NLC, TUC Sun Tsayar da Lokacin Tattauna Sabon Mafi Ƙarancin Albashi da Gwamnatin Najeriya
- Ƙungiyoyin ƙwadago da suka hada da NLC da TUC sun ce za a fara tattaunawa kan sabon mafi ƙarancin albashi a Najeriya
- Wannan batu ya taso ne a lokacin da Najeriya ta yi bikin ranar ma'aikata da aka gudanar a ranar Juma'a, 1 ga watan Mayu, 2026
- Ƙungiyoyin sun jaddada bukatar a hada kai, a yi magana da baƙi ɗaya idan an tashi tunkarar lamarin kara wa ma'aikatan Najeriya albashi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Ƙungiyoyin ƙwadago a Najeriya sun bayyana cewa za su fara shirin sake tattaunawa kan mafi ƙarancin albashin daga watan Yulin 2026, domin kauce wa jinkirin da aka saba fuskanta a baya.
Shugabannin ƙungiyar NLC da TUC ne suka bayyana hakan a bikin ranar ma’aikata ta shekarar 2026 da aka gudanar a babban birnin tarayya Abuja.

Source: Facebook
Daily Nigerian ta wallafa cewa a yayin bikin ranar ma'aikatan, an nemi a haɗa kai domin tunkarar batun kara albashi da murya ɗaya
NLC ta nemi hadin kai wajen albashin ma'aikata
Jaridar Independent ta wallafa cewa shugaban NLC, Joe Ajaero, ya ce za a fara tattaunawa da wuri ne na da nufin tabbatar da cewa an kauce wa tsaiko da aka saba samu a tattaunawar albashi a baya.
Ya buƙaci ma’aikata da su haɗa kai domin neman albashi mai ma’ana wanda ya dace da halin da tattalin arzikin ƙasar ke ciki a halin yanzu.
A cewarsa:
“Rarrabuwar kai zai raunana karfin tattaunawar ma’aikata. Yayin da ake gab da fara tattaunawar albashi, kungiyar kwadago ta yi gargadin cewa rashin hadin kai zai karya karfin hadin gwiwar ma’aikata."
Ajaero ya kuma nemi a fara biyan ma’aikata cikakken 100% na albashinsu na asali daga watan Yuli 2026 har zuwa lokacin da za a kammala sabuwar yarjejeniya.
Ya bayyana cewa wannan buƙata na da nufin rage raɗaɗin matsin tattalin arziki da ma’aikata ke fuskanta a ƙasar nan ta ɓangarori da dama.
TUC ta magantu kan karin albashi
A nasa jawabin, shugaban TUC, Festus Osifo, ya jaddada buƙatar ƙarfafa tsarin tattaunawa tsakanin gwamnati, ma’aikata da masu daukar aiki.

Source: Facebook
Ya jaddada muhimmancin aiki tare da farfaɗo da majalisar tuntuba ta ƙwadago ta ƙasa domin a saukaka al'amuran albashi.
Osifo ya ce akwai buƙatar yin gyare-gyare a tsarin kula da harkokin ƙwadago domin tabbatar da adalci da ingantaccen hulɗar aiki a Najeriya.
Ya kuma yi gargaɗi kan ci gaba da take dokokin aiki da wasu masu daukar ma’aikata ke yi, yana mai kira da a tabbatar da an tilasta bin dokokin da ake da su.
Shugaban na TUC ya nuna damuwa kan yadda wasu gwamnatocin jihohi ke ƙin aiwatar da dokar mafi ƙarancin albashi ta shekarar 2024 yadda ya kamata, duk da karin kuɗaɗen shiga da wasu jihohi ke samu.
An fara raina ƙarin albashi
A baya, kun ji shugaban kungiyar NLC, Joe Ajaero, ya bayyana cewa ko da ma’aikata za su rika karbar albashin Naira miliyan daya, hakan ba zai amfane su ba.
Shugaban kungiyar ya jaddada cewa hauhawar farashin kayayyaki da tsadar rayuwa sun riga sun cinye karfin ikon sayayya da ma’aikata ke da shi aNajeriya.
Game da sabon mafi karancin albashi, shugaban NLC ya ce tattaunawa za ta gudana ne bisa ka’idojin doka, kuma ba za a gaggauta zama don kauce wa matsaloli.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


