An Karya Doka: PDP Ta Yi Fatali da N150m da Gwamnati Ta Jibgawa Ƴan Takara a 2027

An Karya Doka: PDP Ta Yi Fatali da N150m da Gwamnati Ta Jibgawa Ƴan Takara a 2027

  • Jam’iyyar PDP a Kogi ta yi watsi da N150m da gwamnatin jihar ta sanya wa ’yan takarar shugaban kasa domin tallan yakin neman zabe
  • Ta ce kudIn da aka sanya wa tallace-tallacen siyasa sun yi yawa, ba su dace ba kuma suna iya hana ’yan takara da jam’iyyun adawa shiga siyasa yadda ya kamata
  • PDP ta bukaci gwamnatin Kogi ta sake duba kudIn tare da tattaunawa da jam’iyyun siyasa da sauran masu ruwa da tsaki domin samar da tsarin da ya dace

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kogi - Jam’iyyar PDP reshen jihar Kogi ta yi watsi da sabbin kudin da gwamnatin jihar ta sanya kan allunan tallan yakin neman zabe da sauran kayayyakin tallata 'yan siyasa.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kebbi ta fadi watannin da za ta tsaya da kafarta babu tallafin tarayya

Gwamnatin ta sanya haraji a kan dukkanin masu neman tallata yan takarar shugaban kasa, sanatoci da sauran masu neman takarar gabanin zaben kananan hukumomi na watan Oktoban 2026 da babban zaben 2027.

PDP ta ce akwai matsala tattare da kudin tallata dan takara a Kogi
Gwamna Ahmed Ododo, alamar jam'iyyar PDP Hoto: Alhaji Ahmed Usman Ododo, PDP
Source: Facebook

Jaridar Punch ta ruwaito cewa jam’iyyar ta bayyana kudin da cewa ya yi tsada da yawa kuma wadanda ba su dace da tsarin dimokuradiyya ba.

Kogi: PDP ta fusata

Jaridar Vanguard ta kawo labarin cewa shugaban PDP na jihar, Mohammed Gambo, ne ya bayyana takaicin yawan kudin a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis 13 ga watan Agusta, 2026 a Lokoja, babban birnin jihar.

Mohammed Gambo ya ce jam’iyyar ta amince cewa gwamnati na da hakkin tsara yadda ake amfani da allunan tallace-tallace a wuraren jama’a.

Sai dai acewarsa, ya kamata irin wannan tsari ya kasance mai sauki, mai saukin biya kuma ya dace da kundin tsarin mulkin kasa.

A cewar rahotanni, gwamnatin Kogi ta sanya N150m ga ’yan takarar shugaban kasa, N50m ga ’yan takarar majalisar dattawa daN30m ga ’yan takarar majalisar wakilai.

Sai kuma N5m ga ’yan takarar majalisar dokokin jiha, N2m ga ’yan takarar shugabancin karamar hukuma, sannan N300,000 ga ’yan takarar kansila domin tallan yakin neman zabe da sauran kayayyakin talla.

Kara karanta wannan

ADC ta ji kamshin hadakar 'yan adawa, ana son tsayar da dan takara 1 ya tunkari Tinubu

Martanin PDP kan farashin talla

A martanin Mohammed Gambo, ya ce kudin N50m da aka sanya wa dan takarar majalisar dattawa kadai ya kai kashi 10 cikin 100 na iyakar kudin da doka ta kayyade dan takarar zai iya kashewa a zabe.

Ya yi nuni da cewa sashe na 92(4) na Dokar Zabe ta 2026 ya kayyade cewa dan takarar majalisar dattawa ba zai kashe sama da N500m ba.

PDP ta ce an karya dokar zabe a Kogi
Shugaban INEC na kasa Amupitan Hoto: INEC Nigeria
Source: Facebook

A cewarsa, bayan biyan N50m na kudin tallan yakin neman zabe, dan takarar zai kuma fuskanci kashe wasu kudade da suka hada da gudanar da gangamin siyasa, kafafen yada labarai, sufuri, ofisoshin yakin neman zabe da sauran harkokin yakin neman zabe.

PDP ta ce kudaden da gwamnati ke karba saboda kula da tallace-tallace ya kamata su kasance tsaka-tsaki kuma su dace da abin da dokar zabe ta tanada.

Gwamnatin Kogi ta yanke kudin tallan siyasa

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnatin Ahmed Ododo ta amince da N150m a matsayin kuɗin yada fastoci da sauran abubuwan talla na yan takarar shugaban kasa a 2027.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC ya ƙaƙaba harajin N150m kan Bola Tinubu da wasu yan takara a zaben 2027

’Yan takarar Sanata za su biya N50m, ’yan majalisar wakilai N30m, yayin da ’yan majalisar jiha za su biya N5m tare da barazanar cewa za ta cire tallan siyasar da aka sanya ba tare da izini ba.

Kwamishinan Yada Labarai da Sadarwa na jihar, Kingsley Fanwo, ne ya bayyana hakan a Lokoja bayan wani taron masu ruwa da tsaki da masu gudanar da harkokin tallace-tallacen siyasa a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng