An Gano Kasar da Ta ba Iran Babbar Gudunmawa a Kai Hare Hare kan Sojojin Amurka

An Gano Kasar da Ta ba Iran Babbar Gudunmawa a Kai Hare Hare kan Sojojin Amurka

  • Rahoto ya nuna cewa Iran ta sayi tauraron ɗan adam mai suna TEE-01B daga hannun kamfanin China a asirce domin leƙen asirin sansanonin Amurka
  • Ana zargin Iran da amfani da wannan fasaha wajen zaɓar sansanonin sojin Amurka da za ta kai wa hare hare a Saudiyya, Jordan, da ma Iraki
  • Sai dai, gwamnatin China ta yi watsi da rahoton, tana mai bayyana shi a matsayin "ƙage" da wasu suka shirya don cimma wata manufa ta daban

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Iran – Wani bincike ya nuna cewa dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran sun sayi wani tauraron dan adam na leƙen asiri daga hannun kamfanin Earth Eye Co na ƙasar China a asirce.

Rahoton ya bayyana cewa Iran ta yi amfani da wannan tauraron dan adam mai suna TEE-01B wajen sa ido kan manyan sansanonin sojojin Amurka a yankin Gabas ta Tsakiya.

Kara karanta wannan

Muhimman abubuwa 5 da Amurka da Iran suka gaza warwarewa a zaman sulhu a Islamabad

Rahoto ya nuna cewa Iran ta yi amfani da na'urar dan Adam da ta saya daga China wajen kai hare-hare kan sojojin Amurka.
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump (hagu) da Ministan wajen Iran, Abbas Aragchi (dama). Hoto: Valentin Flauraud / AFP via Getty Images
Source: Getty Images

Yadda Iran ta farmaki sansanonin Amurka

Financial Times, wadda ta fitar da rahoton, ta ce hakan na zuwa ne a daidai lokacin da takun-saƙa tsakanin Iran da Amurka ya kai kololuwa sakamakon hare-haren jirage marasa matuƙa da makamai masu linzami.

Bayanai daga wasu takardu da suka fito daga rundunar sojin Iran sun nuna cewa jami'an IRGC sun ba da umarnin ɗaukar hotunan sansanonin Amurka a ƙasashe daban-daban.

Daga cikin wuraren da aka leƙa har da sansanin sojin Amurka na Prince Sultan da ke Saudiyya a ranar 13 zuwa 15 ga Maris, da kuma sansanin Muwaffaq Salti da ke Jordan, sai kuma tashar jiragen ruwan sojojin Amurka da ke Bahrain da ma filin jirgin sama na Erbil a Iraq.

Tallafin da Iran ta samu daga China

Wannan rahoto ya nuna cewa an ɗauki hotunan ne a daidai lokacin da aka kai hare-haren da Shugaba Donald Trump ya tabbatar a ranar 14 ga Maris, 2026, inda aka lalata wasu jiragen Amurka.

Kara karanta wannan

Trump ya fadi babbar barazana 1 da har yanzu Iran take da shi ga kasashen duniya

An kuma bayyana cewa IRGC ta samu damar gudanar da ayyukanta daga gine ginen Emposat, wani kamfanin China da ke Beijing wanda ke samar da ayyukan tauraron dan Adam da leken asiri zuwa yankunan Asia, Latin Amurka da sauran yankuna.

IRGC dai ta sayi tauraron dan Adam na TEE-01B ne jim kadan bayan kamfanin Earth Eye Co ya harba shi zuwa sararin samaniya daga China, kamar yadda takardun suka nuna.

An ce Iran ta yi amfani da tauraron dan Adam wajen kai hare-hare kan sansanonin Amurka.
Iran ta yi gwajin makami mai linzami kirar Fateh 110. Hoto: Mohsen Shandiz/Corbis via Getty Images
Source: Getty Images

Martanin China da Amurka

Ma'aikatar harkokin wajen China ta yi watsi da wannan rahoto a wata sanarwa da ta aike wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.

Ma'aikatar ta bayyana cewa:

"A 'yan kwanakin nan, ana yawan samun wasu bara-gurbi da ke kirkirar labaran karya suna jinga wa China. A sani cewa, China ta na Alla-wadai da ire-iren wadannan maganganu da aka kirkire su don cimma wata muguwar manufa."

A ɓangare guda, fadar White House ba ta yi sharhi ka-tsaye kan rahoton ba, sai dai ta yi nuni da kalaman da Shugaba Trump ya yi a ƙarshen mako, inda ya yi gargaɗin cewa China za ta fuskanci "babban tashin hankali" idan har ta samar wa Iran da makaman kariya daga hare-haren sama.

Kara karanta wannan

APC: Tsohon saƙon shugaban INEC ya jawo zazzafar muhawara kan sahihancin zaben 2027

Trump ya yi wa China gargadi kan Iran

Tun da fari, mun ruwaito cewa, Shugaban Amurka Donald Trump ya sake yin gargadi ga kasar China game da yakin da ake yi a Gabas ta Tsakiya.

Trump ya ce China za ta fuskanci manyan matsaloli idan ta aika makamai zuwa Iran, yana mai gargadi kan yiwuwar rikicin ya kara tsananta.

Mista Trump ya kuma yi ishara da karuwar ayyukan soji a tekun yankin Gulf, yana cewa ana gudanar da aikin share nakiyoyi a mashigar ruwa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com