'Yan Bindiga Sun Bude Wuta kan Sojojin Najeriya, An Yi Asarar Rayuka a Borno
- Wasu da ake zargi mayakan Boko Haram ne sun kashe sojoji hudu da mace daya a wani hari da suka kai garin Mussa, jihar Borno
- Dakarun bataliya ta 115 sun nuna bajinta wajen dakile yunkurin maharan na shiga cikin gari domin yin barna, amma an rasa rayukan sojoji
- Mazauna yankin sun shiga fargaba yayin da aka rina musayar wuta na tsawon mintuna 30 kafin sojoji su fatattaki maharan gaba daya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Borno – Mayakan Boko Haram sun kai wani sabon hari a garin Mussa da ke ƙarƙashin ƙaramar hukumar Askira/Uba a jihar Borno.
A yayin wannan mummunan harin, an ruwaito cewa 'yan ta'addar sun kashe sojoji huɗu da wata mata, lamarin da ya sake jefa yankin a tashin hankali.

Source: Twitter
'Yan ta'adda sun kashe sojoji a Borno

Kara karanta wannan
Amurka ta cafke wasu ƴan Najeriya 8 da ke ɗaukar nauyin ta'addanci? Gaskiya ta fito
Wannan hari dai ya afku ne da misalin ƙarfe 12:00 na rana a ranar Laraba, 15 ga Afrilu, 2026, kamar yadda rahoton jaridar Punch ya nuna.
Shugaban ƙaramar hukumar Askira/Uba, Mada Saidu, ya tabbatar da faruwar lamarin a yau Alhamis, 16 ga Afrilu, 2026.
Mada Saidu ya bayyana cewa 'yan ta'addar sun farmaki mazauna yankin ne da tsakar rana, kuma sojoji sun yi ƙoƙarin dakile su, sai dai an rasa rayukan sojoji da na farar hula a yayin gumurzumun.
Rahotanni daga majiyoyin tsaro sun nuna cewa sojojin da suka rasa rayukansu suna karkashin bataliyar hadin gwiwa ta 115 ne da ke yankin.
Bajintar da sojoji suka nuna a Borno
Majiyar ta bayyana cewa mayakan sun yi ƙoƙarin kutsawa cikin garin ne da nufin yin barna mai yawa, amma sojojin sun tsaya tsayin daka wajen kare al'umma.
Duk da cewa maharan ba su da yawa, sun tsara harin ne ta yadda za su ruda jami'an tsaron, kamar yadda rahoton PM News ya nuna.
Sojojin sun yi nasarar fatattakar su, amma abin takaici hudu daga cikin jami'an sun riga mu gidan gaskiya a fagen fama yayin da suke gudanar da aikinsu na kare ƙasa.

Kara karanta wannan
An yi rashi: 'Yan Boko Haram sun sake hallaka babban kwamanda da wasu sojoji a Najeriya
Mazauna garin Mussa sun bayyana cewa sun shafe kusan mintuna 30 suna jin ƙarar harbe-harben bindiga, wanda hakan ya sa mutane da dama tserewa daga gidajensu domin neman tsira.

Source: Original
Sojoji na ci gaba da farmakar sojoji
Wani mazaunin garin ya bayyana cewa da ba don jarumtar da sojojin suka nuna ba, da maharan sun shiga cikin gari sun tafka barna mai yawa.
Wannan hari na zuwa ne a matsayin ci gaba da matsin lambar da mayakan ke yi wa dakarun soji da fararen hula a sassan jihar Borno.
Hukumomin tsaro sun bayyana cewa suna ci gaba da sa ido da kuma ƙarfafa tsaro a yankin Askira/Uba domin gudun sake afkuwar makamancin hakan.
An yi jana'izar sojojin da aka kashe
A wani labari, mun ruwaito cewa, Rundunar sojojin Najeriya ta rasa wasu daga cikin dakarunta a hannun mayakan kungiyar Boko Haram.
An gudanar da jana'izarsu cikin jimami da bakin ciki a birnin Maidguri na jihar Borno a ranar Laraba, 15 ga watan Afirilun 2026.
Ministan tsaro, Christopher Musa da Gwamna Babagana Umara Zulum na daga cikin manyan mutanen da suka halarci jana'izar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng