Tubabbun 'Yan Boko Haram da Sauran 'Yan Ta'adda 744 za Su Dawo cikin Al'umma

Tubabbun 'Yan Boko Haram da Sauran 'Yan Ta'adda 744 za Su Dawo cikin Al'umma

  • Gwamnatin tarayya ta kammala shirin sauya tunani da gyaran halin tsofaffin 'yan ta'adda 744 da suka fito daga jihohi daban-daban da wasu kasashe
  • Mafi yawan tsofaffin 'ya ta'addan sun fito daga jihar Borno da ke fama da matsalar Boko Haram da wasu jihohi kamar Kano, Yobe da sauransu
  • Shugaban gwamnoni Arewa ya yi kira ga tsofaffin 'yan ta'addan da su yi amfani da damar da suka zamu wajen zamowa mutanen kirki a al'umma

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Borno - Gwamnatin Tarayya ta kammala shirin gyara rayuwar mutane 744 da suka hada da tsofaffin ‘yan ta'adda da wadanda suka fada cikin tsattsauran ra’ayi, ciki har da ‘yan kasashen waje takwas.

An ba su horo ne a karkashin shirin kawar da tsattsauran ra’ayi, gyara tunaninsu da mayar da su cikin al’umma (DRR) na Operation Safe Corridor.

Kara karanta wannan

Bayan tafiyar jami'an Amurka, 'yan ta'adda sun tsara kai babban hari Abuja, Neja

'Ya ta'addan da suka tuba a Najeriya
'Yan ta'addan da suka tuba yayin bikin yaye su a Gombe. Hoto: @AIT_Online
Source: Twitter

Daily Trust ta wallafa cewa ‘Yan kasashen waje din sun hada da mutum daya daga Burkina Faso da Kamaru, biyu daga Chadi, da hudu daga Jamhuriyar Nijar, yayin da sauran 736 duk ‘yan Najeriya ne.

Jihohin da mutanen suka fito

An kafa wannan shiri a shekarar 2016 a matsayin wani bangare na dabarar magance tada kayar baya ta hanyoyin da ba na soja kadai ba, bisa fahimtar cewa zaman lafiya mai dorewa ba zai samu ta hanyar karfi kadai ba.

Kididdiga ta nuna cewa jihar Borno ce ke da mafi yawan wadanda suka tuba da mutum 597, sai Yobe da 58, Kano da 15, Bauchi da 12, da Adamawa da 10.

Sauran sun fito ne daga jihohin Abia, Akwa Ibom, Anambra, Ebonyi, Enugu, Katsina, Kebbi, Kogi, Nasarawa, Niger, Plateau da Sokoto. Daga cikin wadanda suka kammala shirin, 733 Musulmi ne, yayin da 11 Kiristoci ne.

Kara karanta wannan

Yadda APC ke fatan samun miliyoyin kuri'u a Kano da Katsina a zaben 2027

Bayanin hafsun tsaron Najeriya

Da yake jawabi a wajen bikin kammala shirin a Gombe, Hafsun tsaro Janar Olufemi Oluyede, ya bayyana shirin a matsayin wani muhimmin tsari da ke da nufin rage tashin hankali da hana yaduwar tsattsauran ra’ayi.

Wanda ya wakilce shi, Kabiru Tanimu, ya jaddada cewa shirin wani yunkuri ne na magance tushen matsalolin tada kayar baya da kuma inganta zaman lafiya.

Bayanin mai kula da shirin

Mai kula da shirin, Birgediya Janar Yusuf Ali, ya ce wadanda suka amfana sun samu cikakken horo da ya hada da tallafin lafiyar kwakwalwa, koyon sana’o’i, gyaran fahimtar addini, ilimin zamantakewa da kuma sauya dabi’u.

Punch ta rahoto ya kara da cewa da dama daga cikin mahalartan sun shiga matsalar ne sakamakon tilastawa da ruɗi, yana mai cewa shirin ya ba su damar sake gina rayuwarsu da kuma komawa cikin al’umma.

Kiran da gwamnan Gombe ya yi

Gwamnan Jihar Gombe, Inuwa Yahaya, wanda hadiminsa kan harkokin tsaro, Yusuf Musa ya wakilta, ya bukaci wadanda suka kammala shirin da su dauki wannan dama a matsayin hayar kawo cigaba.

Kara karanta wannan

Amurka ta cafke wasu ƴan Najeriya 8 da ke ɗaukar nauyin ta'addanci? Gaskiya ta fito

Ya kara da cewa wannan shiri na nuna kudurin Najeriya na hada hanyoyin soja da na zaman lafiya wajen magance matsalar tada kayar baya da kuma samar da zaman lafiya mai dorewa.

Gwamnan Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya
Gwamna Inuwa Yahaya a fadar gwamnatin jihar Gombe. Hoto: Ismaila Uba Misilli
Source: Facebook

An fatattaki 'yan ta'adda a Bauchi

A wani rahoton, kun ji cewa rundunar sojin Najeriya ta kai farmaki kan wasu 'yan ta'adda da suka fake a kauyukan Bauchi da Gombe suna satar mutane.

A wani farmaki da sojoji suka kai ta sama da kasa, sun yi barin wuta kan 'yan ta'addan tare da ceto wasu daga cikin mutanen da suka sace.

Dakarun sun yi nasarar kwato bindigogin da 'yan ta'addan ke kai hari da su tare da wasu muhimman kayayyakin da suke aikin yau da kullum.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng