Ma'aikatar Gwammatin Tarayya Ta Gaza Bayanin Yadda Aka Kashe Tiriliyoyin Naira a Najeriya

Ma'aikatar Gwammatin Tarayya Ta Gaza Bayanin Yadda Aka Kashe Tiriliyoyin Naira a Najeriya

  • Jami'an ma'aikatar kudi sun gaza bayanin yadda aka kashe wasu biliyoyin Daloli a rahoton binciken kudi na NEITI
  • Sai dai daga bisani ma’aikatar ta ce rashin wasu muhimman bayanan kudi ne ya hana ta amsa tambayoyin binciken NEITI
  • Babban sskataren ma'aikatar ya bayyana abin da ya jawo hakan yayin da ya gurfana a gaban kwamitin Majalisar dattawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Ma’aikatar Kudi ta Tarayya ta bayyana dalilin da ya sa ta kasa ba da amsa nan take kan wasu tambayoyin da suka shafi biliyoyin Daloli da aka gano a Rahoton Binciken Bangaren Mai da Gas na 2021 zuwa 2023.

Ma’aikatar ta bayyana hakan ne ranar Alhamis yayin da babban Sakatarenta, Raymond Omachi, ya bayyana gaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan Asusun Jama’a da ke binciken rahoton da hukumar NEITI ta wallafa.

Kara karanta wannan

Gwamntin Tinubu na neman 'ƙaryata' rahoton da ƙasar Amurka ta fitar kan Najeriya

Majalisar dattawa.
Zauren Majalisar dattawan Najeriya yayin da sanatoci ke cikin zama a Abuja Hoto: Senate Nigeria
Source: Facebook

Daily Trust ta ce Omachi ya zargi Kamfanin Man Fetur na Najeriya (NNPCL) da Hukumar Kula da Harkokin Man Fetur (NUPRC) da kin samar da muhimman bayanan kudi da ake bukata domin amsa tambayoyin da rahoton ya gabatar.

An samu kura-kurai a harkokin kudi

Rahoton NEITI ya bayyana wasu kura-kurai da bambance-bambance a harkokin kudi da ma’aikatar ta ce ba ta iya yin karin bayani a kansu saboda rashin hadin kai daga wasu hukumomin da abin ya shafa a bangaren mai.

Daya daga cikin batutuwan ya shafi bashin Dala biliyan 3 da aka karba a shekarar 2012 domin biyan kudaden tallafin man fetur.

NEITI ta ce har yanzu ba a yi cikakken bayani kan yadda aka dawo da bashin ta hanyar kudaden shiga na Tarayya na wata-wata ba, karkashin yarjejeniyoyin Pre-Export Financing da Project Eagle.

Rahoton ya kuma nuna cewa a shekarar 2021, kamfanin NLNG ya biya NNPCL dala miliyan 722.6 a matsayin rarar riba da kudin ruwa a madadin Tarayya.

Kara karanta wannan

Shugaba Bola Tinubu ya tabo maganar raba Najeriya saboda sabani

Sai dai an ce ba a shigar da kudaden cikin Asusun Tarayya ba, sannan kuma ba a yi cikakken bayani kan yadda aka yi amfani da su ba.

Ina kudaden matatun mai suka shige?

Rahoton NEITI ya kuma yi tambaya kan kashe sama da Naira biliyan 200 da aka yi wajen matatun man Najeriya a 2021, duk da cewa babu daya daga cikin matatun da ke aiki a lokacin.

Omachi ya ce Ma’aikatar Kudi ba ta da hannu kai tsaye a dukkan harkokin da rahoton ya gabatar, yayin da kamfanin mai na NNPCL da NUPRC ba su samar da bayanan da ake bukata ba.

Ya ce:

“Ba mu da hannu kai tsaye a dukkan batutuwan da aka gabatar. Bayanan kudi da ake bukata daga hukumomin da abin ya shafa, musamman NNPCL da NUPRC, ba su samu ba.”

Wane mataki ma'aikatar ta dauka?

Omachi ya bayyana cewa ma’aikatar ta dauki wani kamfanin binciken kudi na waje domin gudanar da cikakken bincike kan mu’amalolin kudaden, cewar rahoton Punch.

Shugaba Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a fadar Aso Rock Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Ya ce manufar binciken ita ce taimakawa wajen daidaita bayanan da kuma gano hakikanin yadda aka gudanar da mu’amalolin kudaden da NEITI ta yi tambaya a kansu.

Kara karanta wannan

Magana ta girma: An bukaci hukumomin tsaro su cafke Sheikh Jingir

Ya kuma bukaci Majalisar Dattawa ta yi amfani da ikon da doka ta ba ta wajen tilasta shugabannin NNPCL da NUPRC su bayyana a gaban kwamitin tare da Ma’aikatar Kudi.

Tinubu zai fadi yadda aka kashe kudin tallafi

An ji cewa Shugaba Bola Tinubu ya ce gwamnatin tarayya za ta bayyana yadda ta yi amfani da kudaden da aka samu bayan cire tallafin man fetur.

Tinubu ya ce cire tallafin ya bai wa gwamnati damar karkatar da kudade zuwa wasu bangarorin tattalin arziki da ayyukan more rayuwa da ake gani

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262