Bayanin da Sheikh Gumi Ya Yi kan Amfanin da Kudin Gwamnati don Shirya Auren Gata
- Sanannen malamin addinin Musulunci, Dr Ahmad Gumi ya yi magana kan amfani da kudin gwamnati wajen gudanar da auren gata da wasu gwamnatoci ke gudanarwa a jihohinsu
- Malamin addinin ya kare shirin auren gata na Kano bayan wasu sun soki yadda ake amfani da kudaden gwamnati wajen gudanar da shi
- Sheikh Gumi ya ce taimaka wa matasan da ke tsananin bukatar aure na daga cikin nauyin da gwamnati ke da shi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kaduna - Sanannen malamin addinin Musulunci da ke jihar Kaduna, Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi, ya kare amfani da kudaden gwamnati wajen gudanar da auren gata.
Sheikh Gumi ya bayyana cewa hakan wani bangare ne na halastaccen kuma nagartaccen shugabanci a jihar da ke tafiyar da harkokinta bisa Shari’a.

Source: Facebook
Sheikh Ahmad Gumi ya bayyana hakan ne a shafinsa na Facebook a ranar Alhamis, 13 ga watan Agustan 2026.
Malamin addinin ya bayyana hakan ne yayin da yake mayar da martani kan sukar da ake yi wa auren gata da gwamnatin jihar Kano ta gudanar.
Me Sheikh Gumi ya ce kan auren gata?
Sheikh Gumi ya ce irin wannan shiri ya dace a jihar da dokokin Musulunci da na gwamnati suka haramta karuwanci, zina da lalata.
“A jihar da ke tafiyar da harkokinta bisa Shari’a, inda dokokin Allah da na gwamnati suka haramta karuwanci, zina, lalata da fasikanci, amfani da kudin gwamnati wajen tallafa wa auren matan da suka fi yawan mazan da suka cancanci aurensu, ko kuma duk wani matashi da ke tsananin bukatar aure, wani bangare ne na halastaccen kuma nagartaccen shugabanci,” in ji shi.
Gumi ya bayyana nauyin da ke kan gwamnati
Malamin addinin Musuluncin ya ce taimaka wa matasan da ke tsananin bukatar aure ya kamata a dauke shi a matsayin wani bangare na nauyin da gwamnati ke da shi, musamman a al’ummar da ake tafiyar da harkokinta bisa ka’idojin Shari’a.
Kalaman Gumi sun zo ne a daidai lokacin da ake ta sukar shirin auren gata na jihar Kano, inda wasu ke tambayar dalilin amfani da kudaden gwamnati wajen gudanar da shirin.
Sai dai Sheikh Gumi ya dage cewa ya kamata a fahimci manufar shirin ne bisa la’akari da dokoki da kuma yanayin zamantakewar al’ummar jihar da ke tafiyar da harkokinta bisa Shari’a.
Ya ce idan wasu halaye sun haramta a karkashin dokokin Allah da na gwamnati, to sa hannun gwamnati wajen tallafa wa auren da ya halasta za a iya kallonsa a matsayin matakin da ya dace da kyakkyawan shugabanci.

Source: Facebook
Auren gata: Gwamnatin Kano ta mika bukata ga malamai
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf, ta ba da umarni ga limaman masallatan Juma’a kan auren gata.
Gwamnatin ta umarci malaman su yi amfani da wa’azinsu wajen karyata bayanan ƙarya game da shirin aurar da jama’a.
Ta ce shugabannin addini, musamman limamai da malaman Musulunci, suna da muhimmiyar rawa wajen tabbatar da zaman lafiya da dakile yaɗuwar bayanan ƙarya.
Asali: Legit.ng

