Manyan Arewa Sun ba da Mafita kan Ambaliyar Ruwan da Ake Hasashen Za a Yi a Jihohi 30
- Ƙungiyar ACF ta tunatar da gwamnatoci muhimmancin ɗaukar matakan kariya gabanin faruwar ambaliyar da ake hasashe a daminar bana
- Manyan Arewa sun buƙaci gwamnatin tarayya, da ta jihohi da ƙananan hukumomi su shirya domin daƙile illar ambaliya
- ACF ta kuma yi kira ga mazauna garuruwan da ake hasashen za a iya fuskantar ambaliya da su kare mahallansu, ka da su toshe hanyoyin ruwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Kungiyar Dattawan Arewa (ACF) ta bukaci gwamnatoci da kuma mutanen da ke zaune a yankunan da ambaliya ke yawan faruwa da su dauki matakan kariya.
Kungiyar ACF ta buƙaci a gaggauta ɗaukar matakan kariya domin rage illar ambaliyar ruwa da ake hassshen faruwarta a shekarar 2025.

Asali: Twitter
Daily Trust ta tattaro cewa hakan na kunshe ne a wata sanarwa da mai magana da yawun ACF na ƙasa, Farfesa Tukur Nuhammad ya fitar
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Manyan Arewa sun nuna damuwa kan ambaliya
ACF ta nuna damuwa kan hasashen da Hukumar Kula da Madatsun Ruwa ta Kasa (NIHSA) ta fitar, wacce ta ce akalla garuruwa 1,249 a kananan hukumomi 176 na jihohi 30 da Abuja na fuskantar barazanar ambaliya.
Kungiyar ta ce ambaliyar ruwa na kara dagula matsalolin tattalin arziki da zamantakewa da ake fama da su a fadin kasar nan.
ACF ta ce:
"Yankunan da ba su yi kyakkyawan shiri ba ana samun asarar rayuka, lalacewar gonaki, asarar kadarori, matsin rayuwa da ƙarancin abinci.
"Game da hasashen 2025, da alama ambaliyar za ta zo a lokacin da mutane ke cikin mawuyacin hali idan aka yi la'akari da wahalar da jama'a ke ciki."
Kungiyar ACF ta bayar da shawarwari
ACF ta yaba da kokarin wayar da kan jama’a da gwamnatin tarayya ke yi, amma ta nuna cewa yawancin al’ummomi ba su da fahimta ko shiri duk da cewa damina ta fara kankama a wasu yankuna.
Kungiyar ta bukaci hukumomin tarayya, jihohi da kananan hukumomi da su kara himma wajen wayar da kai da shirye-shiryen kariya.

Asali: UGC
Ta kuma bukaci hukumomin agaji su tanadi abinci, magunguna, ruwa da sauran kayan bukatu don tallafawa wadanda za su iya fuskantar ambaliya.
ACF ta yi kira da a gyara hanyoyi, gadoji, makarantun gwamnati, asibitoci da kasuwanni kafin ambaliyar ta zo.
Ƙungiyar ta kuma bukaci a aiwatar da doka da ka’idojin gine-gine da na kare muhalli don kauce wa hadurra da asara.
Manyan Arewa sun ba ƴan Najeriya shawara
Bugu da ƙari, ACF ta ja hankalin jama’a kan su kare muhallansu ta hanyar guje wa toshe magudanan ruwa da zubar da shara a wuraren da ba su dace ba.
ACF ta kara da cewa za ta ci gaba da goyon bayan duk wani kokari na kare rayuka da dukiyoyin al’umma a lokacin wannan barazana ta ambaliya.
Jerin jihohin da ake hasashen ambaliya
A wani labarin, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta fadi jihohi 19 da ake hasashen za a samu ambaliyar ruwa mai muni a daminar bana a Najeriya.
Ministan ruwa da tsaftar muhalli, Farfesa Joseph Utsev ya bayyana cewa a karshen watan Yuli da muke ciki za a samu ambaliyar ruwa a jihohi da dama.
Ministan ya ce ambaliyar ruwan na zuwa ne saboda mamakon ruwa da za a rika yi a kwanakin da kuma toshe magudanar ruwa da mutane ke yi.
Asali: Legit.ng