Bayan Zuwan Amurka, Kasar Musulunci za Ta Kafa Cibiyar Soji a Najeriya

Bayan Zuwan Amurka, Kasar Musulunci za Ta Kafa Cibiyar Soji a Najeriya

  • Rahotanni sun nuna cewa gwamnatin Turkiyya za ta kafa cibiyar horas da sojoji a Najeriya domin tallafawa kasar ta magance matsalolin tsaro
  • Gwamnatin Najeriya ta yi na'am da kudirin tare da bayyana wasu matakai da za a dauka domin tabbatar da nasarar shirin wajen yaki da ta'addanci
  • Hakan na zuwa ne bayan wata ziyara da shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya kai kasar Turkiyya a watan Janairun shekarar 2026 da muke ciki

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Najeriya da Türkiyya sun amince su kafa babbar cibiyar horas da sojoji a Najeriya a matsayin wani bangare na hadin gwiwar tsaro da ke da nufin karfafa tsarin tsaron kasar.

An cimma yarjejeniyar ne a yayin tattaunawar bangarorin biyu tsakanin Ministan Tsaro na Najeriya, Christopher Musa, da takwaransa na Turkiyya, Yasar Guler, a gefen taron Antalya Diplomacy Forum na 2026.

Kara karanta wannan

Abubuwan da 'yan Najeriya za su gani idan jam'iyyar ADC ta kifar da Tinubu a zaben 2027

Christopher Musa da jami'in Turkiyya
Ministan tsaron Najeriya, Christopher Musa da jami'in Turkiyya. Hoto: Ministry of Defence Nigeria
Source: Facebook

A cewar wata sanarwa da jami’ar yada labarai ta ma’aikatar tsaro, Queeneth Iheoma-Hart, ta fitar a Facebook, cibiyar horaswar da ake shirin kafawa za ta taimakawa Najeriya sosai.

Wajen da za a kafa cibiyar sojin

Ma'aikatar tsaro ta ce shirin zai bunkasa kwarewar dakaru, inda tuni Najeriya ta gano wani wuri mai kyau a bakin teku domin gina cibiyar ta dindindin.

Rahoto jaridar Punch ya nuna cewa Queeneth Iheoma-Hart ta ce ana sa ran samar da wani wuri na wucin gadi domin fara ayyukan a halin yanzu.

Aikin sojojin Turkiyya a Najeriya

A karkashin shirin, jami’an rundunar sojin Najeriya za su samu horo na musamman a fannoni kamar ayyukan rundunar musamman, yaki da ta’addanci da tattara bayanan sirri.

Haka zalika shirin zai mayar da hankali kan yaki da jirage marasa matuka, da kuma yaki da abubuwan fashewa da dai sauransu.

Sanarwar ta ce:

“Ministan Tsaro, Janar Christopher Gwabin Musa (mai ritaya), ya jagoranci wata babbar tawaga ta Najeriya zuwa tattaunawa mai amfani da Ministan Tsaro na Türkiyya.

Kara karanta wannan

Tattaunawar sulhu tsakanin Amurka da Iran ta dawo farko, an ji halin da ake ciki

“Bangarorin biyu sun amince su kafa babbar cibiyar horas da sojoji a Najeriya; Najeriya za ta samar da wurin horaswa na wucin gadi, kuma ta gano wani wuri a bakin teku domin gina cibiyar ta dindindin.”

Yarjejeniyar ta kuma kunshi karfafa kula da iyakoki, musayar bayanan sirri da kuma hadin kai wajen magance kungiyoyin da ba na gwamnati ba da sauransu.

Bayanin ministan tsaron Najeriya

Da yake magana kan wannan ci gaba, Musa ya bayyana sakamakon taron a matsayin “babban ci gaba” a dangantakar tsaro tsakanin Najeriya da Türkiyya.

Ya ce:

“Mun kuduri aniyar samar da sakamako mai ma’ana wanda zai karfafa tsaron kasa tare da inganta ajandar Renewed Hope,”

A ‘yan shekarun nan, Najeriya ta fadada hadin gwiwar tsaro domin kara karfin yaki da sababbin barazanar tsaro, ciki har da ta’addanci da fashi da makami.

Shugaban Najeriya da na Turkiyya
Recep Tayyip Erdoğan da Bola Tinubu a Turkiyya a farko 2026. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Yarjejeniya da Turkiyya na zuwa ne a daidai lokacin da sojojin Amurka ke cikin kasar suna bayar da tallafi a fannin horaswa, tattara bayanan sirri da kuma kayan aiki.

An yaye tubabbun 'yan ta'adda 744

A wani labarin, mun kawo muku cewa gwamnatin Najeriya ta kammala shirin yaye tubabbin 'yan ta'adda a jihar Gombe a makon da ya wuce.

Kara karanta wannan

An fara matsa wa Tinubu daga Amurka, ana son ya kori Matawalle daga kujerar minista

Rahotanni sun nuna cewa 'yan ta'adda akalla 744 ne da suka fito daga jihohin Borno, Yobe, Kano, Filato da sauransu aka yi wa horo a karkashin shirin.

Rundunar tsaron Najeriya ta sanar da cewa hakan na cikin ayyukan da ta ke wajen yaki da ta'addanci ba tare da amfani da karfin soji ba a kasar nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng