'Yan Bindiga Sun Farmaki Tawagar Hadimin Gwamna Soludo, Sun Yi Kisa
- Harin da 'yan bindiga suka kai wa ayarin babban jami'in gwamnatin jihar Anambra, Charles Soludo ya yi sanadin mutuwar mutum huɗu
- Shaidun gani da ido sun ba da labarin mummunan musayar wuta da aka yi yayin harin kwanton bauna da aka kai a Orumba ta Arewa
- Gwamnatin Anambra ta yi alƙawarin gurfanar da waɗanda suka kai harin gaban kuliya yayin da ake ci gaba da nuna damuwa kan tsaro
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Anambra – Gwamnatin Jihar Anambra ta tabbatar da kai wani mummunan hari kan ayarin babban jami'in Gwamna Chukwuma Soludo, Ben Nwankwo.
An ce an kai harin ne a kan hanyar Amansea–Awa–Ufuma da ke Ƙaramar Hukumar Orumba North yayin da Ben Nwankwo ke wucewa.

Source: Facebook
Punch ta wallafa cewa lamarin ya yi sanadin mutuwar jami’an ’yan sanda biyu da fararen hula biyu, yayin Ben Nwankwo ya tsira ba tare da rauni ba.

Kara karanta wannan
'Yan bindiga sun kai mummunan hari masallaci ana tsakiyar sallar Magriba a Kaduna
Harin da aka kai Anambra
Shaidun gani da ido sun ce maharan, waɗanda ake zargin sun buya a cikin dazuzzukan da ke kusa, sun buɗe wuta ne yayin da ayarin ke isowa yankin, lamarin da ya haddasa mummunar musayar wuta tare da jefa mazauna yankunan cikin firgici.
An ce ayarin na kan hanyarsa ta komawa Awka ne bayan kammala wani aiki na musaman a lokacin da aka kai masa harin.
Da yake mayar da martani kan lamarin, kwamishinan yaɗa labarai, Law Mefor, ya ce gwamnatin jihar ta yi matuƙar kaɗuwa da harin, tare da tabbatar da cewa za a gurfanar da masu hannu a ciki gaban shari’a.
A cikin wata sanarwa, ya ce:
“Gwamnatin jihar Anambra ta yi matuƙar kaɗuwa da harin da aka kai wa ayarin shugaban ma'aikata a daren Lahadi, 31 ga Mayu, 2026, tsakanin ƙarfe 8:00 na dare zuwa 9:00 na dare a kan iyakar Orumba ta Arewa da Awka ta Kudu, yayin da suke dawowa daga wani aiki na musamman.”
Ya ƙara da cewa:
“Bayan jawo asarar rayuka, Harin barazana ne ga zaman lafiya, tsaro da tsarin dimokuraɗiyyar jiharmu.”
Matakain da gwamnati ta dauka
Mefor ya kuma bayyana cewa an tura jami’an tsaro domin farautar maharan, yana mai jaddada cewa harin ba zai hana ci gaba da ƙoƙarin da ake yi na inganta tsaro a jihar ba.
Vanguard ta rahoto ya ce:
“Abin takaici, mutum huɗu sun rasa rayukansu kuma sun cancanci a yi musu adalci. Gwamnatin jihar Anambra na miƙa ta’aziyyarta ga iyalan waɗanda suka mutu tare da taya su jimamin wannan rashi."

Source: Original
'Yan bindiga sun kai hari masallaci
A wani labarin, mun kawo muku cewa an tabbatar da mutuwar mutum daya yayin da wasu masu ibada da dama suka jikkata sakamakon harin da aka kai wa wani masallaci.
Rahotanni sun nuna cewa an kai hari masallacin ne a lokacin sallar Magariba a ƙauyen Namama da ke karamar hukumar Giwa ta Jihar Kaduna.
Maharan sun kutsa cikin masallacin ne yayin da masu ibada ke gudanar da sallar Magariba a lokacin da ake ruwan sama mai ƙarfi, sannan suka fara harbe-harbe.
Asali: Legit.ng
