Tsadar Fetur: Kudin Sufuri Ya Yi Tashin Gwauron Zabi a Kaduna

Tsadar Fetur: Kudin Sufuri Ya Yi Tashin Gwauron Zabi a Kaduna

  • Masu ababen hawa sun yi ƙarin kuɗin da suke karɓa daga wajen fasinjoji a birnin Kaduna biyo bayan ƙarin kuɗin fetur
  • Ƙarin kuɗin na fetur dai ya sanya a yanzu masu adaidaita sun kusan ninka kuɗin da suke karɓa a hannun fasinjojinsu
  • Wani mai sana'ar ta Keke Napep ya bayyana cewa akwai yiwuwar kudin su ƙaru saboda ba a samun mai a gidajen NNPCL

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Masu ababen hawa sun yi ƙarin kuɗin sufuri da fasinjoji ke biya domin zirga-zirga a a birnin Kaduna.

Ƙarin kuɗin dai na zuwa ne biyo bayan ƙarin kuɗin man fetur da kamfanin mai na ƙasa (NNPCL) ya yi.

Kara karanta wannan

'Yan majalisa sun yi martani kan karin kudin fetur, sun ba gwamnati shawara

Farashin sufuri ya tashi a Kaduna
Masu adaidaita sahu sun yi karin kudi a Kaduna Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Ƴan adaidaita sun yi ƙarin kuɗi a Kaduna

Jaridar The Punch ta ce wani bincike da NAN ta gudanar a ranar Laraba a Kaduna ya nuna cewa kuɗin adaidaita sahu daga babbar kasuwa zuwa Sabo yanzu ya kai N500 saɓanin N300 da ake biya a baya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sauran wuraren da suka samu ƙarin sun haɗa da Gonin Gora zuwa Kasuwa wanda ya koma N500 saɓanin N300, Kakuri zuwa Kasuwa wanda ya koma N400 daga N300 sai Kasuwa zuwa Kawo wanda ya koma N300 daga N200.

Jaridar Vanguard ta ce wasu mutane sun ƙara da cewa ƙarin kuɗin da aka samu ya shafi har da ƴan Achaɓa waɗanda suka ninka kuɗin da suke karɓa.

Meyasa aka yi ƙarin kuɗin?

Wani mai keken Napep mai suna Malam Abubakar Sa’idu, ya ce akwai yiwuwar a ƙara kuɗin da ake biya a halin yanzu nan da kwanaki masu zuwa.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun hallaka jami'in tsaro, sun cinnawa ofishin 'yan sanda wuta

Ya ce yana da wuya a samu mai a gidajen mai na NNPC inda ya ƙara da cewa sai mutum ya kusan shafe wuni ɗaya yana jira a layi.

"Saboda haka, a yanzu mun koma saya a wajen ƴan buburutu a kan kuɗi Naira 1,400 kan kowace lita."
"Fasinjojin ma ba su ƙorafi saboda kowa ya san halin da muka tsinci kanmu a Najeriya."

- Malam Saidu Abubakar

Ƴan majalisa sun caccaki ƙarin kuɗin fetur

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙungiyar marasa rinjaye ta majalisar wakilai ta yi magana kan ƙarin kuɗin man fetur da aka yi a Najeriya.

Ƙungiyar marasa rinjayen ta yi Allah wadai da ƙarin farashin man fetur da kamfanin NNPCL ya yi wanda ta bayyana a matsayin bai dace ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng