Yakubu Gowon Ya Tuna baya, Ya Fadi abin da Ya Jawo Barkewar Yakin Basasa a 1967
- Janar Yakubu Gowon ya ce yarjejeniyar Aburi ta rushe ne saboda sabani da Chukwuemeka Ojukwu kan ba gwamnonin sojoji iko
- Gowon ya ce Ojukwu ya so gwamnoni su jagoranci sojoji a yankunansu, amma gwamnati ta ki amincewa saboda ya saba wa doka
- Tsohon shugaban ya ce rashin lafiyarsa da sanarwar da Ojukwu ya fitar sun jawo rushewar yarjejeniyar Aburi tare haddasa yakin basasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Tsohon shugaban kasar Najeriya, Janar Yakubu Gowon, ya bayyana dalilin da ya sa yarjejeniyar Aburi ta rushe, sannan yakin basasa ya barke a 1967.
Gowon ya ce sabanin da ya kunno kai tsakaninsa da Chukwuemeka Odumegwu Ojukwu ya ta’allaka ne kan "wanda zai rike iko da dakarun soja a yankuna".

Asali: Getty Images
Gowon ya fadi dalilin rushewar yarjejeniyar Abure
A wata tattaunawa da yayi da Arise TV, tsohon shugaban kasar ya ce an cimma matsaya a taron Aburi da aka yi a Ghana, amma daga baya Ojukwu ya bukaci cikakken ikon mulki na yankuna, wanda gwamnati ta ki yarda.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“Misali, Ojukwu na so a ce gwamnoni ne za su jagoranci rundunar sojan kowanne yanki, kuma shi ne zai rike nasu a gabas."
- Janar Yakubu Gowon.
Janar Yakubu Gowon ya ce wannan abu ne da bangaren tarayya ba zai taba amincewa da shi ba, saboda ya sabawa tsarin kasa.
Ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta dauki taron Aburi a matsayin wata dama ta yin sulhu, ba wai wajen sake fasalin tsarin mulki ba.
Gawon ya kara da cewa:
“Muna ganin lokaci ne da za mu zauna a matsayin sojoji domin shawo kan rikicin cikin gida, amma ba hakan na nufin za mu canja tsarin mulki ba ne.
An ji kuskuren Ojukwu da ya jawo yakin basasa
Bayan komawa gida daga taron Aburi, Gowon ya ce ya kamu da rashin lafiya wanda ya hana shi mayar da martani cikin gaggawa kan bayanan da Ojukwu ya fitar.
Wannan jinkiri, a cewarsa, ya bude kofar fassarar da bangaren gabas yayi ta daban, tare da fitar da sanarwa ba tare da amincewar kowa ba.
“Ojukwu ya fito ya fadi abubuwan da ba mu amince da su a wannan taro ba, ya riga mu fitar da bayani game da taron."
- Inji Yakubu Gowon.
Don warware rikicin, Gowon ya ce gwamnati ta kira wani taro a Benin da dukkanin gwamnoni na yankuna suka halarta, amma Ojukwu ya ki zuwa.
“Da Ojukwu ya halarci taron da muka kira a Benin, da akwai yuwuwar a hana rikicin ya yi kamari,” a cewar Gowon.

Asali: Facebook
Rushewar yarjejeniyar Aburi da yakin basasa
Tsohon shugaban kasar ya ce gwamnatin tarayya ta shirya aiki da “yarjejeniyar Aburi,” amma ba za ta taba amincewa da ikon soja ya koma hannun gwamnonin yankuna ba.
Yarjejeniyar Aburi da ta rushe na daya daga cikin abubuwan da suka haddasa yakin basasa da ya lashe rayuka fiye da miliyan daya tsakanin 1967 da 1970.
Gowon ya ce bukatar Ojukwu na ikon soja ne ya janyo sabani, ba siyasa kadai ba, kuma wannan ne ya hana a cimma burin zaman lafiya a lokacin.
'Yan Najeriya su guji barkewar yakin basasa' - Gowon
A wani labarin, mun ruwaito cewa, tsohon shugaban mulkin soja na Najeriya, Janar Yakubu Gowon, ya yi Allah wadai da kisan gillar da ake ci gaba da yi a faɗin ƙasar.
Ya gargadi 'yan Najeriya da su guji sake ta da wani yaƙin basasa, yana mai tunatar da illolin da irin waɗannan rikice-rikicen ke haifarwa.
Gowon, wanda ya mulki Najeriya daga 1967 zuwa 1970, ya bayyana cewa lamarin kashe-kashen da ake yi a ƙasar yana matuƙar tada masa hankali.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng