'Yan Majalisa Sun Gabatar da Hujjoji 6 na Tsige Ministan Tsaro, Trump Zai Rasa Makusanci
- 'Yan Democrat a majalisar wakilan Amurka sun gabatar da hujjoji shida na tsige ministan tsaro kan zargin keta dokokin yaƙi da kisan fararen hula a Iran
- Zarge-zargen da ake yi wa ministan Donald Trump sun haɗa da kaddamar da yaƙi ba bisa ƙa'ida ba da fallasa bayanan sirrin soja ta manhajar Signal
- Duk da cewa ma'aikatar tsaro ta Pentagon ta yi watsi da lamarin, hakan ya ƙara rura wutar takun-saƙa tsakanin Democrat da gwamnatin Amurka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Amurka – Wakilan jam’iyyar Democrat a majalisar wakilan Amurka sun ƙaddamar da babban yunƙuri na tsige ministan tsaro, Pete Hegseth.
Ana yunkurin tsige Hegseth ne sakamakon zarge-zarge masu tsanani da suka shafi yadda yake tafiyar da yaƙin Iran da kuma jagorancinsa a ma’aikatar tsaro.

Source: Twitter
An gabatar da hujjojin tsige ministan Amurka
Karkashin jagorancin 'yar majalisa Yassamin Ansari daga Arizona, ƴan Democrat sun gabatar da daftarin shari’ar mai shafuka bakwai wanda ke ƙunshe da korafe-korafe shida da suka ce sun sa ya zama wajibi a cire shi daga muƙaminsa, in ji rahoton CBS News.
Ƴan jam'iyyar Democrat sun bayyana waɗannan dalilai a matsayin hujjar tsige Ministan domin nuna cewa ya saɓa wa rantsuwar aikin sa.
Hujjojin da suka gabatar sun hada da:
- Kaddamar da yaƙi kan Iran ba tare da amincewar majalisa ba, wanda hakan ya jefa rayukan sojojin Amurka cikin haɗari.
- Yin biris da dokokin ƙasa da ƙasa, ciki har da kai hare-hare da suka kashe fararen hula 168 a wata makarantar ƴan mata a Iran.
- Nuna sakaci wajen sarrafa bayanan sirrin soja, har da raba bayanan ayyukan soja a Yemen a wata hira ta sirri a manhajar Signal.
- Toshe hanyoyin gudanar da bincike na majalisa ta hanyar ƙin bayar da bayanai kan ayyukan soja a Venezuela da Iran.
- Yin amfani da muƙaminsa wajen sanya siyasa a cikin harkokin rundunonin sojin ƙasar Amurka.
- Aikata ayyukan da suka janyo wa Amurka da dakarunta rashin mutunci a idon duniya da kuma raunana ƙawance da NATO.
Martanin Pentagon ga shirin tsige minista
Sakatariyar yaɗa labarai ta ma'aikatar tsaro ta Pentagon, Kingsley Wilson, ta mayar da martani inda ta ce wannan yunƙuri na tsige ministan ba komai ba ne illa ƙoƙari na ƴan jam'iyyar Democrat na son fitowa a kanun labarai.
Ta jaddada cewa ma'aikatar tsaro ta samu gagarumar nasara wajen aiwatar da muradin Shugaban Ƙasa a yakin da aka yi daIran yadda ya kamata.
Sanarwar ta nuna cewa gwamnati na kallon wannan mataki a matsayin siyasa tsantsa da nufin dakile nasarorin da aka samu, in ji rahoton Fox News.

Source: Twitter
Wutar rikicin siyasa ta fara ruruwa a Amurka
Duk da tsananin waɗannan zarge-zarge, masana na ganin cewa wannan yunƙuri ba zai kai ga gaci ba a wannan shekarar, domin jam’iyyar Republican ce ke da rinjaye a majalisar wakilai.
Sai dai, ƴan Democrat na shirin sake tada batun idan har suka samu nasarar karɓe ikon majalisar bayan zaɓen tsakiyar wa’adi da ke tafe.
Wannan shari’a dai ta ƙara zafi a siyasar Amurka, musamman a daidai lokacin da yaƙi a Gabas ta Tsakiya ke ci gaba da ɗaukar hankali.
Hegseth na son raba hafsun soja da kujerarsa
A wani labarin, mun ruwaito cewa, ministan tsaron Amurka Pete Hegseth ya taso babban hafsan rundunar sojojin kasa, Janar Randy George ana tsaka da yaki da Iran.
Rahotanni sun ce an bukaci George ya yi ritaya da wuri, wanda ke cikin jerin manyan jami’an soja da aka sallama tun bayan Hegseth ya hau mulki.
Matakin na zuwa ne bayan an sallami manyan hafsoshin soja da dama, ciki har da shugabannin rundunar ruwa da sama.
Asali: Legit.ng


