Boko Haram Ta ba Gwamnati Wa'adin Kwanakin Kashe Mata da Yara 176 a Jihar Kwara
- ’Yan ta’addan Boko Haram sun kara tura sako ga gwamnatin Najeriya game da kananan yara, mata da mazan da ta yi garkuwa da su daga Kwara
- 'Kungiyar ta kutsa garin Woro da ke jihar Kwara inda ta yi awon gaba da mutane kusan 200, sannan ta aika sako ga mazauna yankin da gwamnati
- Sarkin yankin ya tabbatar da barazanar, ya ce an ba daya daga cikin wadanda aka sace damar kiran iyalanta domin shaida masu halin da suke ciki
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kwara – 'Yan Boko Haram ne sun yi barazanar kashe mutane 176 mata da kananan yara da suka sace daga al’ummar Woro da ke karamar hukumar Kaiama a jihar Kwara.
Kungiyar ta yi barazanar cewa za ta aikata wannan mummunan aiki da ta kudiri aniya, idan har gwamnatin Najeriya ba ta biya mata bukatunsu cikin mako guda ba.

Source: Original
Channels TV ta wallafa cewa rahotanni sun nuna cewa maharan sun isar da wannan sako ne ta bakin wadanda suka sace bayan sallar Juma’a da ta gabata.
'Yan Boko Haram sun yi barazanar kashe mutane
Jaridar Punch ta wallafa cewa mazauna yankin da iyalan wadanda abin ya shafa sun tabbatar da barazanar, inda suka ce an sanar da su ne ta hanyar daya daga cikin wadanda aka sace.
Sarkin yankin, Salihu Bio, wanda matarsa na cikin wadanda aka sace, ya tabbatar da wannan lamari ga manema labarai a ranar Litinin 27 ga watan Afrilu, 2026.
Ya bayyana cewa daya daga cikin matan da aka sace ta samu damar tuntubar iyalanta tare da isar da sakon daga hannun ’yan ta’addan.

Source: Facebook
A cewarsa:
“Wadanda aka sace sun shaida mana cewa bayan sallar Juma’a, ’yan ta’addan sun ce gwamnati ba ta dauki lamarin da muhimmanci ba. Sun kuma ce idan babu wani mataki cikin mako guda, za su fara daukar matakai masu tsauri.”

Kara karanta wannan
2027: Ana rade radin za a sauya shi, matasa sun tara wa Sanata Ndume kudin fam sama da N38m
Boko Haram: An shiga fargaba a Kwara
Sarkin ya kara da cewa ’yan ta’addan sun nuna damuwa kan yadda gwamnati ba ta nuna kwazo wajen tattaunawa da su ba, duk da kudin da suke kashewa wajen kula da wadanda suka sace.
A wani bangare, wata majiya daga cikin al’ummar yankin da ta bukaci a sakaya sunanta ta bayyana cewa barazanar ta fi yadda ake zato muni.
Ta ce maharan sun yi barazanar aurar da wasu daga cikin ’yan matan da aka sace, sannan su kashe wadanda suka dauka nauyi ne a gare su idan ba a cimma matsaya cikin lokacin da suka bayar ba.
Majiyar ta ce:
“Sun koka cewa suna kashe kudi da kayan aiki wajen ciyar da wadanda suka sace amma babu wani sakamako. Sun ce idan ba a cimma yarjejeniya a cikin mako guda ba, za su fara aurar da wasu daga cikin ’yan matan, sannan su kashe wasu.”
'Yan ta'addan Boko Haram sun dasa bam

Kara karanta wannan
Asiri ya tonu: An kama mai taimaka wa yan bindiga su samu kudi a Sakkwato, ya fara bayani
A baya, mun wallafa cewa an shiga jimami a jihar Borno bayan 'yan ta'addan Boko Haram sun dasa bam din da ya yi sanadiyyar rasuwar mutanen da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba.
Bam din ya tashi da mutanen da suka fita neman na sanyawa a bakin salati, inda aka rasa rayukan mutane da dama suka rasa rayukansu yayin da suka tsaka da gudanar da harkokin yau da kullum.
Majiyoyi sun bayyana cewa an gano gawarwakin mutane kusan 20 yayin da ake fargabar adadin wadanda suka mutu zai iya wuce hakan bayan an kara zurfafa bincike idan kura ta lafa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
