Biki Bidiri: Fitaccen Jarumin Kannywood Adam A. Zango Ya Yi Sabon Aure a Kasar Waje

Biki Bidiri: Fitaccen Jarumin Kannywood Adam A. Zango Ya Yi Sabon Aure a Kasar Waje

  • Jarumin masana'antar Kannywood, Adam. A Zango ya yi sabon aure, inda rahotanni suka ce an daura auren ne da wata yar Jamhuriyar Nijar
  • Zango ya ce ya yi auren ne da fatan samun dacewa da wannan lokaci na watan Rabi’ul Awwal, inda ya nemi masoyansa su ci gaba da yi masa addu’a
  • Wannana dai na zuwa ne makonni kadan bayan auren Adam A. Zango da Maimuna Pretty ya mutu, lamarin da ya ja hanjalin jama'a

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kaduna, Nigeria - Fitaccen jarumin masana'antar shirya fina-finai ta Kannywood, Adam. A. Zango ya yi sabon aure kwanaki kadan bayan rabuwa da tsohuwar matarsa.

Wannna aure na jarumin na zuwa ne bayan aurensa da jarumar Kannywood, Maimuna Musa, wacce aka fi sani da Maimuna Pretty ya mutu.

Adam A. Zango.
Fitaccen jarumin Kannywood, Adam A. Zango d sabuwar amaryarsa Hoto: Adam. A. Zango
Source: Facebook

Adam A. Zango ya tabbatar da cewa ya yi sabon aure a wani gajeren sako mai dauke da hotonsa da na amaryarsa da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

Trump ya hadu da fushin Iran da ya tsokano Tehran kan 'kwace' Hormuz

Adam Zango ya yi sabon aure a Nijar

Rahotanni sun nuna cewa fitaccen jarumin na Kannywood, Adam A. Zango, ya sake yin aure ne a ƙasar Nijar.

Bayan kammala bikin, jarumin ya bayyana godiyarsa ga Allah, tare da aika saƙo ga masu nuna baƙin ciki kan sabon aurensa da cewa: “ku ci kanku.”

Rahoton da Aminiya ta wallafa ya nuna cewa Adam A. Zango, ya sake aure a ranar Juma’a, 14 ga Agusta 2026, da wata ’yar ƙasar Jamhuriyar Nijar.

Zango ya ce ya yi auren ne da fatan samun dacewa da wannan lokaci na watan Rabi’ul Awwal, inda ya nemi masoyansa su ci gaba da yi masa addu’a domin samun zaman lafiya da ɗorewar auren.

Ya kuma ce bai taɓa yin aure da niyyar rabuwa da matar ba, yana mai cewa rabuwar da ta faru a baya ƙaddara ce.

Kara karanta wannan

Shugaba Paul Biya na Kamaru ya yi batan dabo, wata 2 ba a gan shi ba

Martanin jama'a kan auren Zango

Tuni dai magoya baya da sauran al'umma musamman a Arewacin Najeriya suka fara tofa albarkacin bakinsu kan wannan sabon aure na Adam A. Zango.

Wasu na tura sakonnin fatan alheri yayin da wasu ke sukar jarumin kan yawan abin da suka kira da auri saki.

Abdulraahman Yusuf Kankia ya ce:

"Wannan yana daya daga cikin dalilan da ya sa kake samun matsala a zamantakewar aurenka. Ka jaraba daina kawo maganar aurenka kafafen sada zumunta da idanun mutane, za ka yadda gidanka zai kasance cikin farin ciki."

Usman Nasir Huzaifa ya ce:

"Allah ya sanya alkhairi."

Uthman Yusuf Bawa ya ce:

Sabuwar amarya kuma yallaɓai, ina fatan kun yi gwajin genotype wannna karon kafin a daura auren."
Adam. A Zango.
Jarumin Kannywood, Adam A. Zango Hoto: Adam. A Zango
Source: Facebook

Dalilin rabuwar Zango da Maimuna Pretty

A wani rahoton, kun ji cewa fitaccen jarumin Kannywood , Adam A. Zango, ya tabbatar da cewa auren sa da Maimuna Musa, wadda aka fi sani da Maimuna Pretty ya mutu.

Kara karanta wannan

Tsautsayi ya faɗa kan matar aure da 'ya'yanta 2 cikin dare, Allah ya musu rasuwa a Kaduna

Adam Zango ya yi bayani cewa auren ya mutu ne kasancewar dukkansu suna da genotype AS, kuma daya ne daga cikin dalilan da suka kawo ƙarshen auren.

Jarumin ya ce ya ga ya dace ya bayyana wannan bayani domin jama'a su san gaskiyar abin da ya faru, maimakon ci gaba da yaɗa jita-jita ko bayanan da ba su da tushe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262