Bayan na Pantami, An Tara wa Ɗan Majalisar Tarayya Miliyoyi domin Takara
- Al'ummar mazaɓar Fufore da Song a jihar Adamawa sun tara sama da N22m domin sayawa ɗan majalisar tarayya, fom ɗin sake tsayawa takara a 2027
- Wannan hobbasa ta fito ne daga ɓangarori daban-daban da suka haɗa da manoma, ƴan kasuwa, mata, da matasa waɗanda ke ganin cancantar Hon. Aliyu Boya
- Gudunmawar ta zo ne a daidai lokacin da jam'iyyar APC ta ayyana kuɗaɗen fom, inda fom ɗin ɗan majalisar wakilai ke a kan Naira miliyan 10
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Adamawa - Siyasar Najeriya ta fara sauya salo yayin da ake tunkarar babban zaben shekarar 2027 a kasar.
Wasu al'umma a jihar Adamawa sun tara miliyoyin Naira ga dan majalisar da ke wakiltarsu, Hon. Barista Aliyu Wakil Boya.

Source: Facebook
An tara wa d'an majalisar Adamawa N22m
Ɗaya daga cikin yaransa, Gambo PA Loko shi ya tabbatar da haka ga wakilin Legit Hausa yayin wata tattaunawa.
Loko ya ce an tara sama da Naira miliyan 22 domin dan majalisar da ke wakiltar mazabar Fufore/Song a majalisar tarayya.
"Al'ummar da yake wakiltar ne suka ga dacewar yin karo karon kudi don ganin ya koma majalisa. Kuma abin da zai baka mamaki, da yawansu ma ba su da wata alaka ta kusa da shi.
"Akwai kuma wadanda ya taimaka wajen sama masu aiki, ko 'yan uwansu, sannan wasu sun amfana da ayyukan mazaba da yake yi, kamar raba kayan aikin noma, koyar da sana'o'i da sauransu."
- Gambo PA Loko.
Har ila yau, Loko ya yada wani faifan bidiyo da aka gudanar da taron tara miliyoyin kudin ga dan majalisar domin ci gaba da wakilci na gari.
'Dan majalisa ya samu gudunmuwar jama'a
Matashin wanda shi ne shugaban matasa na ƙungiyar 'City Boy Movement' a karamar hukumar Song ya bayyana farin cikinsa kan wannan gudunmawa da aka ba mai gisansu.
Hon. Boya shi ne shugaban kwamitin majalisa kan cibiyoyin 'yan sanda a Najeriya ya samu wannan gudummawa ne daga masoya daga mazaɓarsa.
Yan mazabar da suka yi wannan hobbasa domin tara kudin sayan fom din takara na ɗan majalisar sun hada da mata, matasa, dattawa, yan kasuwa, manoma da sauransu.
A martaninsu mabambanta, al'ummar yankin sun ce sun dauki matakin ne duba da irin wakilci na gari da Hon. Boya ke yi masu.
Dalilin mutane na tara wa dan majalisar kudi
Sun ce a jihar Adamawa, Hon. Boya ya fita daban a cikin ƴan siyasa saboda yadda ya ke inganta rayuwar al'ummar mazaɓarsa.

Source: Original
Wata Hauwa'u Aliyu Sani, wadda take sana'ar sayar da garin danwake da na kunun tsamiya, ta shaida wa Legit Hausa cewa ta tura wa d'an majalisar N20,000 daga ribar da take samu.
"Ni ma na bada tawa gudunmawar. Kawai na ga ya cancanta ne. Ni kai na na amfana da shi, don na taba samun jarin N150,000 daga wajensa, amma an kwana biyu. To ai ruwan da ya duke ka shi ne ruwa, mu mun ji dadin mulkinsa, ko ma wakilci zan ce, duka dai."
- Hauwa'u Aliyu Sani.
An tabbatar da cewa Boya na daga cikin ƴan siyasa a jihar da suka fi kusanci da al'umma wanda hakan ya sake tabbatar da salon shugabancinsa.
Mutane da dama sun ba da gudummawa kama daga N2,000, N5,000, N10,000, N50,000 har zuwa N500,000 da N1m.
Kalli bidiyon taron hada kudin wanda wani Abdulaziz Umar ya wallafa a shafinsa na Facebook a kasa:
Kudin sayen fom din takara a APC
Tun da fari, Legit Hausa ta ruwaito cewa jam'iyyar APC dai ta fitar da kudin sayan fom da nuna sha'awar neman takara domin fafatawa a zaben 2027.
APC ta ayyana kudin fom da nuna sha'awar takara na shugaban kasa kan N100m yayin da fom na gwamna zai kai N50m.
Sai kuma na sanata an ajiye a kan N20m, sannan dan majalisar wakilai N10m sai kuma na karshe dan majalisar jiha kan N5m.
Asali: Legit.ng


