyana dalili

Nafiu Bala ya musanta rade-radi kansa

Rahoton ya ambato Bala yana cewa bai yi tsammanin rikicin siyasar cikin jam’iyyar zai kai wannan matsayi mai muni da ya gagari shawo kansa ba.

An kuma ruwaito shi yana cewa ya yi nadamar rawar da ya taka a rikicin ADC saboda lamarin ya kai matsayin da rayuwarsa ta shiga haɗari.

Sai dai a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi, Bala ya bayyana rahoton a matsayin ƙarya, sharri da kuma yunƙurin bata masa suna a idon jama’a.

Bala ya addada cewa bai yi wata hira ba kan rikicin, kuma bai bai wa wani izinin yin magana a madadinsa dangane da lamarin ba.

Ya ce duk wani zargi da ke nuna ya nuna nadama ko yana ƙoƙarin nesanta kansa daga rikicin shugabanci gaba ɗaya ƙarya ne marar tushe.

Nafiu Bala ya yi martani kan zargin da ake yaɗawa kansa
Dan majalisar tarayya daga Kogi, Leke Abejide da Nafiu Bala a Abuja. Hoto: ADC Vanguard.
Source: Twitter

Shugaban tsagin ADC ɗin ya ce bai umurci wani mutum, har da wanda aka ambata a rahoton, ya yi magana a madadinsa kan rikicin ba.

Kara karanta wannan

Sharadin Trump ga Iran yayin da ya ke shirin afkawa kasar da yaki karo na 2

Martanin Nafiu Bala kan yi masa barazana

Bala ya kuma musanta rahotannin da ke cewa rayuwarsa ko ta iyalansa na cikin barazana, yana cewa an kirkiri labarin ne domin tayar da tausayi.

Dangane da zargin da ya haɗa sunan Leke Abejide cikin rikicin, Bala ya ce bai taɓa zargin ɗan majalisar da watsi ko cin amana ba.

Sai dai ya amince cewa ficewar Abejide daga ADC babban rashi ne ga jam’iyyar, yana mai yabawa gudummawar da ya bayar wajen bunƙasa jam’iyyar.

A ƙarshe, Bala ya bayyana rahoton a matsayin farfagandar siyasa da aka shirya domin yaudarar jama’a da kuma tasiri kan shari’ar da ke kotu, cewar Daily Post.

Yan sanda sun musanta kona gidan Nafiu Bala

Mun ba ku labarin cewa ’yan sandan jihar Gombe sun yi ƙarin haske kan jita-jitar cewa an kona gidan Nafiu Bala Gombe wanda ake zargi da jawo rikicin ADC.

Rundunar ta ƙaryata rahoton da ke cewa an kona gidan shugaban tsagin ADC da ake yaɗawa a kafofin sadarwa.

Kwamishinan ’yan sanda, Umar Ahmed Chuso ya bukaci jama’a su yi watsi da rahoton, yana tabbatar da cewa zaman lafiya da tsaro suna nan a Gombe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.