Mataimakin Gwamna Ya Jawo Rudani, Ya Ce Yan Bindiga Sun Kai Hare Hare Kananan Hukumomi 26
- Kananan hukumomi 26 cikin 34 na jihar Katsina na fuskantar hare-hare yan bindiga kafin Gwanna Dikko Radda ya karbi mulki a 2023
- Mataimakin Gwamnan Katsina, Faruk Lawal Jobe, ne ya bayyana hakan, yana mai kira ga hadin gwiwa domin dawo da zaman lafiya
- Jobe ya ce lamarin tsaro ya inganta sosai tun bayan da gwamnatin Dikko Radda ta karbi ragamar mulki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Katsina, Nigeria - Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina, Faruk Lawal Jobe, ya ce kananan hukumomi 26 daga cikin 34 na jihar na fuskantar hare-hare a lokacin da gwamnatin Gwamna Dikko Radda ta hau mulki a 2023.
Jobe ya bayyana hakan ne ranar Alhamis yayin da yake wakiltar gwamnan a taron kwata ta biyu na shekarar 2026 na shiyyar Arewa maso Yamma da aka gudanar a Katsina.

Kara karanta wannan
Magana ta fito: An ji yadda ta kaya tsakanin wakilan Najeriya da na Amurka a Washington DC

Source: Facebook
Premium Times ta ce taron, mai taken “hada kai don yaki da ta'addanci”, ya hada daraktocin hukumar DSS da sauran jami’an tsaro daga jihohin Arewa maso Yamma.
Tsaro ya inganta a mulkin Dikko Radda
Jobe ya ce kananan hukumomi 26 na fuskantar hare-hare akai-akai a lokacin da gwamnatin Radda ta karbi mulki, amma ya ce tun daga lokacin an samu gagarumin sauyi a harkokin tsaro.
A cewarsa, kashe-kashe, garkuwa da mutane domin neman kudin fansa da sauran laifuffuka sun yi kamari a lokacin, amma matakan da suka hada da amfani da karfin soji da masalaha sun taimaka wajen inganta lamarin.
Ya ce:
“Lokacin da muka hau mulki, muna da kusan kananan hukumomi 26 da ake ci gaba da kai wa hare-hare.”
Jobe ya ja hankali masu ruwa da tsaki
Mataimakin gwamnan ya kuma bukaci masu ruwa da tsaki su yi amfani da dabarun tattara bayanai wajen taimakawa yakin da ake yi da ta’addanci.
Ya kuma bukaci kafafen yada labarai su kara taka-tsantsan wajen rahoton abubuwan da suka shafi tsaro.
Ya yi tsokaci ne kan karuwar aikin jaridancin da ’yan kasa ke yi ta kafafen sada zumunta, yana gargadin cewa yada bayanai ba tare da la’akari da illolinsu ba na iya zama matsala.
An samu sabani kan alkaluman
Alkaluman kananan hukumomi 26 da Jobe ya ambata sun samar da wani sabon ma’auni da za a iya amfani da shi wajen tantance ikirarin gwamnatin jihar na cewa tsaro ya inganta.
Sai dai jami’an Katsina sun yi amfani da kalmomi daban-daban wajen bayyana wuraren da matsalar tsaro ta fi kamari, cewar rahoton Guardian.

Source: Facebook
Wata sanarwar gwamnatin Katsina da aka wallafa a watan Janairu ta ce kafin babban zaben 2023, kananan hukumomi 19 sun shiga jerin wuraren da ake fama da matsalar ’yan bindiga da garkuwa da mutane.
Bambancin alkaluman ba lallai ne ya nuna sabani kai tsaye ba, domin Jobe ya yi magana ne kan wuraren da ake “ci gaba da kai wa hare-hare”, yayin da sanarwar gwamnatin ta yi amfani da kalmar “wuraren da matsalar ta fi ƙamari.”
Sojoji sun tashi tsaye a Katsina
A wani labarin, kun ji cewa dakarun Sojoji Najeriya sun kara zafafa ayyukan yaki da ‘yan ta’adda da kungiyoyi masu dauke da makamai a Katsina da Zamfara.
Dakarun sun kai hare-hare ta sama da kasa kan yan bindiga a wadannan jihohi a karkashin Operation CLEAN SWEEP IV, wani sabon mataki na Operation Fansan Yamma.
Asali: Legit.ng

