Kano za Ta Karbi Manyan Baki, Akwai Babban Taro kan Miyagun Kwayoyi
- Gwamnatin Kano za ta hada gwiwa da Kwamitin Majalisar Wakilai wajen shirya taron yaki da shaye-shaye da safarar miyagun kwayoyi
- Taron zai tattaro masu tsara manufofi, jami'an tsaro, masana lafiya, sarakuna, malamai da kungiyoyin farar hula domin a warware matsalar
- An ce an zabi Kano ne saboda matsayinta na cibiyar kasuwanci, yawan al'umma da rawar da take takawa a Arewacin Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Gwamnatin Jihar Kano ta sanar da cewa za ta hada hannu da Kwamitin Musamman na Majalisar Wakilai mai kula da Miyagun Kwayoyi da Safarar Haramtattun Kwayoyi .
Za a yi wannan hadin kai domin shirya taron yankin Arewa maso Yamma kan yaki da shaye-shayen miyagun kwayoyi, safararsu tare da kula da amfani da taba sigari da barasa.

Source: Facebook
Jaridar Punch ta kawo labarin cewa ana sa ran gudanar da taron daga baya a wannan shekarar a Kano, inda za a tattauna hanyoyin da za su kara karfafa matakan da Najeriya ke dauka domin dakile matsalar shaye-shayen miyagun kwayoyi, musamman tsakanin matasa.
Kano za ta karbi baki
The Nation ta wallafa cewa taron zai hada masu tsara manufofi, jami'an tsaro, kwararrun ma'aikatan lafiya, sarakunan gargajiya, shugabannin addini, kungiyoyin farar hula da sauran masu ruwa da tsaki.
A cikin wata sanarwa da shugaban kwamitin, Oluwatimehin Adelegbe, ya fitar ranar Talata, 4 ga watan Yuli, 2026 ya bayyana cewa taron na daga cikin shirin wayar da kan jama'a da kwamitin ke gudanarwa a fadin kasar.
Adelegbe, wanda dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Sumaila/Takai, Rabiu Yusuf, ya wakilta yayin ziyarar da suka kai Kano, ya yabawa Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa amincewarsa da karbar bakuncin taron na yankin Arewa maso Yamma.

Kara karanta wannan
Majalisar shari'ar musulunci ta Najeriya ta hango matsala a shirin kafa yan sandan jihohi
Ya ce:
"Muna godiya ga Gwamna Yusuf saboda nuna hangen nesa ta hanyar hada kai da Majalisar Dokoki ta Kasa wajen karbar bakuncin wannan muhimmin taro na yanki."
An girmama matsayin Kano a Najeriya
Adelegbe ya bayyana cewa an zabi Kano ne saboda muhimmancin matsayinta a matsayin cibiyar kasuwanci, yawan al'ummarta da kuma rawar jagoranci da ta dade tana takawa a Arewacin Najeriya.

Source: Getty Images
A cewarsa, hadin gwiwar ba wai karbar bakuncin taro kadai ba ne, illa wata muhimmiyar alaka tsakanin Gwamnatin Kano da Majalisar Dokoki ta Kasa domin samar da dorewar dokoki da za su rage yawaitar shaye-shaye.
Ya jaddada cewa yaki da miyagun kwayoyi ba aikin jami'an tsaro kadai ba ne. A cewarsa, ana bukatar hadin kan gwamnati, al'umma, dokoki, ilimantarwa, gyaran hali, wayar da kai da kuma karfafa hadin gwiwa tsakanin bangarori daban-daban.
Kano ta yi magana kan yan sandan jihohi
A baya, mun kawo labarin cewa Gwamnatin Kano ta ce 'yan sandan jihohi ba za su kasance da alaka da zabukan 2027 ba kamar yadda wasu ke fargaba ba bayan umarnin shugaban kasa.
Hadimin Gwamna a kan kafafen yada labarai, Ahmed S Aruwa ya tabbatar wa Legit cewa akwai dalilan da suka sa dole aka kirkiri yan sandan jihohi wanda ake sa ran zai karfafa tsaron rayuka.
Ya bayyana cewa jami'an rundunar jihohi ba za su shafe na tarayya da ake da ita ba, saboda haka zai yi wahala a gansu kan akwatunan zabe kamar yadda wasu ke fargaba gabanin 2027.
Asali: Legit.ng

