Gobara Ta Lalata Dukiyar Miliyoyin Naira a Gidan Sarki a Abuja
- Mummunar gobara ta tashi a gidan wani sarki a birnin tarayya Abuja, inda ta jawo asarar dukiyar miliyoyin Naira gare shi da iyalan shi
- Rahotanni sun bayyana cewa mutanen da ake kusa sun kai masa dauki yayin da wutar ta shi, amma duk da haka ta yi mummunar barna
- Bayan kashe wutar, shugaban karamar hukumar Gwagwalada, Alhaji Kasim Mohammed Ikwa ya fitar da sako yana yi wa sarkin jaje
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Wata gobara da ta tashi da sassafe ta lalata gidan Sarkin Dawakin Zuba da ke karamar hukumar Gwagwalada a Babban Birnin Tarayya, Alhaji Musa Danliman.
Rahotanni sun nuna cewa tashin wutar ya jawo wa Alhaji Musa Danliman asarar dukiya mai dimbin yawa ta miliyoyin Naira.

Kara karanta wannan
2027: Ana rade radin za a sauya shi, matasa sun tara wa Sanata Ndume kudin fam sama da N38m

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa jama'a da dama ciki har da shugaban karamar hukumar Gwagwalada sun taya sarkin jaje.
Gobara ta tashi a gidan sarki
Wani dan uwan sarkin dawakin Zuba, Ibrahim Bala, ya ce lamarin ya faru da misalin karfe 4:48 na asubahin ranar Juma’a, daidai lokacin kiran sallar asuba.
Ya bayyana cewa ana zargin gobarar ta samo asali ne daga wajen janareta, inda ta tashi kwatsam ta kuma bazu zuwa babban ginin gidan.
A cewarsa, an fara gano gobarar ne bayan hayaki mai kauri ya fara tashi daga daya daga cikin dakunan gidan yayin da mazauna gidan ke barci.
“Da na ji warin waya na tashi kuma na ga hayaki mai yawa yana fitowa daga wani bangare na gidan, sai na yi sauri na fita na sanar da sauran ‘yan uwa, wadanda suka fito daga dakunansu,”
In ji shi.
Gobara ta yi barna a gidan sarki
Bala ya kara da cewa gobarar ta mamaye dukan ginin, inda ta kone kayayyaki masu muhimmanci da na’urorin lantarki kafin agaji daga makwabta da jami’an kashe gobara ya iso.
“Duk da cewa mun yi asarar komai, muna godiya ga Allah da babu wanda ya rasa ransa ko ya jikkata. Wannan kadai ya isa mu gode masa,”
In ji shi.
An yi wa sarki jaje kan gobara
A wani bangare kuma, zababben shugaban karamar hukumar Gwagwalada, Alhaji Kasim Mohammed Ikwa, ya jajanta wa wanda lamarin ya shafa da iyalansa.
Ikwa, wanda ya kai ziyara gidan a ranar Asabar, ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici tare da yi musu addu’ar samun juriya da saukin radadin asarar da suka yi.

Source: Facebook
Wani mai amfani da Facebook, Sule Mustapha, ya wallafa hotunan barnar da gobarar ta yi a shafinsa yayin ziyarar shugaban karamar hukumar.
An yi gobara a kotun Amurka
A wani labarin, mun kawo muku cewa an samu wata mummunar goba a wani tsohon ginin da ya hada kotu da ma'aikatu a kasar Amurka.
Tun bayan tashin wutar jami'an kashe gobara suka isa wajen da gaggawa, inda suka shafe sa'o'i suna kokari kafin nasarar kashe ta.
Bayan kashe wutar, an fitar da dukkan jami'an gwamnati da suke aiki a wajen tare da kaddamar da bincike domin gano dalilin tashin gobarar.
Asali: Legit.ng

