Gwamna Ya Amince da Sabon Albashin N70000 ga Ma'aikatan Kananan Hukumomi a Gombe
- Gwamnan Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya amince da fara biyan sabon mafi ƙarancin albashi ga dukkan ma’aikatan ƙananan hukumomin jihar
- Wannan sabon albashi na N70,000 zai fara aiki ne daga watan Mayun 2026, kuma zai shafi ma’aikatan ƙananan hukumomi 11, malamai da ma’aikatan lafiya
- Gombe na ɗaya daga cikin jihohin farko da suka fara biyan sabon mafi ƙarancin albashi a 2024, amma a lokacin, tsarin bai shafi kananan hukumomi ba
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Gombe – Gwamnan Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya bayar da umarnin fara aiwatar da cikakken sabon mafi ƙarancin albashi ga dukkan ma’aikatan ƙananan hukumomin jihar.
Wannan sanarwa, wadda shugaban ma’aikatan gwamnatin jihar, Farfesa Muazu Shehu, ya fitar a ranar Laraba, ta kawo ƙarshen dogon jiran da ma’aikatan suka yi.

Source: Twitter
Gwamna Inuwa zai fara biyan sabon albashi
Rahoton Jaridar Daily Trust ya nuna cewa umarnin ya ƙunshi biyan ragowar kashi 43 na albashin da ya rage, wanda hakan ke nufin ma’aikatan yanzu za su fara karɓar kashi 100 na sabon albashin tun daga watan Mayun 2026.
Rahoton ya nuna cewa ma'aikatan kananan hukumomin Gombe za su dawo karbar N70,000 a matsayin sabon mafi karancin albashinsu.
Umarnin gwamnan zai shafi dubban ma'aikata da suka haɗa da:
- Ma'aikatan dukkan ƙananan hukumomi 11 na jihar.
- Ma'aikatan hukumomin ilimi na matakin farko (LEA).
- Ma'aikatan asibitoci na matakin farko.
Yadda aka samu damar biyan sabon albashin
Farfesa Muazu Shehu ya bayyana cewa samun kyautatuwar yanayin tattalin arziƙi a matakin ƙananan hukumomin ne ya ba gwamnati damar ɗaukar wannan mataki ba tare da tunanin fuskantar cikas ba.
A cewarsa, kudaden da kananan hukumomi ke iya samar wa yanzu zai ba gwamnati damar biyan ma'aikata albashinsu ba tare da wani tasgaro ba, in ji rahoton The Punch.

Kara karanta wannan
Arewa da Kudu za su amfana da Tinubu ya nemi izinin sake ciyo bashin Dala miliyan 516
Ya ƙara da cewa:
"Muna sa ran wannan mataki zai ƙarfafa gwiwar ma'aikata, ya haɓaka aiki, sannan ya inganta yadda ake gudanar da ayyuka a matakin grassroots."

Source: Original
Martanin jama'a da ma'aikata
Idan za a iya tunawa, jihar Gombe na ɗaya daga cikin jihohin farko da suka fara biyan sabon mafi ƙarancin albashi tun bayan sanya hannu kan dokar a shekarar 2024.
Sai dai a lokacin, Gwamnatin Muhammadu Inuwa Yahaya ba ta iya samar wa ƙananan hukumomi cikakken kudin da suke samu ba, wanda ya jawo jinkirin aiwatar da albashin ga ma'aikata.
Ƙungiyoyin kare haƙƙin bil'adama da sauran jama'a sun daɗe suna yin kira ga gwamnati da ta lura da halin matsin rayuwa da ma'aikatan matakin kananan hukumomi ke ciki.
Halin da ma'aikata ke ciki a jihohi 3
A wani labari, mun ruwaito cewa, ma'aikatan kananan hukumomi ba su fara shan romon sabon mafi karancin albashi na kasa ba a jihohin Kaduna, Borno da Gombe.
Ƙungiyar Ma’aikatan Kananan Hukumomi ta Ƙasa (NULGE) ce ta yi wannan zargin, tana mai cewa gwamnatocin wadannan jihohi sun kasa fara biyan N70,000 ga mambobinta.
Kwamitin NEC na NULGE ya bayyana kin biyan sabon albashi a matsayin “zalunci da rashin adalci”, musamman ganin matsin halin tattalin arziki da ake ciki a ƙasar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

