'Yan Boko Haram Sun Dasa Bam a Borno, Mutane da Dama Sun Rasu

'Yan Boko Haram Sun Dasa Bam a Borno, Mutane da Dama Sun Rasu

  • An shiga jimami a jihar Borno bayan 'yan ta'addan Boko Haram sun dasa bam din da ya yi sanadiyyar rasuwar mutanen da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba
  • Bam din ya tashi da mutanen da suka fita neman na sanyawa a bakin salati, inda aka rasa rayukan mutane da dama suka rasa rayukansu
  • Majiyoyi sun bayyana cewa an gano gawarwakin mutane kusan 20 yayin da ake fargabar adadin wadanda suka mutu zai iya wuce hakan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Borno - 'Yan ta'addan Boko Haram sun hallaka akalla mutane kusan 20 da suka haɗa da masunta da masu saran itace, bayan dasa bam a jihar Borno.

Wasu mutane da ba a tantance adadinsu ba sun samu raunuka sakamakon tashin bam din da aka dasa a gefen garin Gwoza da ke jihar Borno.

Kara karanta wannan

Rashin imani: Bam ya tashi da mutane da yawa, yan ta'adda sun bi su da harbi a Borno

'Yan Boko Haram sun dasa bam a Borno
Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum Hoto: @GovBorno
Source: Original

Jaridar Leadership ta kawo rahoton cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 11:00 na safe a ranar Alhamis, 23 ga watan Afirilun 2026.

'Yan Boko Haram sun kashe mutane a Borno

Lamarin ya auku ne a ƙauyen Hambagda da aka sake tsugunar da mutane, wanda ke da nisan ƴan kilomitoci daga garin Gwoza.

A cewar majiyar jami'an sa-kai na Civilian JTF, waɗanda abin ya shafa masu saran itace ne da suka tafi neman makamashin girki don tallafa wa iyalansu.

“Rana ce ta baƙin ciki a gare mu a garin Gwoza, mun rasa masu saran itace kusan 20 sannan wasu da dama sun samu raunukan harbin bindiga."
"Yan ta’addan sun dasa bama-bamai a kan hanyar, kuma bayan fashewar su, sun buɗe wa farar hular da ba su da kariya wuta."

- Wata majiya

Bam ya tashi da bayin Allah a jihar Borno

Wata majiyar kuma ta ce mutanen da abin ya shafa, waɗanda galibinsu manoma ne da masu tattara itace, sun shiga daji na kusa ne don gyara gonakinsu gabanin shigowar damina mai zuwa lokacin da aka kai musu harin.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun zo da sabon salon ta'addanci, sun kashe basarake da iyalansa

Wasu majiyoyin sun tabbatar da cewa ya zuwa yanzu an gano gawarwaki 18 a wasu ƙauyuka da ke kusa da garin Gwoza, rahoton Daily Post ya tabbatar da hakan.

'Yan Boko Haram sun kashe mutane a Borno
Taswirar jihar Borno, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Sun kuma yi gargaɗin cewa adadin waɗanda suka mutu na iya ƙaruwa, tunda har yanzu ba a san inda wasu mutane da dama suke ba.

Mazauna yankin sun ce maharan suna zagaye yankin ta hanyar kai jerin hare-hare na tashin hankali, lamarin da ya tada sabuwar fargaba game da tsaro a yankunan manoma yayin da lokacin shuka ke gabatowa.

An dauki mataki kan hare-haren Boko Haram

A wani labarin kuma, kun ji cewa Majalisar dattawan Najeriya ta nuna matukar damuwa kan hare-haren da 'yan ta'addan Boko Haram suka kai a Borno.

Majalisar dattawan ta umarci babban hafsan hafsoshi da sauran shugabannin rundunonin tsaro da gudanar da bincike kan hare-haren.

An bukaci su yi bincike a kan harkokin aiki da kayan aiki bayan hare-haren da 'yan ta'addan Boko Haram suka kai kan sansanonin sojoji a Benisheikh da Monguno da ke jihar Borno

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng