Komai na Son Bayani: Tinubu Ya Faɗi Hanyar da Talakawa ke Morar Cire Tallafi
- Shugaba Bola Tinubu ya ce kudaden da aka samu bayan cire tallafin man fetur suna biyan albashi tare da tallafa manyan ayyukan hanya
- Tinubu ya bayyana cewa gwamnati za ta fara wallafa yadda ake amfani da kudaden tallafin da aka cire, domin nuna amfaninsu ga talakawa
- NUPENG ta roki Tinubu ya dakatar da aikin wucin-gadi a masana'antar man fetur, tare da farfado da matatun mai da ma'ajiyar bututun mai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana amfanin kudin cire tallafi ga ƴan ƙasar duk da wahalar da ake ciki.
Tinubu ya ce kudaden da gwamnati ke ajiyewa bayan cire tallafin man fetur suna taimakawa wajen biyan albashi da gudanar da manyan ayyuka.

Source: Twitter
Tinubu ya bayyana hakan ne yayin da yake karbar shugabannin kungiyar ma'aikatan man fetur da iskar gas ta Najeriya, NUPENG, a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja, cewar Arise TV.
Tinubu ya fadi amfanin cire tallafin mai
Ya ce cire tallafin man fetur, wanda ya sanar a ranar da aka rantsar da shi a matsayin shugaban kasa ranar 29 ga Mayun 2023, yana amfanar talakawa.
Shugaban ya kuma yi alkawarin cewa gwamnati za ta fara wallafa bayanai kan yadda ake amfani da kudaden da aka samu bayan cire tallafin.
Tinubu ya ce biyan albashin ma'aikatan kananan hukumomi, jihohi da gwamnatin tarayya a kan lokaci na daga cikin amfanin cire tallafin man fetur.
Ya ce kudaden suna taimakawa wajen samun damar gudanar da manyan ayyukan tituna, ciki har da hanyar Lagos zuwa Ibadan, Abuja zuwa Kaduna da Abuja zuwa Kano.

Source: Twitter
Manyan hanyoyi da Tinubu ya ba da misali
Tinubu ya kuma ambaci babbar hanyar Sokoto zuwa Badagry da sauran hanyoyin da ake ginawa ko gyarawa a fadin Najeriya, yana mai cewa ayyukan za su taimaka wa tattalin arziki da tsaron jama'a.

Kara karanta wannan
Tinubu zai wallafa yadda aka kashe kudin da aka samu daga cire tallafin man fetur
Ya ce matatun man Najeriya hudu da suka dade ba sa aiki za su koma aiki, amma ya jaddada cewa dole ne su kasance masu samar da riba.
A cewar Tinubu, hayaki ko wutar da ake gani daga matatar mai kadai ba ya tabbatar da cewa tana aiki yadda ya kamata, matukar ba ta samar da riba.
Ya ce ya karbi dukkan kadarori da basussukan gwamnatocin baya, kuma a matsayinsa na shugaban kasa, alhakinsa ne ya gyara matsalolin tare da dawo da darajar kadarorin.
Shugaban ya kuma bukaci shugabannin NUPENG su tabbatar da cewa masu motocin dakon kaya suna isar da amfanin amfani da CNG ga fasinjoji.
Ya ce duk wata fa'ida da aka samu daga amfani da iskar gas mai matsewa, CNG, bai kamata ta tsaya a aljihun masu motocin dakon kaya kadai ba.
Mawaki ya wanke Tinubu kan matsalolin Najeriya
An ji cewa mawaki a Najeriya, Femi Kuti ya ce Shugaba Bola Tinubu ba shi ne babbar matsalar Najeriya ba kamar yadda wasu suke tunani a kasar.
Kuti ya ce tsarin shari’ar Najeriya ya kamata ya kasance mai ƙarfi, har ya hana mutanen da ake zargi da manyan laifuka tsayawa takarar shugabanci.
Femi Kuti ya ce cin hanci ya yi katutu a Najeriya, yana shafar cibiyoyi da dama tare da rage wa matasa kwarin gwiwar makomar ƙasar.
Asali: Legit.ng
