Cikin Jimami an Gudanar da Jana'izar Janar da Sojojin da Boko Haram Ta Kashe, an Saki Hotuna

Cikin Jimami an Gudanar da Jana'izar Janar da Sojojin da Boko Haram Ta Kashe, an Saki Hotuna

  • Rundunar sojojin Najeriya ta rasa wasu daga cikin dakarunta a hannun mayakan kungiyar Boko Haram
  • An gudanar da jana'izarsu cikin jimami da bakin ciki a birnin Maidguri na jihar Borno a ranar Laraba, 15 ga watan Afirilun 2026
  • Ministan tsaro, Christopher Musa da Gwamna Babagana Umara Zulum na daga cikin manyan mutanen da suka halarci jana'izar

​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Borno - Rundunar sojojin Najeriya ta gudanar da jana'izar dakarunta da suka rasu a hannun 'yan ta'addan Boko Haram.

An binne Birgediya Janar Oseni Braimah, Kyaftin Ismail, da sauran sojojin da aka kashe a wani hari da ’yan ta'adda suka kai kwanan nan a jihar Borno.

An yi jana'izar sojojin Najeriya a Borno
Sojoji na tura gawa lokacin jana'iza a Borno Hoto: HQ Nigerian Army
Source: Facebook

Hakan na kunshe ne a cikin sanarwa da rundunar sojojin Najeriya ta sanya a shafinta na Facebook a ranar Laraba, 15 ga watan Afirilun 2026.

Kara karanta wannan

Sojojin Najeriya sun bi 'yan ta'adda cikin daji sun musu barin wuta

A ina aka gudanar da jana'izar?

An gudanar da jana'izar jami'an da sauran sojojin ne a makabartar barikin Maimalari da ke Maiduguri tare da ba su dukkan girmamawa na aikin soja.

Jaruman sojojin sun rasa rayukansu ne a ranar 9 ga Afrilu, lokacin da ake zargin mayakan Boko Haram da na ISWAP sun ƙaddamar da hare-haren haɗin gwiwa kan sansanonin soji a Benisheikh, ƙaramar hukumar Kaga da ke kan hanyar Maiduguri zuwa Damaturu.

A cikin sanarwar, rundunar ta bayyana bikin binne su a matsayin wanda ya cika da baƙin ciki da ban tausayi.

Wani bangare na sanarwar na cewa:

“A cikin wani biki mai cike da alhini da ban tausayi, ƙasar nan a yau Laraba, 15 ga Afrilu, 2026, ta binne marigayi Birgediya Janar Omo Braimah, Kyaftin Ismail, da sauran jaruman sojoji waɗanda suka sadaukar da rayukansu wajen gudanar da aikinsu."
“Jana’izar, wadda aka gudanar a makabartar barikin Maimalari da ke Maiduguri, jihar Borno, ta kasance cike da tsananin baƙin ciki, darajawa, da nuna jimami."

Kara karanta wannan

An yi rashi: 'Yan Boko Haram sun sake hallaka babban kwamanda da wasu sojoji a Najeriya

An girmama sojojin da suka rasu

Ta ƙara da cewa an ba wa sojojin dukkan girmamawar da soja ke samu a matsayin amincewa da hidima da sadaukarwar da suka yi wa ƙasa.

Daga cikin waɗanda suka halarci jana’izar har da Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, Ministan tsaro Christopher Musa, da ma sauran manyan jami’an sojoji.

An yi jana'izar sojoji a Borno
Sojojin Najeriya a wajen jana'izar jami'an da aka kashe Hoto: HQ Nigerian Army
Source: Facebook

Sun bayyana mamatan a matsayin masu kishin ƙasa waɗanda suka rasa rayukansu domin kare ƙasar nan.

An gudanar da addu’o’i a gare su, sannan aka karanta takaitaccen tarihin ayyukansu a gaban iyalansu.

Rundunar sojojin ta nuna cewa alhinin da iyalansu ke ciki ya nuna girman asarar rayukan da ake yi a ƙoƙarin tabbatar da tsaron ƙasa, ko da yake jarumtakarsu za ta ci gaba da kasancewa abin alfahari ga ƙasar baki ɗaya.

Shettima ya je Borno kan kisan sojoji

A wani labarin kuma, kun ji cewa mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya kai ziyarar jaje zuwa jihar Borno.

Kara karanta wannan

An kama ɗan shekara 15 da ake zargi da hannu a kashe Janar a harin Borno

Kashim Shettima ya je jaje ne kan harin da aka kai wa jami’an sojoji kwanan nan a Benisheikh, wanda ya yi sanadin mutuwar jami’ai da sojoji da dama, ciki har da Birgediya Janar Oseni Braimah.

Ziyarar ta’aziyya ta gudana ne bayan wani mummunan hari na tsakar dare da aka kai wa sansanin soji a Benisheikh, jihar Borno.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng