Mutane 12 Sun Sha da Kyar yayin da Sojojin Najeriya Suka Yi Luguden Wuta a Borno
- Hare-haren da sojojin Najeriya suka kai sansanin yan ta'addan Boko Haram sun yi sanadin kubutar mutane 12 da aka yi garkuwa da su
- Rahotanni sun nuna cewa wadanda suka kubuta na daga cikin mutane 416 da mayakan Boko Haram suka sace a jihar Borno
- Mazauna yankin sun tabbatar da faruwar wannan lamarin, sun bukaci gwamnati ta tashi tsaye wajen kubutar da sauran mutanen
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Borno, Nigeria - Mutane 12 daga cikin waɗanda mayaƙan Boko Haram suka sace a ƙauyen Ngoshe da ke ƙaramar hukumar Gwoza a jihar Borno sun kubuta, yayin da har yanzu mutum 404 ke hannun ‘yan ta’addan.
Wannan na zuwa ne bayan wa’adin awa 72 da ‘yan ta’addan suka bai wa gwamnati tare da barazanar ci gaba da tsare sauran mutanen da ke hannunsu.

Kara karanta wannan
Hankalin iyalan mutum 416 da Boko Haram ta sace ya tashi yayin da wa'adi ya kusa cika

Source: Original
Yadda mutanen suka kubuta a Borno
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa majiyoyi daga Pulka sun bayyana cewa waɗanda suka tsere, maza 10 da mata biyu, sun samu damar guduwa ne bayan sojoji sun yi luguden wuta a wani sansanin Boko Haram.
“Ɗaya daga cikin waɗanda suka dawo gida ya shaida mana cewa hare-haren sojoji ne ya sa ‘yan ta’addan suka tsere, suka bar wasu daga cikin mutanen da suka kama,” in ji majiyar.
Kungiyar Borno South Youth Alliance ta tabbatar da faruwar lamarin, inda shugabanta, Samaila Kaigama, ya ce waɗanda suka gudo, na cikin aminci a wani gari da ke kusa.
Boko Haram na rike da mutane 404
Ya bayyana sunayen wasu daga cikinsu da suka haɗa da Aisha Audu mai shekaru 20, Aisha Idrisa mai shekaru 17 da Musa Umar mai shekaru bakwai, da sauransu.
Duk da wannan cigaba, Kaigama ya jaddada cewa har yanzu mafi yawan waɗanda aka sace suna hannun ‘yan ta’addan, inda ake hasashen akwai sauran mutane 404.

Kara karanta wannan
Majalisa ta dauki mataki kan hare haren Boko Haram da suk kashe manyan sojojin Najeriya
“Duk da muna farin ciki da wannan ci gaba, dole ne mu bayyana cewa har yanzu mutane da yawa suna tsare a hannunsu,” in ji shi.
Yadda Boko Haram ta sace mutane 416
An sace mutanen ne bayan harin da ‘yan Boko Haram suka kai ranar 4 ga Maris, 2026 kan sansanin sojoji da ke ƙauyen Ngoshe, kamar yadda Leadership ta ruwaito.
Wannan ya tilasta wa mutane da dama tserewa zuwa garin Pulka, inda iyalansu ke ƙoƙarin tattaunawa da ‘yan ta’addan domin a sako su.

Source: Twitter
A ranar 20 ga Afrilu, wani ɓangare na Boko Haram ƙarƙashin jagorancin Imam Abu Ubaida ya fitar da bidiyo yana neman a biya kuɗin fansa.
Sun kuma yi gargaɗin cewa duk wani yunƙuri na ceto mutanen da ƙarfi zai fuskanci turjiya, tare da barazanar kai su wurare daban-daban.
Sojoji sun kashe mayakan ISWAP 30
A wani rahoton, kun ji cewa dakarun sojojin sama na Najeriya sun kai wasu hare-hare masu zafi kan 'yan ta'addan kungiyar ISWAP a jihar Borno.
Bayanai sun nuna cewa dakarun sojojin sun kashe sama da ‘yan ta’addan ISWAP 30 a jerin hare-hare da aka kai a yankin Tafkin Chad na jihar.
Farmakin sojojin ya biyo bayan sahihan bayanan sirri, sa ido da kuma bincike da suka nuna ƙaruwar ayyukan ta’addanci, gami da jigilar kayan aiki ta hanyoyin ruwa a kewayen yankin tsibirin Kaniram.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng