Kotu Ta Dauki Matakin Farko kan Wadanda Ake Zargi da Yunkurin Yi Wa Tinubu Juyin Mulki
- Babbar kotun tarayya ta umarci hukumar DSS ta tsare mutane shida da aka gurfanar gabanta bisa zargin kitsa juyin mulki a Najeriya
- Wannan mataki na zuwa ne bayan gwamnatin tarayya ta gurfanar da wadanda ake zargin a yau Laraba, 22 ga watan Afrilu, 2026
- Bayan sauraron kowane bangare da bukatar da gwamnati ta shigar, kotu ta dage zaman shari'ar zuwa ranar 27 ga watan Afrilu, 2026
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta ba da umarnin tsare mutane shida a hannun Hukumar Tsaro ta DSS bayan an gurfanar da su kan zargin hannu a kitsa juyin mulki.
Gwamnatin tarayya ta gurfanar da wadanda ake zargin ne kan tuhume-tuhume guda 13 da suka shafi zargin ta’addanci da cin amanar kasa.

Kara karanta wannan
Kurunkus: An gurfanar da mutane 6 da ake zargi da yunkurin yi wa Tinubu juyin mulki a Najeriya

Source: Getty Images
Jaridar Punch ta ruwaito cewa an fara zaman wannan shari’ar ne a ranar Laraba, 22 ga watan Afrilu, 2026, inda aka fara zaman da misalin karfe 1:46 na rana.
An samu tsaiko a zaman kotu
A yayin zaman, Antoni Janar na Tarayya kuma Ministan Shari'a, Lateef Fagbemi (SAN), ya shaida wa kotu cewa an shirya takardar tuhuma tare da neman izinin karanta wa wadanda ake zargi.
Sai dai an samu tsaiko na 'dan lokaci bayan wanda ake tuhuma na uku ya sanar da kotu cewa lauyansa ba zai samu halarta ba saboda yana fama da rashin lafiya.
Haka kuma, lauyan wanda ake tuhuma na shida ya bayyana cewa wanda yake karewa na fahimtar Larabci da Hausa ne kawai, lamarin da ya sa kotu ta dakatar da zaman domin nemo mai fassara.
Da aka koma zaman da misalin karfe 2:18 na rana, an karanta wa dukkanin wadanda ake zargi tuhume-tuhumen, inda suka musanta su baki daya tare da cewa ba su aikata ba.
Gwamnatin Tarayya ta mika bukata
Bayan gurfanar da su, bangaren gwamnatin tarayya ya bukaci kotu da ta bayar da umarnin tsare su a hannun hukumar DSS tare da gaggauta fara shari’ar.
Yawancin lauyoyi masu kare wadanda ake zargi ba su yi adawa da wannan bukata ba, sai dai lauyan wanda ake tuhuma na farko ya nuna niyyar neman beli.

Source: Twitter
Matakin farko da kotu ta dauka
A hukuncin da ya yanke, alkalin kotun ya amince da bukatar gaggauta shari’ar, tare da bayar da umarnin a tsare wadanda ake zargin a hannun DSS amma a ba su damar ganawa da lauyoyinsu.
Kotun ta dage sauraron shari’ar zuwa ranar 27 ga Afrilu, 2026 domin fara cikakken zama kan shari’ar, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.
Laifuffukan da ake zarginsu da aikatawa
A baya, kun ji cewa Gwamnatin tarayya ta fara shigar da duka tuhume-tuhumen da take wa wadanda ake zargi da kitsa juyin mulki tun kafin gurfanar da su a gaban babbar kotun tarayya.

Kara karanta wannan
Yadda sojoji da tsohon minista suka raba miliyoyin Naira don kifar da gwamnatin Tinubu
Tuhume-tuhumen sun hada da laifuffukan cin amanar kasa, ta’addanci, boye bayanan tsaro da kuma alaka da kudin da suka shafi daukar nauyin ta’addanci.
Ofishin Antoni Janar na tarayya ya ne ya shigar da tuhume-tuhumen tare da sanya hannun Daraktan gurfanarwar gwamnatin tarayya, Rotimi Oyedepo.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
