Magana Ta Fito: An Ji Yadda Ta Kaya tsakanin Wakilan Najeriya da na Amurka a Washington DC
- Tawagar hadin gwiwa tsakanin Amurka da Najeriya ta yi zaman tattaunawa na biyu a jere a birnin Washington DC jiya Alhamis
- Kasashen biyu sun duba yadda za a karfafa hukumomin shari’a da tsaro domin hukunta masu aikata ayyukan tashin hankali
- Sun kuma tattauna kan sake tsugunar da ‘yan gudun hijira, yaki da masu daukar nauyin ta’addanci da kare kiristocin Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yaubda kullum
United States - Gwamnatin Amurka ta ce zagaye na biyu na tattaunawarta da Najeriya karkashin kwamitin hadin gwiwa ya maida hankali kan muhimman batutuwan tsaro.
Amurka ta ce taron ya mayar da hankali kan kare rayukan Kiristoci da ke yankin Arewa ta Tsakiya, karfafa hukumomin shari’a da tsaro domin hukunta masu aikata laifi da kuma fadada hadin gwiwar sojojin kasashen biyu.

Source: Twitter
Rahoton The Cable ya ce taron ya fara ne ranar Laraba kuma ya ci gaba zuwa ranar Alhamis, 13 ga watan Agustan 226 a birnin Washington na Amurka.

Kara karanta wannan
'Yan Najeriya na cikin alheri, an turo musu tallafin fiye da Naira biliyan 40 daga ƙasar waje
Mai ba Shugaban Najeriya shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, ya jagoranci tawagar Najeriya, yayin da Mataimakiyar Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Allison Hoker, ta jagoranci tawagar Amurka.
An duba batun ‘yan gudun hijira
A cikin wata sanarwa da Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta fitar, ta ce Allison da tawagar Najeriya sun duba ci gaban da aka samu wajen mayar da ‘yan gudun hijira zuwa zuwa garuruwansu na asali.
Sun kuma tattauna gurfanar da wadanda ake zargi da aikata ta’addanci a gaban kotu da kuma yaki da hanyoyin samun kudin gudanar da ayyukan ta’addanci.
Sanarwar ta ce wakilan kasashen biyu sun kuma gano wasu kalubale da har yanzu suke akwai, ciki har da rahotannin mutuwar fararen hula da kuma gibin bayyana yadda ake kashe kudaden agaji.
Amurka ta yaba da wasu matakai
A cewar sanarwar, Amurka ta lura da matakan da Najeriya ta dauka kawo yanzu, ciki har da gurfanar da daruruwan mutanen da ake zargi da kasancewa mambobin Boko Haram da ISIS-WA.

Kara karanta wannan
Amurka ta daina boye boye, ta bayyana manufofi 2 da take son cimmawa a yaki da Iran
Ta kuma ambaci fadada karfin hukumomin shari’a da kuma daukar karin jami’an ’yan sanda 50,000 tare da ba su horo.
Sanarwar ta ce:
“Bangarorin biyu sun amince cewa akwai sauran ayyuka da yawa da ya kamata a yi, musamman wajen tallafa wa ‘yan gudun hijira.”
Sun tattauna musayar bayanan sirri
Kasashen biyu sun kuma tattauna ci gaba da hadin gwiwa wajen dakile hanyoyin samar da kudin ta’addanci da musayar bayanai domin taimakawa wajen tabbatar da hukunta masu laifi.
Sun kuma duba yadda za a kara karfin hukumomin tabbatar da doka ta hanyar ofisoshin Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka da ke kula da yaki da miyagun kwayoyi da tabbatar da doka (INL) da kuma yaki da ta’addanci (CT).

Source: Twitter
Amurka ta sake tabbatar da hadin gwiwa
Amurka ta ce Allison ta kuma gana da Ribadu daban domin kara inganta muhimman batutuwan da suka shafi kasashen biyu.
A yayin ganawar, ta sake tabbatar da kudurin Amurka na yin aiki tare da Najeriya wajen kare al’ummomin Kirista da kuma zurfafa hadin gwiwar tsaro tsakanin kasashen biyu.
Rahoton Amurka bai yiwa Najeriya dadi ba
A baya, kun ji cewa fadar shugaban kasa ta yi fatali da rahoton Amurka, wanda ya nuna damuwa kan yadda ake tafiyar da harkokin kudin Najeriya.
Ta ce sabon rahoton Amurka kan bayyana harkokin kudin Najeriya bai yi cikakken nazari da tantance sauye-sauyen da gwamnatin kasar ke aiwatarwa ba.
Asali: Legit.ng
