El Rufa'i Ya Maka Hukumar ICPC a Gaban Kotu saboda Iyalansa, Ya Nemi Diyya

El Rufa'i Ya Maka Hukumar ICPC a Gaban Kotu saboda Iyalansa, Ya Nemi Diyya

  • Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, ya shigar da ƙarar kotu ya na kalubalantar kan ICPC bisa zargin hana matarsa da ɗansa ziyartarsa
  • El-Rufai ya ce jami’an ICPC sun hana iyalansa kawo masa abinci, magunguna da sauran abubuwan da yake buƙata, ba tare da wata doka ko umarnin kotu ba
  • Ya kuma zargi jami’an hukumar da tare matarsa da ɗansa tare da tsoratar da su a ranar 7 ga Yuli, 2026 lamarin da ya ce ya saɓa wa haƙƙoƙinsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kaduna – Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya shigar da sabuwar ƙarar N10bn kan Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa da sauran Laifuka (ICPC).

A wannan karon, El-Rufa'i ya garzaya kotu ne bisa zargin cewa jami'an hukumar sun hana matarsa da ɗansa damar ganinsa yayin da yake tsare.

Kara karanta wannan

Maganin mallaka: Matashin da ya birne Kur’ani da wasu kayan tsubbu ya shigo hannu

Tsohon gwamnan Kaduna ya koma gaban kotu
Tsohon gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufa'i Hoto: Nasir El-Rufai
Source: Twitter

Premium Times ta kawo labarin cewa an shigar da ƙarar mai lamba FHC/ABJ/CS/1852/2026 a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja a ranar 13 ga Agusta, 2026.

Zargin El-Rufa'i kan ICPC

A ruwayar jaridar Punch, Nasir El-Rufai ya zargi ICPC da hana matarsa, Aichatou Asabe, da ɗansa, Abba El-Rufai, ziyartarsa.

Lauyansa, Ubong Akpan, ya kuma haɗa Shugaban ICPC da Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya a matsayin na biyu da na uku waɗanda ake ƙara.

El-Rufai ya nemi kotu ta ba shi wasu umarni guda tara, ciki har da tabbatar da cewa haƙƙoƙins da Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999 ya tanada har yanzu suna aiki duk da cewa yana tsare.

Nasir El-Rufai na neman kotu ta biya shi diyya
Tsohon gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya na addua Hoto: Nasir El-Rufa'i
Source: Twitter

Ya yi zargin cewa ci gaba da hana iyalansa ganinsa, musamman domin su kai masa abinci, magunguna da sauran abubuwan da yake buƙata, ba tare da wata hujja ba ya saba doka.

Ya ce hakan ya take haƙƙinsa da Sashe na 34 da 37 na Kundin Tsarin Mulki da kuma Mataki na 5 da 18 na Yarjejeniyar Afirka kan Haƙƙin Dan Adam da Jama'a.

Kara karanta wannan

Zaben 2027: Mai neman takarar gwamnan PDP a Gombe ya fice daga jam'iyyar

An tsoratar da iyalina - El-Rufa'i

Tsohon gwamnan ya kuma zargi jami’an ICPC da tare matarsa da ɗansa tare da tsoratar da su a ranar 7 ga Yuli, 2026 yana mai cewa hakan ya kasance tsoma baki ba bisa ka’ida ba cikin dangantakarsa da matarsa da ɗansa.

Ya nemi kotu ta bayyana cewa ci gaba da hana wanda ake ƙara damar ganin iyalinsa ba tare da hurumin doka ba ya saɓa wa kundin tsarin mulki, ya saba wa doka, kuma ba shi da inganci.

Haka kuma, ya nemi kotu ta umarci waɗanda ake ƙara su ba shi damar ganin ’yan uwansa da lauyansa ba tare da wani cikas ba kuma cikin adalci a duk tsawon lokacin da yake tsare, kamar yadda Babbar Kotun Tarayya ta umarta a baya.

Likitan El-Rufai ya kare kansa

A baya, mun ruwaito cewa likitan tsohon gwamnan jihar Kaduna, Dr. Bello Abubakar ya bayyana cewa bai san Mohammed Bala Aliyu ba, da ya yi rantsuwa da bayanin da ya fitar.

Kara karanta wannan

Kwana 3 kafin zabe, INEC ta ƙara sunan ɗan takara 1 a zaben gwamnan jihar Osun

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa da sauran laifuffuka mai zaman kanta ta ICPC na tuhumar likitan Nasir El-Rufa'i da rubuta takardar lafiya ta bogi da aka yi rantsuwa da ita wajen neman belin tsohon gwamnan a kotu.

Likitan ya bayyana yadda ya duba El-Rufai a lokuta daban-daban tun daga shekarar 2005 zuwa 2026, tare da kokarin wanke kansa daga zargin hukumar ICPC ta ke yi masa na rubuta sakamakon karya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng