"Kada Ku Bar Turawa Su Yaudare Ku": Gumi Ya Shawarci Gwamnati kan Sulhu da Ƴan Ta'adda
- Fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi sha'awarci gwamnati ta duba batun tattaunawa da ƴan ta'adda
- Ya gargadi gwamnati kada ta bi ra’ayin kasashen yamma na kin sasanci da masu ɗauke da miyagun makamai suna kashe bayin Allah a Najeriya
- Dr Ahmad Gumi ya kuma danganta karuwar ayyukan taaddanci a Najeriya da bude iyakokin kasar, wanda ya ba ƴan ta'adda damar kwararowa
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kaduna – Fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Abubakar Gumi, ya bayyana cewa bai kamata gwamnatin Najeriya ta ci gaba da bin abin da ya kira taken kasashen yamma ba.
Ya ce batun da ƙasashen Turai ke yi na kin tattaunawa da ‘yan ta’adda ba duk lamari ne da zai kai Najeriya ya baro ta a halin da ake ciki.

Kara karanta wannan
Gwamna zulum ya fadi manyan dabaru 2 da ke ba ƴan ta'adda damar kai wa sojoji hari

Source: Facebook
A wani rubutu a shafinsa na Facebook, Ahmad Gumi ya bayyana cewa tattaunawa ita ce hanya mafi dacewa da za ta iya kawar da tashin hankali da kasar ke ciki a halin yanzu.
Shawarar Ahmad Gumi kan ƴan ta'adda
Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya ce Najeriya za ta ci gaba da zama cikin wannan rikici matuƙar ba a shawo kan matsalar tsaron iyakoki ba.
Ya jaddada cewa bude iyakoki na sauƙaƙa shigowar makamai, kwayoyi da abubuwan fashewa, wanda ke kara dagula yaki da ta’addanci da ake yi.
Malamin ya kuma kawo misali da Amurka, wadda a zahiri take nuna kin tattaunawa da ‘yan ta’adda, amma a lokaci guda tana tattaunawa da Iran kan rikicin da ya shafi mashigar ruwa ta Hormuz.
'Ana sulhu idan bukata ta tashi' – Gumi
Sheikh Gumi ya ce wannan na nuna cewa a aikace, kasashe na yin sulhu idan bukatar hakan ta taso, don haka Najeriya ma ya kamata ta yi koyi da hakan wajen neman mafita.

Kara karanta wannan
Yadda rikicin Iran ya buɗe kasuwar man Najeriya, ƙasashen Turai sun zo neman agaji
Malamin ya yi karin haske da cewa rikice-rikicen duniya sun nuna cewa babu wata ƙasa ko bangare da ke da cikakken iko kan amfani da ƙarfi a kan wasu.

Source: Facebook
A cewarsa, sau da yawa manyan kasashe kan guji sulhu saboda tsoron abin da za su kira kaskanci a teburin tattaunawa.
Ya bayyana cewa Pakistan ta taka rawa a matsayin mai shiga tsakani domin rage tashin hankali a wasu rikice-rikice, yana mai tambayar ko hakan na nufin tana taimakawa ta’addanci, wanda ya ce ba haka ba ne.
Dangane da Najeriya, Gumi ya ce muddin iyakoki ba su da tsaro, to za a ci gaba da fuskantar hare-haren ta'addanci a Najeriya.
Gumi ya tunatar da majalisa
A baya, mun wallafa cewa fitaccen Malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Gumi ya buƙaci Majalisar Dattawa ta shiga batun yawan kai hare-hare da sojoji kan fararen hula.
Ya ce ta’aziyya kaɗai ba ta wadatar ba, ganin yadda yanzu lamarin kai hari bisa kuskure ke neman zama ruwan dare a wasu daga cikin jihohin Najeriya, musamman a Arewa.
Rahotanni sun ce wani sabon hari da sojojin suka kai bisa kuskure kan wata kasuwa da ke iyakar Borno da Yobe ya kashe mutum 200, sai dai gwamnati ta ce an rufe kasuwar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng