Yadda Za Ku Duba: WAEC Ta Saki Sakamakon Jarabawar Kammala Sakandare ta 2026
- Hukumar WAEC ta fitar da sakamakon jarabawar WASSCE ta 2026, inda sama da ɗalibai miliyan 1.2 suka samu aƙalla darussa biyar da suka haɗa da Turanci da Lissafi
- Ɗalibai za su fara samar da PIN da Serial Number a shafin WAEC kafin su shiga shafin duba sakamako domin ganin sakamakonsu cikin sauƙi
- Jarabawar ta gudana tsakanin Afrilu da Yuni 2026, yayin da makarantu da dama suka yi amfani da tsarin jarabawar kwamfuta tare da tsarin rubutu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida.
Abuja - Hukumar Shirya Jarabawar Kammala Makarantun Sakandare ta Yammacin Afirka (WAEC) ta sanar da fitar da sakamakon jarabawar WASSCE ta shekarar 2026 ga ɗaliban makarantu.
Hukumar ta bukaci ɗalibai su mallaki PIN sannan su duba sakamakonsu ta shafukan intanet na WAEC.

Source: Facebook
Duba sakamakon jarabawar WAEC
Wannan na kunshe ne a cikin sanarwar da hukumar ta wallafa a shafinta na X a ranar Laraba, 5 ga watan Agustan 2026.
A cewar WAEC, daga cikin ɗalibai 1,950,726 da suka rubuta jarabawar, mutum 1,200,514, wanda ya kai kashi 61.54 cikin 100, sun samu maki na darussa biyar ko fiye, ciki har da Turanci da Lissafi.
Hukumar WAEC ta bayyana cewa masu neman sakamakonsu su bi waɗannan matakai:
1. Samar da PIN da Serial Number
Da farko, ɗalibi zai shiga shafin WAEC domin samar da PIN da Serial Number da za a yi amfani da su wajen duba sakamako.
2. Shiga shafin duba sakamako
Bayan samun PIN, sai a shiga shafin WAEC Direct domin fara aikin duba sakamakon.
3. Cika bayanan da ake buƙata
A shafin, ɗalibi zai shigar da lambar jarabawarsa, Lambar Shaidar Ɗan Ƙasa (NIN) da ya yi amfani da ita wajen rajista, tare da sauran bayanan da ake buƙata domin tabbatar da sahihancin bayanansa.
4. Tabbatar da lambar OTP
Hukumar ta ce za a aika lambar tabbatarwa (OTP) zuwa bayanan tuntuɓar da aka yi rajista da su, wanda dole ne a shigar kafin a samu damar ganin sakamakon.
Dalibai miliyan 1.9 suka rubuta jarabawar
Kimanin ɗalibai miliyan 1.96 daga makarantu sama da 24,200 a faɗin Najeriya ne suka rubuta jarabawar, wadda ta gudana tsakanin ranar 21 ga Afrilu zuwa 19 ga Yunin 2026.

Source: Twitter
Yayin da mafi yawan cibiyoyin jarabawa suka yi amfani da tsarin rubutu na takarda da biro, makarantu da dama sun kuma zaɓi yin amfani da tsarin jarabawar kwamfuta (CBT), wanda ya ƙaru idan aka kwatanta da shekarun baya.
WAEC ta tunatar cewa tun da farko ta sanar da cewa za ta fitar da sakamakon ne kusan kwanaki 45 bayan kammala jarabawar ƙarshe, kafin ta cika wannan alƙawari da sanarwar da ta fitar a ranar Laraba.
Asali: Legit.ng

