Sojojin Sama Sun Toshe Kofofin Tsira ga 'Yan Ta'adda yayin da Aka Hallaka Tsageru Masu Yawa
- 'Yan ta'adda sun gane shayi ruwa ne bayan hare-haren da dakarun rundunar sojojin sama suka kai musu a jihar Borno
- Hare-haren wadanda aka kai cikin kwarewa sun yi sanadiyyar hallaka 'yan ta'adda da dama wadanda suke addabar bayin Allah
- Rundunar sojojin saman ta ba da tabbacin cewa za ta ci gaba da kare dukkan 'yan kasa daga barazanar miyagu
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Borno - Rundunar sojojin saman Najeriya ta ce bangaren ayyukan sama na Operation Hadin Kai ya gudanar da wasu hare-haren sama a jihar Borno.
Rundunar sojojin saman ta ce an gudanar da hare-haren cikin nuna kwarewa a yankin Yuwe da ke cikin dajin Sambisa, inda aka kashe ‘yan ta’adda da dama a ranar Litinin, 20 ga watan Afrilun 2026.

Source: Getty Images
Jaridar The Punch ta ce daraktan hulda da jama'a da yada labarai na sojojin sama, Air Commodore Ehimen Ejodame, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, 21 ga watan Afrilun 2026 a Abuja.

Kara karanta wannan
Hankula sun tashi da 'yan bindiga suka kai sababbin hare-hare a Plateau aka rasa rayuka
Sojoji na matsa wa 'yan ta'adda lamba
Ejodame ya ce rundunar sojojin ta ci gaba da matsa lamba ga ‘yan ta’adda a yankin Arewa maso Gabas.
Ya ce an gudanar da aikin ne biyo bayan sahihan bayanan sirri da aka tabbatar ta hanyar bincike da sanya ido, wadanda suka tabbatar da kasancewar wasu kwararrun ‘yan ta’adda a cikin wasu katangar gine-gine da rumbun ajiya.
A cewarsa, jiragen yaki na NAF sun kai hari kan wuraren da makamai cikin kwarewa, inda suka ruguza gine-ginen, tare da kashe ‘yan ta’adda da dama.
Sannan sojojin lalata muhimman kayayyakin more rayuwa na ta’addanci, kamar yadda tantance barnar da aka yi bayan hare-haren ta tabbatar, rahoton ya zo a jaridar TheCable.
"Ci gaba da gudanar da kai hare-hare ta sama yana ci gaba da raunana cibiyoyin ‘yan ta’adda, lamarin da ke barin su a bayyane kuma cikin hargitsi, yayin da matsin lambar da ke karuwa ke tura su ga daukar matakan yanke kauna da na ramuwar gayya.”
- Ehimen Ejodame
Hafsan sojojin sama ya sha alwashi
Ya nakalto babban hafsan sojojin Sama, Air Marshal Sunday Aneke, yana mai sake jaddada kudurin NAF na ci gaba da gudanar da hare-hare ba tare da kakkautawa ba, bisa jagorancin bayanan sirri, har sai an kawar da ‘yan ta’adda baki daya.

Source: Original
“Muna ci gaba da jajircewa wajen kare ma’aikatanmu, tsaron kasarmu, da kuma kare rayukan dukkan ‘yan kasa."
“Rundunar NAF za ta ci gaba da tsananta ayyukan kwarewa a dukkan fadin yankin, tare da ci gaba da yin amfani da karfin sojoji yayin da take bin ka’idojin aiki da kuma takaita cutar da farar hula."
- Air Marshal Sunday Aneke
'Yan bindiga sun kashe sojoji
A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan bindiga sun kai wani harin ta'addanci a sansanin sojoji da ke jihar Kwara.
Harin wanda aka kai da misalin ƙarfe 3:00 na dare, ya yi sanadiyyar mutuwar sojoji uku da kuma ƴan banga biyu.
Ƴan bindigar, sun farmaki sansanin ne wanda ke ɗauke da sojoji, masu gadin gandun daji, da kuma ƴan banga.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
